Masu zaɓe suna kaɗa ƙuri'arsu a wata rumfar zaɓe lokacin zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jihar Michigan a Dearborn, Michigan, ranar 27 ga watan Fabrairu shekarar 2024. / Hoto: AFP    

Saura wata ɗaya kafin Amurka ta gudanar da zaɓenta na shugaban ƙasa da ke tafe. An fara zaɓen wuri a watan Satumba, kuma aƙalla Amurkawa dubu ɗari biyar tuni sun kaɗa ƙuri'arsu.

Yanayin da ake ciki a Amurka na ɗarɗar ne.

A cikin gida, tana fama da ɓarnar da ta biyo bayan Guguwar Halene, da kuma yajin aikin ma'aikatan tashoshin jirgin ruwa da ke yi wa farfaɗowar tattalin arziƙi barazana.

A ƙetare kuwa, Amurka na ci gaba da goyon bayan ƙazamin yaƙin da Isra'ila ke gwabzawa a Gaza na tsawon shekara ɗaya, da mamayar Lebanon da ta yi a baya bayan nan da faɗaɗa zaman yaƙin da Iran.

Yayin da ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ke nuna mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da tsohon shugaban ƙasa Ronald Trump suna kankankan a gogayyar shiga fadar White House, duk wani zaɓin manufar ƙasashen waje da za a yi wannan watan zai iya bai wa ɗan takara nasara.

Dambarwar siyasa

Tun watan Oktoba da ya gabata, yaƙin da Isra'ila ke gwabzawa a Gaza ya rusa yawancin yankunan da aka mamaye kuma ya halaka dubbanin Falasɗinawa.

Masu zangazangar goyon bayan Falasɗinawa suna nuna adawa da hare haren da Isra'ila ta ke kai wa kan Gaza da Lebanon yayin wata zanga zanga a Birnin New York ranar 26 ga watan Satumba 2024(REUTERS/Shannon Stapleton).

Wannan ɓarnar da aka yi da kuma rayukan da aka rasa sakamakon harin bamabamai babu ƙaƙƙautawa ko shakka babu shi ya kamata ya zama abin da za a mayar da hankali a kansa a halin yanzu da ma tsawon lokacin da za a kwashe ana wannan tashin hankalin.

Amma la'akari na biyu shi ne dambarwar siyasa daga wannan yaƙin. Waɗannan al'amuran ko shakka babu ana jin su a jika a cikin isra'ila da ma faɗin yankin; amma fagen siyasar Amurka ne ya fi shiga tasku.

Musamman, alaƙa ta bayyane da shugaban ƙasa Joe Biden ke da ita da ta'adin da Isra'ila ke yi wa mutanen Gaza ya fusata masu kaɗa kuri'a na Demokarat.

Matasa masu zaɓe da Amurkawa Baƙar fata - al'umomi biyu da jam'iyyar Demokarat ba za ta yi sakacin rabuwa da su ba - suna daga cikin na gaba gaban masu sukar gwamnatin.

Babu mamaki, amma al'umomin da suka fi bayyana rashin gamsuwarsu su ne Larabawa da Amurkawa Musulmai.

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna raguwar farin jinin Biden cikin sauri a shekarar 2024, idan aka kwatanta da shekarar 2020. Yanzu da ba ya takara, shin Musulmi da Larabawa sun sauya matsayinsu? Amsar tana da sarƙaƙiya.

Ra'ayi mai jirwaye game da Harris

Da farkon lokacin da Harris ta zama ƴar takarar shugaban ƙasa ta jam'iyar Demokarat, Larabawa da Musulmi da dama suna da niyyar ba ta dama. Tun da sanannen abu ne ita ce jami'a mafi girman matsayi a gwamnatin Biden da ta yi kira da a tsagaita wuta.

Bugu da ƙari,ana daukar cewa tana ɗan tausayawa idan aka zo batun halin ƙuncin da Falasɗinawa ke ciki.

Amma dai ɗasawar ba ta yi wani nisan a zo a gani ba.

"Idan kuna so Donald Trump ya yi nasara say ku faɗi hakan, idan ba haka ba kuma ni ina magana."

Kamala Harris ta ƙeƙasa ƙasa ta ƙi cewa komai kan kiran tsagaita wuta a Gaza da masu goyon bayan Falasɗinawa suka yi a gangamin yaƙin neman zaɓe a Detroit, a maimakon haka sai ta zaɓi ta kora su waje. pic.twitter.com/LiRWbK8AM7

A wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Michigan (cikin duk wurare fa) jim kaɗan bayan Biden ya janye daga takarar shugaban ƙasar, wasu masu zangazanga da ke kira da a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki game da yaƙin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza, sun katse Harris tana jawabi, inda mataimakiyar shugaban ƙasar ta yi ƙus kamar ruwa ya cinye ta.

Abin da ya fi takaici ma shi ne ƙin yarda Ruwa Romman, wata Bafalastiniya ƴar majalisar dokokin jihar Georgia ƴar jam'iyar Demokarat ta yi jawabi a babban dandamalin Taron Ƙasa Na Demokarat a watan Agusta.

Ta shirya ta yi kira da a tsagaita wuta sannan kuma ta nuna goyon bayanta ga Harris ta zama shugabar ƙasa. Wannan shi ne lokacin da masu kaɗa ƙuri'a da ke mutunta ta tun farko suka hasala.

Idan Harris ba ta ga dacewar ta amince, ko da ta ganin ido ce kuwa, masu kira ga Amurka ta hukunta Isra'ila su ce wani abu ba, to ta yaya masu kaɗa ƙuri'a da suka san me suke yi za su aminta da ita cewa za ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki idan ta zama shugabar ƙasa?

Bincikenmu na baya bayan nan ya nuna cewa Musulmin Amurka masu zaɓe za su iya zama raba-gardama a jihohin da ake kai ruwa rana kamar Michigan da Pennsylvania da Georgia da Arizona da Nevada da kuma Wisconsin. Duk da buƙatu mabanbanta, bai kamata ƴan takara a duk matakai su dinga wasa da damar yin jawabi kan damuwar da Musulmi ke nunawa ba... pic.twitter.com/xUtlF1ozhu

— CAIR National (@CAIRNational) ranar 10 ga watan Satumba shekarar 2024

Saboda haka ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya bayan nan har wa yau, ta ƙara nuna akwai masu ji an yi watsi da su.

Wani bincike da Majalisar Zamantakewar Musulmin Amurka (CAIR) ta gudanar a watan Agusta bai nuna Musulmi masu zaɓe da yawa na goyon bayan Harris a galibin manyan jihohin da ake raba-gardama kamar Georgia da Pennsylvania da kuma Arizona ba.

Har wa yau, a muhimmiyar jihar Michigan, Harris na bin bayan ƴar takarar wata jam'iyyar da ba Demokarat ko Rifublikan ba Jill Stein da wani rinjaye mai gwaɓi-kashi 12 na waɗanda aka gudanar da binciken kansu ne kawai suka ce sun shirya zaɓar ƴan takarar jam'iyyar Demokarat, yayin da kashi 40 suka goyi bayan ɗan takarar jam'iyyar Green Party.

Yanke Shawara mai wahala

Duk da haka, yayin da zaɓen ke ƙaratowa, har yanzu Larabawa da Musulmi suna nazari kan sakamakon ƙuri'arsu-da kuma cimma matsaya mabanbanta.

Wasu sun bayyana matsayinsu ƙarara kamar Kungiyar Musulmi ta Engage Action, wadda ta goyi bayan Kamala Harris, ko Amer Ghalib, magajin garin birnin Amurka ɗaya tilo da Musulmi ke jagoranta, wanda ya mara wa Donald Trump baya.

Reuters: Magoya bayan masu goyon bayan mutum ya yi zaɓe ba tare da yi wa wani ɗan takara alƙawarin ƙuri'arsa ba gabannin zaɓen fid da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar Demokarat a Hamtramck, jihar Michigan, ranar 25 ga watan Fabrairu shekarar 2024 (REUTERS/Rebecca Cook). 

Har wa yau akwai wasu fitattun mutane daga cikin al'umomin Musulmin Amurka waɗanda a bayyane suka ƙarfafi ƴaƴan al'ummar da su zaɓi wani ɗan takarar.

Alal misali, ƴan kungiyar Muslims for Harrise-Walz, sun kaddamar da shirinsu ta hanyar ganawa ta intanet ta manhajar webinar da ya haɗo kan ɗinbin Musulmi ƴan siyasa a matakan gwamnati dabam dabam.

Saɓanin haka, gwamman fitattun malaman addini daga faɗin ƙasar a baya bayan nan sun wallafa wata wasiƙa suna buƙatar Musulmi a Amurka su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na wata jam'iyyar banda Demokarat da Rifublikan, suna cewa "mun doge kan matsayinmu na ƙin goyon bayan kowacce jam'iyyar siyasa ko ɗan takarar da ya shiga dumu dumu kuma ya taimaka da kuɗi wajen gudanar da tashin hankalin da ba a saba ganin irinsa ba (a Gaza)."

Amma da dama daga cikin Musulmi masu zaɓe ba su cusa kai sosai ba.

Kungiyar Waɗanda ba sa yi wa ɗantakara alƙawari ta ƙi ta goyi bayan Harris. Har ila yau kungiyar ta yi gargaɗi game da shuagabancin Trump saboda haka, ta bayar da shawarar kar a zaɓi ɗan takarar wata jam'iyyar ta dabam.

Jill Stein tana gaban Harris da Trump a tsakanin Amurkawa Musulmi masu kaɗa kuri'a a jihohin raba-gardama, rahotanni suka nuna https://t.co/8fFyYHbBS5

— USA TODAY (@USATODAY) ranar 17 ga watan Satumba shekarar 2024

Haƙiƙa ruɗanin siyasa mafi daidai da Amurkawa Musulmi suka shiga ya fito ne daga kungiyar mata Musulmi ta Muslim Women for Harris, waɗanda kowa ya kama gabansa a tafiyar bayan abin da DNC ta yi wa Romman, sai kuma kawai suka sauya ra'ayi, suka sake goyon bayan takarar Harris ɗin kuma.

Ƙungiyar ta ce dalili ɗaya na aikata hakan shi ne saboda hatsari ƙarara da shugabancin Trump zai iya jefa al'umomin baƙar fata da jar fata ciki."

Haƙiƙa abu ne mai wahala ka yi tababar cewa zuwan Trump a wa'adi na biyu zai zo tare da ƙalubale na musamman ga al'umomi marasa rinjaye a Amurka. Idan aka yi la'akari da shaguɓen da yake yi wa (ƴan ciranin da ba farar fata ba) a yaƙin neman zaɓensa, abin da zai iya haifar da manufofin da ba su tsaya ga yi wa ƴan cirani tarnaƙi ba kaɗai, har ma jefa rayuwar halattattun ƴan cirani da ke Amurka cikin garari za su yi.

Tare da waɗannan taka-tsantsan ɗin akwai ƴan takarar jam'iyyar Green Party. Nuna son kai wajen yin allawadai da laifuffukan yaƙi da na gaba gaba a takarar, Jill Stein ke yi yana damun mutane da yawa a cikin al'ummar Musulmin Amurka.

And so many Arabs, Muslims, and others for whom Gaza is a top priority have become those unicorns of American politics: undecided voters.

Saboda haka da yawan Larabawa, Musulmi da sauran mutanen da suka ɗauki lamarin Gaza da muhimmancin gaske sun zama na musamman a siyasar Amurka: masu zaɓe da ba su yanke shawarar wanda za su zaɓa ba.

A halin da ake ciki, abokin takararta,Butch Ware, ya sha kakkausar suka a baya bayan nan, bayan ya nuna cewa waɗanda suka zaɓi Kamala Harris suna iya ja wa kansu hukunci har bayan rayuwarsu.

Saboda haka da yawan Larabawa, Musulmi da sauran mutanen da suka ɗauki lamarin Gaza da muhimmancin gaske sun zama na musamman a siyasar Amurka: masu zaɓe da ba su yanke shawarar wanda za su zaɓa ba.

Amma a maimakon zama wanda bai yanke shawarar wanda za ka zaɓa tsakanin manyan jam'iyun guda biyu,galibinsu sun rabu ne tsakanin zaɓar ƴar takarar jam'iyyar Demokarat ko zaɓar ɗaya daga cikin ƙananan jam'iyun ko ma fasa zaɓen kwatakwata

Idan dai ba wani lamarin siyasa da ba a yi tsammani ba ne ya bujuro, wannan ƙaulanin zai iya kaiwa watan Nuwamba. Duk da haka, idan "wani abin mamaki ya faru a watan Oktoba" tabbas zai zama ba wani abu ba ne sabo a wannan lamari na siyasa.

Marubucin Youssef Chouhoud mataimakin farfesan kimiyyar siyasa ne a jami'ar Christopher Newport, inda yake aiki tare da Reiff Center for Human Rights and Conflict Resolution. Bincikensa yana nazarin ra'ayoyin jama'a ne kan marasa rinjaye a Amurka sannan kuma da taimakon tabbatar da aƙidun dimokuraɗiyya a Yankin Gabas Tsakiya. Har wa yau yana da tarihi mai faɗi a fannin yaɗa ilimi game da ɗabiun Musulmin Amurka. Kafin ya fara aiki da CNU, Dr Chouhoud shugaban ne a jami'ar Kudancin California inda ya samu digiri na uku.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, fahimta da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.

TRT Afrika