Daga Charles Mgbolu
Yayin da aka kai matakin sili-daya-ƙwale a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka, ana ci gaba da tafka muhawara musamman a kafafen sada zumunta kan zagayen ’yan 16.
Wasu magoya bayan Nijeriya musamman a kafafen sada zumunta suna kira da a sanya gola Andre Onana a raga yayin wasan da Nijeriya za ta yi da Kamaru a ranar Asabar 27 ga watan Janairu.
Kasashen za su fafata ne a filin wasa na Stade de la Paix in Bouake, sai dai babu tabbacin wanda zai kama wa Kamaru gola.
Ra’ayoyin mutane sun nuna cewa idan Onana ya kama wa Kamaru gola, to hakan a ganinsu zai sa Nijeriya ta samu nasara a kanta.
Rashin ƙwazo
Onana ya kama wa Kamaru gola a wasanta na biyu, inda ta yi rashin nasara a hannun Senegal a ranar 19 ga watan Janairu.
An rika sukar Onana mai shekara 27, dangane da kura-kuran da ya tafka a wasan da suka buga da Senegal, kuma an ajiye shi a wasan da suka buga na gaba.
Wani mai amfani da shafin X ne @Omojuwa, ya fara magana kan Onana: ’’Ya kamata Kamaru ta kara bai wa Onana wata damar a wasan da za ta buga da Nijeriya.
Bai kamata ku ajiye ƙwararren dan wasanku ba haka kawai kan wani abu ne da za a iya gyarawa cikin ruwan sanyi. Ya kamata su ci gaba da matsa lamba kan yadda za a gyara dangantaka tsakanin masu horar da ’yan wasa da ’yan wasa.
Ina fatan Onana zai koma wa Kamaru (kama gola),” in ji @Omojuwa.
Wannan saƙo ya jawo muhawara sosai a kafafen sada zumunta.’’ Kana so ne a sanya shi a gola saboda Nijeriya ta ci ƙwallaye ko? Na gane abin da kake nufi,” in ji wani @amensure90, wanda ya wallafa ra’ayinsa a shafin X.
‘’Ana so a same shi don a samu gangara,‘’ in ji wani @Olawale55773901.
Vincent Aboubakar
Sai dai magoya bayan Kamaru sun yi watsi da wannan batu, sun fi mayar da hankalinsu kan kyaftin din kasar Vincent Aboubakar wanda ya ji rauni kuma bai taka leda ba har yanzu a AFCON.
Ko da yake wasu suna gargadin cewa kada a raina Onana. Saboda a cewarsu zai iya ba maraɗa kunya.