Sai dai har yanzu mutane kadan ne suka san yadda wannan sassasken ya taimaka wajen daga martaba da sauya tarihin zane-zane /Hoto: Reuters

Daga Lisa Modiano

A tsakiyar shekarar 1907, lokacin da Pablo Picasso yake ta fafutikar gano hanyoyin da zai bi wajen zama fitaccen masassaki na daban a duniya, sai ya ci karo da wani dan sassasken Vili daga Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Sai dai har yanzu mutane kadan ne suka san yadda wannan sassasken ya taimaka wajen daga martaba da sauya tarihin zane-zane.

Nan da nan sassaken ya ba shi sha’awa ganin yadda aka tsara shi da tsawo da tsari mai kyau, wanda tun wancan lokacin, Picasso wanda a lokacin yake da shekara 25 ya samu sauyin tunani.

Sannan ziyarsa zuwa Gidan Adana Tarihi na Paris Ethnographic Museum da ke Trocadero, inda akwai dubban kayyakin tarihin kasashen Afirka da aka sace, sai ya kara samun kusanci da zane-zanen nahiyar, sannan ya kawo masa wani sabon tunani game da rayuwarsa ta fasaha.

Mai fasahar sai ya fara tattara sassake-sassake da mutum-mutumi, inda har ya kai ya tattara sama da guda 100 da suke bayyana irin fasahohin inda ya zauna a tsawon rayuwarsa.

Bayan ya dawo daga ziyararsa daga Trocadero, sai Picasso ya koma wani wajen zane-zanensa da bai kammala ba, wanda ya yi kama da wani wajen da yake yawan ziyarta a wani otel da ke birnin Barcelona a kasar Spain.

Zane-zanen Afirka ne ya sanya wa Picasso Pablo kwarin gwiwa / Hoto: AA

Wannan aikin shi ne Les Demoiselles d’Avignon, wanda a yanzu ake wa kallon sassakar da ta sauya yanayin sassake-sassaken karni na 20.

Sassakar ta kai kusan mita biyu da rabi, sannan tana da fadin mita biyu da doriya, wanda ke nuna karuwai shida masu kama da juna, sannan uku daga cikinsu na hararar mai kallon zanen.

Da wannan zanen wanda aka cire tsoro wajen yi, zanen na Les Demoiselles d’Avignon ya kauce daga tsarin kawa, wanda ya ba har na kusa da Picasso mamaki.

Duk da zanen mata biyu na tsakiya ya nuna alakar mai zane da al’adu na yankin Iberia, wanda ya kunshi Spain da Portugal da Andorra da Gibraltar da wani bangare na Faransa.

Siffar sauran matan da suke cikin zanen suna kama ne da mutanen yankin Kudancin Saharar Afirka, na sassaken takunkumi da suke sanyawa a fuskokinsu.

Fuskokin matan da ke kasa a gefen dama, wadanda aka zana da kala daban-daban suna kama da tsarin al’adar sassaken takunkumin Mbuya na mutanen Pende, wanda a al’adar ce da ake yi bayan kaciya.

A saman gefen daman zanen, fuskar matar na kama da yanayin sassaken takunkumin rufe fuskar matan kabilar Dan na kasar Ivory Coast, wanda ke bambanta da yanayin tsawon hancinsu da babban goshi.

Sai Picasso da wasu abokan aikinsa suka fara daga farko, inda suka fara bayyana yanayin Afirka mai kyau, inda suka sauya tunanin da aka dade ana yi cewa makasudin fasahar zane-zane shi ne a kwaikwayi yadda duniya take a al’adance.

Mikakken zane mai dauke da manyan layuka da kuma yadda yake saukaka zane, ya sa zane-zanen Picasso suka zama daban, inda hakan ya sa ya bambanta da tsarin masu fasahohin Turawan Yamma tun wajajen karni na 14 zuwa 16.

Tasiri

A wannan lokacin ne aka assasa Cubism-Wadda kungiyar fasaha ce da ke kokarin tabbatar da bukatar da ke akwai na bambanta zane da zahiri-wanda daga lokacin da aka fara samun kungiyoyi masu ra’ayin rikau game da sauya yanayin fasaha wadanda suka kawo sauyi a karnoni na gaba.

Pablo Picasso ya cika shekara 50 da rasuwa a 2023 / Photo: AA

Babu wani dalili bayyananne cewa Picasso da makarantar Paris, wadda ke matukar shaukin irin zane-zanen mutanen da sun yi la’akari da Afirka a da al’adun mutanenta.

Da aka tambaye shi tasirin Afirka wajen zana Les Demoiselles d’Avignon, sai Picasso ya yi gaggawar bayyana tasirin yankin Iberia, sannan har ya musanta wata alaka da yake da ita da fasahohin bakake, inda ya ce, “Fasahar bakake? Ban santa ba,” inji mai zanen cikin wulakanci.

Masu sassakar da da sauran masu fasahohi na da wadanda na zamanin yanzu suke kwaikwaya domin bunkasa harkokinsu har yanzu ba a sansu ba.

Don haka a cikin abubuwan da suka sa ake yi wa Picasso kallon daya daga cikin wadanda suka kawo sauyi da cigaba a harkar zane da fasaha, wanne da wanne ne ya aro daga Afirka - sannan me ya sa ba a bayyana tasirin nahiyar a ayyukansa, wadanda a bayyane suke?

A bana ne ake bikin cika shekara 15 da mutuwar Picasso. Domin girmama ranar mutuwarsa, Faransa da Spain sun hada hannu domin nuna ayyukan fasahohin Picasso da za a kwase kusan shekara ana yi da suka sanya wa suna Celebration Picasso 1973-2023.

Za a nuna sama da ayyukansa guda 50 daga kwalejojin fasaha na Turai da Amurka domin girmama tasirin Picasso a fasaha, da kuma jawo hankalin mutane a kan wasu ayyukansa da ba su yi fice ba.

Wasu daga cikin tsare-tsaren da aka yi za shi ne bayyana alakarsa da wasu mutanen da suka yi tasiri a rayuwarsa, ciki har da Gertrude Stein da Joan Miro da Max Becham da Chanel da El Greco.

Sai dai daga cikin tarukan 50 da za a yi, ba a tanadi ko guda daya ba domin nuna alakar Picasso da Afirka ba.

Amfani da kaloli

Duk da cewa a shekarar 2017 a wani taron Baje Kolin Fasahohi da aka yi a gidan tanada kayan tarihi na Musée Du Quai Branly da ke Paris (wanda a da ake kira Trocadero, inda a nan ne Picasso ya fara samun abubuwan da yake bukata wajen kammala zanen Les Demoiselles d’Avignon) da aka yi domin binciko alaka mai zanen da fasasohin wasu da ba Turawan Yamma ba, wannan ne kadai kwalejin da aka taba shirya irin haka.

Idan har duniyar fasahohi na so ta habaka tare da janyo kowane bangare, dole ta amince da gudunmowar da tarihi ya nuna wasu sun bayar /Hoto: AA

Wannan ya sa ake tambayar: Tunda masu fasahohin Afirka sun dade suna amfani da kaloli wajen bayyana fasahohinsu, me ya sa a tarihin cigaban fasahohi ba a bayyana gudunmuwarsu?

Kamar yadda wani malamin bayan samun ’yancin kai mai suna Simon Gikandi ya bayyana, ana farawa ne da bayyana gudunmuwar Afirka a tarihin cigaban fasahohi, amma ana sauran jefa su a kwandon shara.

Wannan ba yana nufin mu mayar da Picasso da cigaban fasahohinsa kacokam kan satar fasahar Afirka da wasu kasashen na Turawan Yamma ba, domin a karni na 20, ba lokacin ba ne farkon siyasar mulkin mallaka.

Goge tarihi da gudunmuwar Pablo Picasso ga fasahohi shekaru da dama bayan mutuwarsa ba zai yi wani tasiri ba, amma gibin da aka samu zai taimaka wajen ba mu dama wajen waiwaiye da kuma lura da ayyukansu.

Bayan haka, tambayoyin da masu tasowa za su yi ta yi ne za su dabbaka tare da habaka tarihin fasahohin nan.

Idan har duniyar fasahohi na so ta habaka tare da janyo kowane bangare, dole ta amince da gudunmowar da tarihi ya nuna wasu sun bayar.

Maimakon tunanin cewa alakanta ayyukan Picasso da Afirka zai rage kimarsa, kamata ya yi masu ruwa da tsaki a bangaren su san yadda za su sanya wadannan labarun - sannan watakila ma su yi tunanin yadda wadannan kayayyakin tarihin da suka sauya tunanin mutane da dama za su samu daukakar da suka cancanta.

(Sassakar da Picasso ya ci karo da ita, wadda mutane Vili na Congo suka sassaka a tsakanin karni 19 zuwa farkon karni na 20 daga BBC)

(Les Demoiselles d’Avignon wanda Picasso ya yi a shekarar 1903 daga MoMA, New York)

Zanen rufe fuska na mutanen Tsakiyar Pende, da ke Bandundu na Jamhuriyyar Congo daga Mujallar Apollo; takunkumin takato na tsakanin karni 19 zuwa tsakiyar karni na 20 daga Gidan Adana Tarihi na Metropolitan Museum of Art

TRT Afrika