Shahararriyar jumla ta “Hankali shi ne abun da aka fi samu na baidaya a duniya” --- ba ya aiki da ‘yan kasar Morokko da Aljeriya. Suna yin wasa da nishadi kan abubuwa na zato da tsammani inda suke musu kan abincin kuskus, kayan sawa ko ma wani kan halitta da ya zo a tarihinsu: Tarik ibn Ziyad, Almohades, ibn Baltuta da sauran su… Sun dilmiyar da jiya don birkita yau. Wadannan kashe biyu suna da kaya na bai daya: Iyalai, yruka, al’adu, lahajoji da dabi’u da suke tafiya tare. Amma wasu masu bayyana ra’ayoyinsu a kasashen sun makance inda ba sa ganin gaskiyar da ya kamata su runguma nan take.
‘Yan Morokko sun harzuka da ganin nau’İkan Zellige ----- duk da cewa sun fito ne daga tlemcen --- a kan rigunan ‘yan kwallon kafar Aljeriya, da manaja da aka kora daga wajen aikinsa na kamfanin jiragen Aljeriya saboda rarraba takardun dake dauke da gine-ginen Morokko. Akwai malkwadawa da juya gaskiyar tarihi tare da bayar da bayanai na karya, wanda hakan ke kara tauyewa da cutar da yanayin tarihin.
Rudanin na sake bayyana ne a lokacin da ake bayyana ma’anar kalmar “Magreb” da take nufin “Maghreb” da “Morokko”. Hakan ya sanya kofar Bab Al-Magreb dake Masallacin Aaksa take nufin Kofar Arewa da kuma Morokko.
Tabbas Morkko ba ta zama kamar Aljeriya ba, haka ita ma Aljeriya ba ta wakiltar Morokko --- kuma kowacce kasa daga cikin kasashen biyu na da nata abubuwan da suka kebanta da ita kadai, a al’adance da tarihance; amma hakan ba zai sanya a yi watsi da ba su da wani abu mai kama da juna a tarihi ba.
Dalilan na iya bwa kowa mamaki matuka. A wani lokaci, shugaban kotun masarautar Morokko ya kama ni ina dudduba yaben da aka yi a kubbar da ake kira “Qubbat Annasr”, wadda ke nuni ga karfin mulkin Morokko --- ma’ana wajen da ake yanke manyan hkunce-hukunce na fadar Morokko da ma gudanar da manyan bukukuwa na fada. Wannan lokaci ne da na kaddamar da bincike kan karfin mulkin Morokko. “Daga ina wannan yabe ya zo?” shugaban kotun ya tambaye ni? “Daga Tetoun” Na ba shi amsa; “Ya bambanta da yaben Fez” “kuskure” ya fada “Ya zo daga Tlemcen”, ya kara da cewa Fqih Al Maamri ne ya dawo da manazartar Tlemcen”, a karninkan da suka gabata ne aka mulmula wannan kubba da yaben wanda ya yiwa qubbar Annasr ado. Fqih Al Maamr wanda shi ne daraktan Makjalisar Zartarwa ta Masarauta kuma malamin yarimomi, ya fito daga Kabylie a Aljeriya. Ya biyo shugabancin Muhammad na V, kuma bayan Morokko ta samu ‘yancin kai an nada shi a matsayin Firaministan Masarauta.
Akwai yiwuwar harzuka zukata idn aka ce Yariman masarautar Morokko ya fito ne daga Aljeriya, ha ma mai kula da karbar baki na fadar --- a wannan yanayi, kaddour Benghabrit --- dan asalin Tlemcen ne. A wannan lokaci kuma, shi ne Shugaban Aljeriya na farko bayan samun ‘yancin kai. --- Haka kuma Ahmad ben Bella --- ya fito daga Morokko, daga kauyen Marrakesh. Sai ya zama kamar wani wasan yara idan muka ji dan siyasar Aljeriya ya rike babban matsayi a Morokko ---- ko kuma dan Morokko ya yi mulki a Aljeriya. Abu ne mai yiwuwa hakan ta faru a tsakanin al’umun da suka fito daga tsatsao daya.
Ba wai al’adu iri daya kawai ‘yan Aljeriya da Moorkko suke da shi ba, suna da wasu dabi’u da suke rage musu kima da kassara su, da kuma wasu gwagwarmaya na zamantakewa d suka bambanta a matakin aiwatar da su.
Mutum zai iya yin mamakin ganin cewa dan kasar Morokko da ya fito daga Rif, ya fi kamanceceniya da Kabyle, maimakon dan uwansa dan kasar Morokko --- Sannan dan fas kuma ya fi kamanceceniya da dan Tlemcen, maimakon makocinsa na Atlas. Wannan nufin gaskiyar al’amarin na da rikitarwa, kuma ana bukatar kula da tsantseni don bayyana gaskiyar al’amura. ‘Yan Morokko da ‘yan Aljeriya na da abubuwa da dama na bai daya. Laifin yaro karami ne idan aka yi musu kallon ba su da alaka da juna.
Shin ya kamata mu tuna da cewa, biyu daga cikin shugabannin juyin juya halin Aljeriya --- Mohammed Khider da Krim Belkacem --- sun kwanta dama a Chouhada dake Kasabalanka, kuma Mohammed Boudiaf ya rayu a Kenitra, Morokko kafin ya zama shugaban kwamitin kolin fadar shugaban kasa.
A duk lokacin da na kalli yadda al’amura suke a tsakanin Aljeriya da Morkko --- ba tare da nuna bacin rai ba --- Ina tuna wasu bangarori na “Dan Talak” da Mouloud Feroun ya rubuta dake bayanin yadda ‘yan biyu suka juya baya, suka kuma fada kazamin rikici saboda ‘ya’yansu.
Watakila wannan rikici kan rigar ‘yan kwallon kafar Aljeriya zai tunawa al’umun biyu tarihinsu na bai daya, kuma sama da haka ma, kaddarar bai daya da suke da ita.