Super Eagles

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta ce ba za ta fafata da Libya ba a wasan ranar Talata na neman cancantar shiga gasar AFCON 2025 saboda hukumomin ƙasar sun sauya filin da ya kamata jirgin tagawar ya sauka da kuma hana tawagar shiga cikin ƙasar inda 'yan wasa da sauran jami'ai suka kwashe fiye da sa'o'i 12 suna zaman jira.

''Tawagar Nijeriya da za ta buga wasa da Libya na neman cancantar shiga gasar AFCON 2025 ranar Talata ta kwashe awanni 12 a filin jirgin saman Al Abraq bayan ta sauka a Libya,'' in ji wata sanarwa da hukumar kula da ƙwallon ƙafar Nijeriya (NFF) ta fitar ranar Litinin da safe.

Tawagar ta Nijeriya ta isa Libya ranar Lahadi gabanin fafatawar, amma ta yi ƙorafin cewa an bar su ba tare da sanin halin da ake ciki ba duk da cewa an canza inda jirginsu zai sauka daga filin jirgin saman Benghazi zuwa filin jirgin saman Al Abraq.

''A wani mataki mai ɗaure kai, an bar jirgin da muka yi haya ValueJet yana waɗari cikin yanayi mai hatsari, kana an sauya masa wurin sauka zuwa ƙaramin filin jirgi daga filin jirgin saman Benghazi a lokacin da direba ya kammala shirin sauka a Benghazi,'' in ji NFF.

Hakan ne ya sa 'yan wasa "suka yanke shawarar ƙin buga wasan kuma jami'an NFF sun soma shirye-shirye domin mayar da su gida," a cewar sanarwar.

Shi ma kyaftin ɗin Super Eagles, William Troost-Ekong ya wallafa saƙo a shafinsa na X inda ya bayyana ce shi da sauran 'yan wasan Nijeriya sun yanke shawarar ƙin buga wasa da Libya.

Troost-Ekong ya nuna rashin jin daɗinsa game da mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki bayan isar su Libya.

Kawo yanzu, hukumomi a Libya ba su ce komai ba game da wannan lamari.

Tawagar Nijeriya ta je Libya ne domin fafatawa da Libya a zagaye na biyu na wasan, kwanaki kaɗan bayan ta doke tawagar Libya da ci 1-0 a wasan da suka yi a filin wasa na Uyo a jihar Akwa Ibom.

Hukumomin wasa na Libya

Hukumar kwallon kafa ta Libya LFF, ta aryata zargin cewa da gangan ta juya akalar jirgin da ya kai 'yan wasan Nijeriya, kuma aka bar su suna jiran gawon shanu a filin jirgi tsawon awanni 15.

A wata sanarwa da ta fitar yau Litinin, hukumar ta LFF ta bayyana cewa jami'an filin jirgi ne, da jami'an tsaro, da yanayin zirga-zirga yakan shafi matafiya ta jirgin sama, kuma ba sabon abu ba ne.

Hukumar ta kuma yi iirarin cewa irin wannan yanayi ya shafi tawagarta da ta je Nijeriya a makon jiya a birnin Uyo, amma su ba su fito sun soki kowa ba.

Bayan ta nuna takaicinta kan abin da ya faru ga tawagar Super Eagles ta Nijeriya, hukumar ta ce ba halayyar asar ba ce in girmama baki. Sannan sun yi fatan za a a warware wannan wannan batu cikin lumana.

TRT Afrika