Daga Husam Maarouf
A taron da ya ɗauki hankali sosai a ranar Asabar a Dandalin Falasɗinu da ke Gaza, Hamas ta gabatar da sojojin Isra'ila mata su hudu, da aka kama a ranar 7 ga Oktoban 2023, jim kaɗan kafin sakin su.
Baya ga nuna ƙarfi a zahiri, taron ya kuma fito da yadda Hamas take, yana ƙalubalantar irin labaran da ake bayarwa game da karfin ɓangarori daban-daban a yankin da ake ci gaba da yaƙi. Wajen taron, yadda ya cika da jama'a, na da ma'ana ta musamman, da ke buƙatar yin nazari a kanta.
Sojojin da aka kama sun hau teburin taron, ba a matsayin waɗanka aka kama suna karkarwa ba, sai a matsayin lafiyayyu da ke cikin nutsuwa. Suna sanye da kayansu na sojoji, sun nuna yadda suke a nutse, babu wani abu da ya samu tunaninsu, lafiyarsu ƙalau ga annushuwa - lamarin da daga baya mahukuntan Isra'ila suka tabbatar.
Ɗaya daga cikin sojojin Isra'ila ta kitse kanta, abu ne da kamar ba shi da muhimmanci, amma kuma babbar alama ce mai girma. Yadda aka yi kitson na bukatar lokaci mai yawa, yana nufin kulawa da mallakar kai, da kuma ruhin mutuntaka. Wannan ɗan ƙanƙanin hoto ya ƙalubalanci dukkan labaran da ake bayarwa na cewar ana cusguna wa fursunonin da aka kama.
Ta hanyar wadannan bayanai zababbu, Hamas ta dinga kira ga magoya bayanta da su sake tunanin da suke da shi, sun gabatar da wadannan fursunonin yakin ba a matsayin abin tausayi ba, sai dai a matsayin jigon siyasar da ake yi a yankin.
A yayin da sojojin suka sauka daga motar Hamas, sun gaishe da taron jama'ar - da murmushi da ɗaga hannu. Dubunnan mutanen da suka halarci wajen sun amsa da shewa, da busa usur, da dariya, suna bayyane cikin yanayin da babu tsoro ko firgici a cikin sa.
Yadda aka yi musayar gaisuwa tare da shewa tsakanin dandazon jama'a da wadanda aka kama aka saki, ya kawar da duk wata farfaganda da ake yada wa ta lokacin yaki.
Babu alamun wata wahalarwa ko fuskantar cuzgunaw a fuskokinsu, babu wani alamun an dauki fansa a kansu. Maimakon haka, dariya ba kakkautawa da ɗaga hannun da suke ta yi na bayyana suna cikin yanayi na tsaro, kai ka ce suna wajen da aka dakatar da yaki na wani ɗan lokaci.
Shewar jama'ar wajen ba iyakacin goyon baya ga Hamas take bayyanawa ba, har ma da zama masu tasirantuwa da alamu da sakonnin da ake son aikawa.
Sarƙar Keffiyeh
Kowace soja ta karbi kyauta, wanda Hamas ta ba su. A wuyansu kuma an rataya sarkoki na shaida, tambarin Kefiyyeh na isra'ila ne a jiki.
Waɗannan ba kawai kayan kawa ba ne; suna matsayin tunatarwa kan gwagwarmayar Falasdinawa. Kefiyyeh, alamar tirjiya da bijirewa, na bayyana nauyi da matsayin tijiyar da aka ɗauki shekaru ana yi.
Yin ado da kwalliya a wuyan fursunonin yakin, na nufin halascin Falasdinawa da gwagwarmaya. Kamar hamas na cewa ne "Ko a lokacin da kuke tsare, kun shaida me muke fafutuka a kai."
A dandalin, a bayan mata sojojin da za a saki akwai babbar tutar Falasdin da kuma tambarin farmakan Al-Aksa. Wadannan alamu na da zuzzurfar ma'ana da muhimmanci, suna sake jaddada alamun nasara da juriya, tare da gabatar da hoto a bayyane game da labaran da ake fada game da Falasdinawa.
Makamai a matsayin nasarori
Mayakan Hamas da ke dauke da makamai daga baya sun hau kan minbarin, suna daga manyan makamai da ake cewa sun kwace a yayin harin 7 ga Oktoba. Wadannan ba 'yan bata ruwa a yaki ba ne kawai, sun zama alamu na nasarori ba wai ga rundunar soji kadai ba, har ma ga bayyana bijirewa mamaya da tsayuwa don kalubalantar karfin da Isra'ila ke amfani da shi.
Yadda aka ajiye wadannan makamai tare a sojojin da ke murmushi ya samar da hoto da tunanin da ba za a taba manta wa da shi ba. A yayin da tsayuwarsu a kan minbarin ta zama mai tunatar da cewa har a gaban masu kallo, gaskiyar rikici na karkashin irin farfagandar da ake yada wa ta hanyar karin gishiri a miya.
Aikin ƙarfin iko
Yadda Hamas ta zaɓi ta gabatar da fursunonin yaƙin a cikin ƙoshin lafiya, suna murmushi tare da mu'amala da dandazon jama'ar, wani sako ne da ake son isarwa. Hakan na nuna kishiyar irin halin wahala da aka jefa Falasɗinawa a ciki a kowacce rana. Tare da bayyana wannan jadawali da nuna wayewa, Hamas na son ƙalubalantar yadda ake bayyana mayaƙanta a matsayin mugaye marasa imani da tausayi.
Duk da haka a ƙarƙashin wannan lamari, akwai alamun tshin-tashina da tunanin yadda yaki ya zauna a kwakwalen jama'a - ta hanyar sanya idanun mayakan Hamas a koyaushe, kallon da suke yi sararin samaniya na nuna musu yadda jiragen yakin Isr'ila suke shawagi, wanda ke tunatar da matsalar da bil'adama yake shiga a wannan rikici da ya shafi dukkan ɓangarorin biyu.
Dariya da nutsuwar sojojin Isra'ila ba alamun halin da suka samu kansu da mu'amalar da aka yi musu kawai ke fayyacewa ba, har ma da zama wani tsararren shiri na ƙalubalantar duk abubuwan da ake faɗa. Wannan batu ne na nuna su ne a sama, da kuma tunatarwa da cewa har ma a lokacin da ake tsare da su, sojojin sun zama masu shiga manyan ayyukan tirjiya.
Taron ya zama mai mayar da hankali ga juya akalar abubuwn da ake faɗa, a jaridu da kafafen yada labarai, kamar yadda yake kuma nuna karfi, kuma a wannan fage, Hamas tana so ta sake bayyana kanta a matsayin ba wadda ke kiyaye Gaza kawai ba, har ma da zama gwagwarmaya halastacciya da ke bisa tushen adalci.
Har ma wanzuwar Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross - wadanda suke wajen don karbar sojojin na Isra'ila tare da mayar da su kasarsu - sanya hannu kan takardu karkashin babbar tutar "Ambaliyar Al-Aksa" na aikewa da bayanannen sako.
A yayin da shigar su lamarin ke sake tabbatar da matsayin kula da dan'adam, hakan na kuma kasancewar su a tsakiya a cikin yanayin siyasar yankin. A wajen Hamas, wannan lokaci ne na bayyana halasci, da nuna matsayinta na gwagwarmayar nuna tirjiya da iya kula da fursunonin yaki.
A wajen Kungiyar Red Cross kuma, lamarin ya zama mai rikitarwa kan cika aikinsu na jin kai da kuma kaucewa shiga tsaka mai wuya a lamarin. Sanya hannun kansa - wata alamar tsari ko da ana tsaka da rikici - na bayyana kishiyar yaki da rauni da haɗari.
Kulawar da ba a gani a bayyane
Taron na Dandalin Falasdinu ya kasance mai kunshe da rassan babban yaki - wajen da karfi da nuna kai da jajircewa suka hadu a lokaci guda. Kowanne motsi da duk abin da ya faru sako ne a wajen, na bayyana tirjiyar mutanen da ke ci gaba da yaki da mamaya ta raba su da matsugunansu. Lamari ne da ke bayyana karfi da kasancewar cikin haɗari ga wadanda lamarin ya shafa, yana aike wa da sakon da ke ruguza labaran da aka ta bayarwa a kafafen yaɗa labarai game da rikicin.
A yayin da duniya ke kallo, wani abu guda da ya bayyane karara shi ne; gwagwarmayar neman adalci da 'yanci a Falasdin batu ne na sake fasalin me ake bayar da labari a kai, matukar dai zai kasance game da gaskiyar abubuwan da ke faruwa. Wannan fage na yaki batu ne na abinda ake gani da idanuwa da wanda ke a ɓoye, takunkuman rufe fuskar da muka saka da kuma furskokin da ke cikin su.
Husam Maarouf Bafalasdine ne mai rubuta waƙoƙi kuma marubuci da ke Gaza, wanda ya rubuta makaloli da yawa, ciki har a Raseef22 da Al Jazeera.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.