Na samu nasara kan Jami'ar Bristol wadda ta kore ni daga aiki a matsayin Farfesa a watan Oktoban 2021 bayan gangamin watanni talatin da masu rajin kafa kasar Isra'ila suka yi na neman a kore ni.
Daga cikin hukuncin da kotun ta yanke, akwai abun mamaki. Na san Brsitol ba su gudanar da cikakken bincike game da ƙorafin da aka yi a kaina ba, ko su auna me ya kamata su yi, wanda shaidun Bristol har sau biyu sun tabbatar da hakan a gaban kotu.
Su ne suka bincike ni tare da kora ta. Sun gabatar da shaidar tasu ne a watan Oktoba. Shaidun Bristol ne suka jefa su rami a kotu.
Kai ta kai ga ma an yi babbar illa ga Bristol ta hanyar dabarun shari'a da suka yi aiki da shi wajen bayar da shaidar manyan jami'anta biyu. Su suka nutsar da Bristol a cikoin ruwa. Bari dai na yi bayani.
Jami'ar Bristol ta bincike ni har sau uku. A kowanne bincike ba a samu shaida ko alamar nuna kyamar Yahudawa ba a rubutu ko kalamai na. Wani kamfani mai zaman kansa na waje ne ya gudanar da bincike na biyu da na uku a kaina.
Jami'ar, har zuwa yau ta ki bayyana wa duniya me aka gano game da ni, ta ki fadin babu a wani waje da na yi rubutu ko na fadi kalaman nuna kyama ga Yahudawa.
A sanarwar da suka fitar a lokacin da aka kore ni, sun fadi cewa kawai "bincike ya samu Farfesa Miller's ayi kalaman da suka karya doka".
An ga wannan rashin gaskiya a yadda suka tunkari kotun. Ana kira tare da fara shari'ar, sai lauyoyin Bristol suka bayyanawa kotu suna son sauya kararsu.
A baya sun amince da cewa ra'ayin da na bayyana sun cancanci a girmama su, amma a sabuwar bukatarsu ga kotu, wanda cikin sauri suka shirya ta email tare da aikawa kotun da sassafe, suna cewa ra'ayina na adawa da kafa kasar Yahudawa kamar yadda shaida ta ta bayyana na da hatsai, kuma akwai wata kulla-kulla a ciki."
Haka kuma, sun bayyana cewa ra'ayina na adawa da kafa kasar Yahudawa daidai yake da nuna wariyar launin fata, a saboda haka ya kamata a kalubalance shi "bai kamata a girmama haka a tsarin demokuradiyya ba".
Wannan ne kalamin shari'a da aka yi amfani da shi a Dokar 'Yanci, wadda ta fayyace ra'ayoyin falsafa.
Wannan dabara ce mara kyau saboda ta yi ikirarin tunanina na kyamar wasu al'ummun, daidai yake da tunanin Nazi, wanda hakan ne ya sanya bai kamata a girmama tunanin ba.
Wannan zai zama dabara mai rikitarwa, amma sai lauyoyina suka yi amfani da wannan dama wajen tirsasa shaidun masu gabatar da kara wajen bayar da bayanan da suka saba da abun da suke kara a kai.
Farfesa Judith Squires ce babbar jami'a ta biyu mafi girma a Jami'ar Bristol, masaniyar siyasa ce inda ta rubuta litattafai da dama kan daidaiton jinsi, kuma ta yi rubutu kan ra'ayin dan Faransa Michel Foucault da yake bincike kan alakar karfi da siyasa.
Ya kamata a kuma fahimci cewa Squires ta jagoranci assasa wani tsari a Jami'ar; wajen dora ta kan tsarin adawa da masu nuna wariyar launin fata.
A watan Oktoban 2020 Squires ta yi wata lacca wadda jami'ar ta saka a shafinta na Youtube mai taken "Samar da Jam'ar da Babu Mulkin Mallaka". A laccar tata, Squires ta bayyana cewa "Alhakin kowa ne a kan mu mu tashi mu yaki nuna wariya".
A yayin da ta bayar da shaida, Farfesa Squires ta ce tunanina ba su da darajar da za a girmama su a cikin al'ummar da ke dabbaka dimokuradiyya, amma ta karkare da tabbatar da cewa ta dauka tunanin kafa kasar Yahudawa daidai yake da nuna wariya, ai kalaman nata suka zama kamar masu cin karo da juna.
Daga kallon irin matakan da ake dauka na yaki da nuna wariya, hakan ya sake bud ekofar gano akwai na'uika na nuna wariya daban-daban da ba za a kawar da su ba.
Tabbas, bayan bayanin da na yi ne cewa Ra'ayin kafa kasar Yahudawa ba daidai yke da nuna wariya ba, amma sai aka ce na aikata laifi mafi muni a wajensu.
A wani kaulin, irin nuna wariyar da Faladinawa, Larabawa ko Musulmai dalibai ke fuskanta wanda ke da masa babba daga Zionism, har yanzu hukumomi irin su Bristol ba su dauke su da muhimmanci ba.
Na bayyana haka a lokacin da ake wa hakan kallon matsala saboda z ata janyo hayaniya a Jami'a.
A wata fahimtar kuma za a iya cewa muhawara kan adawa da mai nuna wariya na bayyanuwa ne a harshe ko adawa da nuna wariya zuwa yin barazana a cikin makaranta.
Ra'ayin ya sake tabbatuwa gare ni bayan da Farfesa a bangaren nazarin shari'a ya kalli batun ta wata suga ta daban. Kungiyoyin Musulmai sun zargi Farfesa Geer Nuna Kyamar Musulmi, a daidai lokacin da ni ma ake zargi na.
Ya soki kungiyoyin Muslman ta siga mafi kaushi sama da yadda na gabatar da tsarin Zionism ga Dalibai. Bristol ba su yi masa wani gargadi ba, kuma a su kore shi ba, lauyoyi da dama a kotu sun bayyana ba a yi mana adalci irin daya da shi ba.
Gaskiyar zance shi ne Jami'o'in Birtaniya kamar sauran al'ummu d asuke cikin su, ba su wani damu da nuna kyama ga Musulunci da ya shafi hukumomin gwamnati ba, kuma suna da sakamako mai muni da ya shafi aikata muggan laifuka, kyara da 'yan sanda da jami'an tsaro ke yi, da ma hana damarmakin tattalin arziki.
Alkaluma sun bayyana cewa a Ingila, Musulmai ne mafi karancin samun damarmakin tattalin arziki, suna karbar kudade kadan a wuraren aiki.
Amma maimakon a dauki matakan kawo gyaran magance wannan gibi, sai ake ta kokarin nuna ai Yahudawa ne ke fuskantar barazanar nuna wariya wariya da danniya a kasar.
Wannan na kai ga batun wuce gona da iri na tsanantar 'sabon nau'in kyamar baki' da kuma yadda hukumomi suka ki kalubalantar nuna wariyar masu ra'ayin kafa kasar Yahudu. A batu na gaskiya, bari mu ari kalmomin Finkelstein: 'Yahudawan Birtaniya na da arzkki, ilimi da samun nasarar sana'o'i'.
Rashin niyyar kalubalantar Zionism da kuma karbar akidar 'sabon nau'in kyamar Yahudawa' na nufin a wurare da dama da suka hada da hukumomin gwamnati, ana waswasin adawa da Zionism shi ne adawa da nuna wariya.
Wannan ne ya snaya nasarata a kotu ke da muhimmanci sosai. Ta kawo wa sauran kotunan Ingila cewar ra'ayin adawa da Zionism ba nuna wariyar launin fata ba ne "kuma sun cancanci a girmama su".
Wannan babbar nasara cewa ba wai don kariyar da hakan ke baiwa mutane ba a wajen ayyuka. Za kuma ta zama a fagen muhawara wajen kalubalantar "sabon nau'in nuna kyamar Yahudawa".
Sama da shekara hamsin gwamnati na aiki kan wannan batu kuma ta yi ta kokari assasa shi ya zama a hukumanace da sunan ma'anar kyamar Yahudawa 'a aikace" wanda a karon farko a watan janairun 2005 Kungiyar Sanya Idanu ta Tarayyar Turai ta amince da shi a matsayin sunan aiki na sabon salon nuna kyama ga Yahudawa.
Hakan ya faru ne bayan kamun kafa da bibiya tare da rokon da Yahudawa suka dinga yi.
Kwararru a fannin shari'a sun soki wannan kudiri saboda yadda yake kallon kalaman goyon baya Falasdinawa a matsayin babban laifi. A 2007 wata kungiya ta maye gurbin ta sanya idanun, Kungiyar Kare Hakkoki ta Turai.
A 2013 FRA ta bayyana cewa ma'anar da aka baiwa hukumar da ta maye gurbi, ba nata ba ne kuma ba ta da ma hurumin amincewa da irin wannan sabon ta'arifi.
Hakan ya sanya a 2015 Masu rajin kafa kasar Yahudawa fara tunanin neman sabuwar hukuma da za a ta amince da sabo nau'in kyamar Yahudawa, kuma ya zuwa 2016 sun yi nasarar assasa ta a sabuwar kungiyar Yahudawa ta 'International Holocaust Remembrance Alliance'.
A yanzu matakin da kotuna ta dauka na kalubalantar duk wannan kokari na kamun kafa da roko, kuma zai samar da yanayin kalubalantar sabon ta'arifin kyamatar Yahudawa, wanda a karshe ma zai kalubalanci Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Turai.
Watakila wannan hukunci na kotu ya fara bayar da sabon tabbaci ga masu goyon bayan Falasdin wanda ba a damu da su ba, da ma irin hare-haren da ake kai musu da sunan 'kyamatar Yahudawa' kuma sun shirya amfani da kalmar Zionism a inda ta dace.
Hukumar IHRA na a karfin iko wajen jan ra'ayin masu goyon bayan Falasdinawa da su daina amfani da kalmar 'Zionism' (Rajin Kafa Kasar Yahudawa) ko "Gwagwarmayar Zionism".
Karar jiniya a bangaren hagu na nufin mu yi amfani a kalmar a wasu lokuta na musamman. Kawai mu dinga suka gwamnatin Isra'ila da manufofinta, ko mu fito a keta hakkokin ɗan'adam da ake yi karara, ko amfani da kalmar kyamar baki.
Sun kuma ce mu daina ambaton yunkurin halasta ayyukan masu rajin kafa kasar Yahudu.
A wasu lokutan kuma. saboda suna kalubalantar kawo karshen matattarar masu rajin kafa kasar Yahudawa, a wasu loktan kuma suna yin hakan bisa dalilai na dabarun dabbaka manufofi. Ko ma mene ne, ya kamata wannan abu ya kawo karshe.
Ya kamata mu fahimta karara cewa ra'ayin Zionism ra'ayi ne na nuna wariya, mamaya da kisan kiyashi, kuma ya kamata mu dinga amfani da matattarar 'yan Zionism, kuma ya kamata a fahimci cewa wannan gwagwarmaya ta masu rajin kafa kasar Yahudu ya kamata a rusa baki daya, ba wai iya mamayar da suke yi a Falasdin a yanzu haka ba.
Marubicin, David Miller, Babban Mai Bincike ne a Cibiyar Nazarin Musulunci da Harkokin Kasa da Kasa a Jami'ar Zaim, kuma tsohon Farfesan Siyasar Zamantakewa a Jami'ar Bristol.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.