Daga Craig Holman
Ba boyayyen abu ba ne cewa tsarin shugabancin "dimokradiyya" na Amurka na dabaibaye da kudade, kuma musamman yadda biloniyoyi da miloniyoyi suke bayar da tallafin yakin neman zabe da makudan daloli.
Kashe kudade a zaben shugaban kasar Amurka na 2024 zai haura n dukkan zabukan baya.
Za a kashe kusa dala biliyan $16 a tallace-tallacen yakin neman zabe kawai. Ku kara da kudaden gudanar da gangamin ina kusan kudin da za a kashe zai kai dala biliyan $20/.
Wannan ya sanya masu hannu da shuni zama a kan gaba wajen zabar shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Amurka.
A kowane lokaci kudi na zama muhimmin abu a gangamin zabuka a Amurka. A 1895, Sanatan Amurka Mark Hanna ya ce "Akwai abubuwa guda biyu masu muhimmanci a siyasa. Na farko shi ne kudi, kuma ba zan iya tuna na biyun ba."
Sai dai kuma, a baya kudaden da ake amfani da su wajen daukar nauyin yakin neman zabuka a Amurka na zuwa dga bangarori daban-daban.
Tabbas, masu kudi ne ke bayar da kashi mafi toka, amma kungiyoyin farar hula, jam'iyyun siyasa, kudaden jama'a - da wasu masu bayar da gudunmowa ma na bayar da nasu.
Bullar manyan Kwamitocin Yakin Neman Zabe
An dade d haramta wa kamfanoni da hukumomi bayar da gudunmowar kudi ga yakin neman zabe a Amurka. Amma hakan ya sauya bayan mummunan matakin da Kotun Kolin Amurka ta dauka a 2010.
Kotun ta yanke hukuncin cewar za a ci gaba da kayyade kudin yaki neman zabe da za a baiwa dan takara a matsayin gudunmawa, amma kuma masu kudi za su iya bayar da irin adadin da suke so na kudi a matsayin gudunmowa ga 'yan takara ta hanyar kungiyoyi.
Wannan mataki ne ya janyo kirkirar manyan kwamitocin gudunmowar yakin neman zabe da ake kira "Super PACs" wanda ba sa cikin da'irar siyasa, kuma a su iya tara kudade da kashe su ba tare da kayyade wa ba matukar ba daga kasar waje kudaden suka fito ba.
Super PACs - dandalin da ba shi da iyaka na kamfanoni da masu hannu da shuni su kashe kudaden da suka ga dama ga wani dan takara ko kalubalantar wani dan takara - sun yadu sosai a fagen yakin neman zabe, suna nan da yawa kuma suna kashe kudade sosai.
Ba da jima wa ba bayan matakin da Kotun Kolin ta dauka, sai super PACs guda 89 suka tara kudi har dala miliyan $89 a lokacin zabukan bazara na 2010.
A wannan shekarar, irin wadannan kungiyoyi su 2,321 sun tara dala biliyan $2.2 zuw ayau, inda ake sa ran zuwan wasu kudaden da dama.
Kusan duk kudaden da suke samu na zuwa ne daga wajen 'yan tsiraru da ke bayar da gudunmowa. Biloniyoyi kaai - akwai su sun kai 700 a Amurka - su suka bayar da kashi 15 na zabukan bazara na 2022, kuma duk ta hannun super PACs suka bayar.
A wannan shekarar, masu bayar da gudunmowa 50 sun bayar da dala biliyan $1.5 ga wadannan kungiyoyi da ba sa cikin siyasa.
Ban gishiri in ba ka manda
Kar ku raba daya biyu: duk wannan kashe kudade d biloniyoyi ke yi na da wata manufa da suke son cimma wa a tattare da dn takara, kuma a mafi yawancin lokuta na zuwa tare da manufofin wani tsari da aka bayyana.
Kimanin rabin super PAC na goyon bayan dantakara guda daya ne, kuma kuma tsaffin abokai da ma'aikata ne ke kafa su. Trump na da nasa super PAC din, haka ma Kamaala Harris na da nata.
Duk kudaden da aka baiwa wadannan super PAC ana kashe su ne kai tsaye ga wannan dan takarar, kuma dan takarar ya san daga ina kudaden suka fito.
Sau da yawa, wadannan manyan masu bayar da gudunmowa suna bayar da tallafin ne tare da tambayar wani abu.
Biloniyoyi Sheldom da Miriam Adelson sun bawa super PAC din Trump dala miliyan $20 a 2016 don neman ya mayar da ofishin jakadancin Isra'ila jerusalem daga Tel Aviv. A lokacinda aka zabi Trump, ya cika wannan aiki.
Biloniya Reid Hoffman ya zuba miliyoyin daloli ga kamfen din Harris, in abai boye ba ya bayyana yana son idan ta ci zabe ta kori Lina Khan, shugabar hukumar kula da gogayya tsakanin kayayyaki.
Duk kusan bukatun iri guda ne, akwai na Mellon da ke son gamnatin Trump ta rage haraji da sayar da kadarorin gwamnati a bangaren kasuwancin da yake yi.
Trump ya fi bayyana zai yi abinda ake so. A wajen cin abincin dare na Mar-a-Lago da shugabannin kamfanonin mai, Trump ya kulla yarjejeniya za su bayar da gudunmowar dala biliyan ɗaya.
Kuma ya yi musu alkawarin idan ya koma White House zai yi fatali da dokar kare muhalli da aka samar a lokacin mulkin Biden.
Dabbaka manufa
Matsalolin da masu kudi da ke daukar nauyin takara ke haifarwa ba su tsaya ga sayen wata bukata kawai ba.
Wadannan Wadannan masu kudi da ke bayar da gudunmowa na iya dabbaka manufofin siyasa na kasa, ta hanyar zabar waye zai zama ko waye ba zai zama dan takarar jam'iyya ba.
Samun gudunmowar kudi daga masu bayar da kudin farko na taimaka wa mutum zama an takarar jam'iyya, sannan daga baya kuma ake zuwa wajen kananan masu bayar da gudunmowa don neman tallafi.
Kamala Harris ta samu shuhura a matakin kasa a loakcinda ta yi takarar shugaban kasa a 2020 inda biloniyoyi da matansu da dama suka ba ta gudunmowa sama da kowanne dan takara, har ma sama da Biden.
A yanzu a matsayin 'yar takarar jam'iyyar Democratic, ta yi alfahari da cewar kashi 40 na kudaden kamfen din ta za su zo ne daga kananan masu bayar da gudunmowa, wanda haka ne. Amma idan ba don taimakon farko na biloniyoyi ba da ba a san ta a matakin kasa ba.
Farashin zama dan takara da cin zabe ya daga sosai daga shekaru 10 zuwa yau. Farashi da Amurkawa matsakaita ba za su iya saya ba, saboda haka ya sanya biloniyoyi da miloniyoyi ne kawai suke kidansu suke rawarsu.
Wadannan masu kudi da ke da bukata ba su da yawa amma sun shirya bayar da manyan kudade, sau da yawa don biyan wata bukata tasu.
Tare da albarkacin Kotun Kolin Amurka da ba a zabar alkalanta, wasu 'yan tsiraru na sake fasalin salo da yanayin siyasar Amurka..
Wannan babban hatsari ne da ke sanya tantama kan shin akwai dimokradiyya da ke kare manufofin al'umma ba wai bukatun wasu 'yan tsiraru ba a Amurka.
Dr. Craig Holman, a yanzu shi ne mai kare manufofin 'yan kasa a majalisar dokoki da ke Washington DC. Shi ne wakilin kungiyar Public Citizen kan sha'anin kudi da ka'idojin tafiyar da gwamnati. Holman na yawan bayar da darasi kan kudaden kamfe, dokokin tafiyar ga gwamnati da sauyin kamun kafa. A baya Holman babban mai nazari ne kan manufofin a Jibiyar Adalci ta Brennan, da ke Sashen Nazarin Shari'a na Jami'ar New York. Kafin sannan kuma ya kasance babban mai binciken ilimi a Cibiyar Nazarin Mulki t Los Angelos, California.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar tunani ko ra'ayoyin tsarin iditocin TRT Afrika ba.