Wani mai zanga-zanga ya tsere wa wani ɗansanda yayin tarzomar ƙyamar baƙi a Rotherham, Birtaniya, 4 ga Augusta , 2024. / Photo: Reuters

Daga Khalida Khan

Kafofin watsa labarai da ƴan siyasa na ci gaba da bayyana tashin hankalin baya-bayan nan a Birtaniya a matsayin 'tarzomar ƙyamar jinsi.' Idan ana son magance wannan matsala, akwai buƙatar mu kalli halayyar ƙin jinin Musulmi daban da sauran halayyar ƙyamar jinsi kuma a tunkare su daban-daban.

A nan Birtaniya, mun fuskanci tarzomar ƙyamar Musulmi, amma ba za ka fahimci hakan ba. Idan ka karanta rahotannin kafafen watsa labarai na 'yan makwannin da suka gabata, ba za ka yi tunanin cewa ƙyamar Musulmi ita ce ummul-aba'isin tarzomar a faɗin ƙasar ba.

Wata ɗaya tsakani, kowa na maganar zanga-zangar 'kyamar jinsi' ko kuma 'tarzoma'. Wata muƙalar BBC kan yadda ya kamata Firaministanmu ya magance "tushen" abubuwan da suka haddasa tarzomar ba ta ambaci kalaman ɓatanci kan Musulmi ko da sau ɗaya ba. Kuma ranar Juma'a, wani kwamitin MDD ya buƙaci Birtaniya ta ayyana dokoki da za su daƙile kalaman ɓatanci da nuna kyamar baƙi, amma shi ma bai ambaci nuna ƙin jinin Musulunci ba.

Sai dai kuma, masu tarzomar ba su hari majami'u, da wurin bautar Yahudawa, da wurin bautar Hindu da kuma wurin bautar addinin Shikh ba, amma sun far ma masallatai, a wani lokacin ma, har da ƙaburburan Musulmi. Tarzomar ƙin jinin Musulmi a Southport ta samo asali ne daga labaran ƙarya ta kafar intanet da ke cewa wai mai laifin da ya kashe ƙananan yara mata su uku a wani ajin koyar da rawa Musulmi ne kuma baƙon haure.

Ko shakka babu, Musulmai masu tarzomar suka afkawa, abin da daga bisani ya bazu zuwa kan ƴan Asiya da baƙaƙen fata.

Komai yana da sanadi. Nuna kyamar Musulmi mai tarihi, da kuma tattaunawa kan ƙin jinin Musulmi a kowane mataki na al'umma a ƙasar nan tsawon gwamman shekaru, saura ƙiris ake jira.

Abin da ya faru a Southport shi ne sanadin

Ɓoye munin nuna kyamar Musulmi

Yayin da wasu ƴansiyasa da rahotanni kafofin watsa labarai da farko suka yarda cewa Musulmi aka kai wa hari a tarzomar watan jiyan, amma yanzu ana nuna rashin muhimmancin wannan batun.

Birtaniya na da dokokin da suka ƙyale kotuna su zartar da hukunci kan laifuffukan nuna ƙin jinin wani addini, amma kawo yanzu, kamar ana tuhumar masu tarzomar ne da aikata laifuffukan nuna kyamar jinsi ba ƙyamar addini ba, abin da ya ƙara bayyana kau da kai kan babban abin da ya haddasa ƙin jinin Musulmi.

Idan zatona ya zamo gaskiya, za ta iya yiwuwa cewa gwamnatin jam'iyyar Labour ba za ta tunkari batun nuna kyamar Musulmi kai tsaye ba, ko ta wata takamammiyar hanyar bincike a nan gaba ba.

Yin hakan zai zama sauya tunani gabaɗaya da kuma tattaunawa kan matsayin da ake kai, kuma ya kunshi yin gagarumin sauyi manufofi - a illahirin harkokin gwamnati, da da Tsarin Shari'ah, daga ayyukan kula da walwala, da fahimtar buƙatun Musulmi, da kuma yadda ƴansanda ke gudanar da laifuffukan nuna ƙin jinin Musulmi.

Birtaniya ta ƙara zama ƙasa mai kunshe da mutane masu al'adu daban daban, amma ɓullar aƙidar ƙin Musulmi da ƙyamar baƙi na nuna yiwuwar ita ma tana ƙara zama mai nuna wariyar launin fata. https://t.co/aK9ANW6RAA

— The New Yorker (@NewYorker) 25 ga watan Agusta, 2024

Ta yaya muka tsinci kanmu a nan? An jima ana musa wanzuwar nuna kyamar Musulmi a tattaunawa a Birtaniya. A maimakon haka, kafofin watsa labarai da bangaren jama'a da kuma gwamnatin sun fi son su dinga kallon matsalar ta fuskar jinsi.

Nau'in ƙyama iri biyu

Da yawa ba za su fahimci cewa yana da muhimmanci a banbance tsakanin ƙin jinin Musulmi da kuma nuna wariyar jinsi ba. Bari na yi bayani.

Kafin ka samu shawo kan matsaloli yadda ya kamata, dole ka gano ainihin abubuwan da suke haddasa matsalolin. Ba za ka gwama ƙin jinin Musulmi tare da nuna kyamar jinsi ba, domin ƙiyayya ne guda biyu mabanbanta. Suna buƙatar matakai mabanbanta bisa manufa kafin a samu kyakkyawan sakamako.

Aƙidar Ƙin jinin Musulunci wani mummunan nuna bambanci da tsoron Musulmi ne a tunanin mutanen yammacin duniya, wanda ya haifar da cin zarafi da nuna wariya.

Sama da shekaru dubu har rana mai kamar ta yau, yankin Turai ya yi hannun riga da Musulunci ta fuskoki da dama. Ka tuna shekaru 800 ta daular Muslunci a Sifaniya, da yaƙe yaƙe kafa addini kirista da kuma daular Usmaniya a nahiyar Turai. Waɗannan yaƙe yaƙen sun yi sanadiyar wasu masana tarihi da ƴansiyasar Turai suna nuna cewa Musulmi dodanni ne, fasiƙai, masu danne haƙƙoƙin mata, masu ɗabi'ar dabbobi, kuma yanzu ƴan'ta'adda ne, mutane ne da suka kasance barazana mai yawa ga yammacin duniya.

Tallata Larabawa mutanen banza ne

Idan kana so ka fahimci dalilin da ya sa aka dasa ƙiyayyar Musulmi a tunanin mutanen yammacin duniya. Ɗaya daga cikin dalilai da dama shi ne yadda kafofin watsa labarai suke gabatar da Larabawa/Musulmai

Ka kalli wannan fim ɗin game da yadda masana'antar Hollywood take gabatar da Larabawa/Musulmi.https://t.co/A26ITkuWqY via @YouTube

— An-Nisa Society (@AnNisaSociety) August 21, 2024

(kalli fim ɗin Jack Shaheen mai suna Reel Bad Arabs). Duk wannan an sanya shi a tarihin nahiyar Turai, da adabi, da fasaha da kafofin watsa labarai da kuma Hollywood.

Lokacin da aka juya maka tunani a fakaice domin ka ji tsoron kuma ka tsaki Musulunci da Musulmi, ba za a daɗe ba ƙin jinin Musulmi zai ɗarsu a zuciyarka sannan ya rikiɗe ya zama ɗabi'ar nuna banbanci, da cin zarafi da kuma kai hare hare. Wannan shi ne tarihin aƙidar ƙin jinin Musulunci. Ba batun launin fata ba ne, face wata daɗaɗɗiyar aƙidar nuna wariya da ƙiyayya kan Musulunci da Musulmi.

Wariyar jinsi kuma a ɗaya bangaren, nuna banbanci ne ta fuskar launin fata da asalin mutum. Shi ma yana da nasa tarihin.

Ya wanzu ne bisa mazhabobi kan jinsi, inda jinsin farare suka ɗauki kansu madaukakin jinsi yayin da jinsi baƙaƙe da jajayen fata ake musu kallon maƙaskanta. Duk waɗannan ire iren nuna wariyar guda biyu ana amfani da su wajen halarta mulkin mallaka.

Wani lokaci aƙidar ƙin jinin Musulmi da wariyar launin fata suna kama da juna, amma dole a tunkare su a matsayin nau'o'in ɓatanci mabanbanta.

Wani lokaci aƙidar ƙin jinin Musulmi da wariyar launin fata suna kama da juna, amma dole a tunkare su a matsayin nau'o'in ɓatanci mabanbanta, kafin a samu kyakkyawar masalaha ga kowannensu.

A Birtaniya, wata kungiya mai adawa da wariyar launin fata a shekarun 1950, domin magance nuna banbanci saboda launin fatar mutum, tsantsar babu ruwanta da addini, kuma ita batun launin fata kaɗai a gabanta. Hasali ma, da gangan aka zare batun addini da nuna banbanci addini daga kungiyar, saboda "yawan kawo rarrabuwar kai" kamar yadda Ambalavaner Sivanandan, shahararren ɗan fafutikar yaƙi da wariyar launin fatar nan da kansa ya sheda min, a wani wajen bayar da horo.

Sabuwar kungiyar a Birtaniya ta fara ne lokacin da sababbin ƴancirani masu launin fata da addinai mabanbanta suka iso Birtaniyar bayan kammala yaƙin duniya na biyu, inda suka fuskanci cin zarafi saboda jinsinsu, da kai hari kansu da tarzoma da kuma kisan gilla mai nasaba da jinsin mutum.

A shekarun 1970 da 1980, al'ummomi mabanbanta sun haɗa kai saboda ana kai mana hare hare dukkanmu don launin fatarmu. Amma ko ma a wancan lokacin, akwai dabi'un ƙyamar Musulmi idan da ka lura, a sigar yi wa wani ɗalibi Musulmi kisan gilla, a wata makaranta mai ɗabi'ar ƙin jinin Musulmi, da kuma kashe wani matashi ɗan gidan kaso a tsakiyar jami'an gidan kaso masu aƙidar ƙyamar Musulunci.

Ba a taɓa tantance waɗannan batutuwan ƙin jinin Musulmi ba a matsayin haka ba saboda mahukuntan wariyar launin fata suka gani ba ƙyamar addini ba.

Daidaiton jinsi ba a kasa da Musulmi ba

Sakamakon tarzomar wariyar jinsi ta farkon shekarun 1980, gwamnati ta umurci bangaren hukuma da ya ƙaddamar da shirye-shiryen daidaiton jinsi. A matsayina na jami'i mai kula da hulɗar jinsi, babu daɗewa na fahimci cewa, haɗa kai domin yaƙar wariyar launin fata wani abu ne daban, amma kuma, ƙaƙaba mana wasu sunaye a matsayin baƙaƙen fata da ƴan yankin Asiya, sannan da yin amfani da su a matsayin ma'aunin yin hidima ga al'ummomi masu addinai da al'adu mabanbanta a bangaren hukuma, shi ma wani abu ne daban.

Gaskiyar magana, babban koma-baya ne ga al'ummar Musulmi. Ko shakka babu, Dokar Hulɗar Jinsi ta shekarar 1976 ta kare al'ummomi bisa jinsunsu ne kaɗai, amma Musulmai, kasantuwar tarin ƙabilu mabanbanta kuma mabiya addini ɗaya ne, ba a ba su kariya ba.

Na fara ganin rashin fahimtar wanzuwar Musulmi a wajen gwamnati da hukumomin gwamnati; a wajen su, ba ma wanzuwa.

A cewar wani bincike bayan afkuwar lamarin da international initiative More in Common suka gudanar, kashi 53 na mutanen da aka tambaya suna da ra'ayin cewa "Birtaniya yanzu tana da hatsari ga Musulmai" idan aka kwatanta da kashi 38 kafin tarzomar da masu tsattsauran ra'ayi suka yi.(Reuters).

Musulmai sun daɗe da kasancewa, kuma har yanzu, al'ummomi masu rangwamen tagomashi a fannin zamantakewa da tattalin arziƙi da kuma kiwon lafiya a Birtaniya, kuma hakan ya faru ne saboda an zamar da su kamar ba sa wanzuwa da gangan; imma ta rashin samun a yi musu ayyuka, ko ayyukan da aka yi musu na je-ka-na-yi-ka ne ko kuma waɗanda ba su dace ba.

Alal misali, idan aka zo batun ɗaukar renon yara da riƙe su na dindindin, ana saka ƴaƴan Musulmi a rukunonin da ake la'akari da jinsi a maimakon waɗanda ake la'akari da addini. Saboda haka za a saka yaro Musulmi ɗan Nijeriya tare da yaro Kirista ɗan Afrika da yankin Caribbean, sannan yaro Musulmi ɗan Pakistan a haɗa shi da yaron indiya mai bin addinin Hindu.

A wajenmu Musulmi, babban muhimmin abu a wajenmu shi ne ya kamata ƴaƴan Musulmi a miƙa su cikin Iyali Musulmai, ko da kuwa ƙabila ko jinsi ba su zo ɗaya ba.

A Birtaniya, shirin kidayar jama'a babu tambaya kan addini har sai a shekarar 2001, saboda da haka, mawuyacin abu ne sosai a iya sanin girman wariyar da Musulmi suke faskanta.

kamun ƙafa domin samun canji

A shekarar 1985, na kafa kungiyar An-Nisa, domin ta yi aiki don jin daɗin iyalan musulmai da kuma wayar kai kan batutuwan da na zayyano.

Ya saɓa wa doka ka nuna wa wani wariya saboda wata kararriyar sifa.

Dokar Daidaito ta ambaci sifofi guda tara, da suka haɗa da addini da imani.

Wancan ya haɗa da rashin imani da kowane #addini.

Nemi ƙarin bayani: https://t.co/WKByvwn9YQ pic.twitter.com/r2QYe4gSGr

— EHRC (@EHRC) 6 ga watan Yuni, 2023

Bayan tsawon shekaru ina kamun ƙafa da jan hankalin, an samu nasarori ƴan ƙalilan, da kuma gagarumin tagomashi, da ya haɗa da Dokar Daidaito ta shekarar 2010 wacce daga karshe ta ƙunshi "addini da imani" a cikin rukunin waɗanda suke da kariya. Yanzu muna da doka da ta ce babban laifi ne mutum ya aikata laifi mai nasaba da cin zarafin wani saboda addini da kuma tunzuwa don a ƙin jinin wani don addini.

Aikinmu kan shirye shiryen zamantakewa, kamar bai wa al'ummomin Musulmi shawara, shi ma ya nuna yadda shirye shirye masu nasaba da addini suke iya wanzar da kyawawan sakamakon zamantakewa da tattalin arziƙi.

Amma duk da waɗannan cigaban, tare da ƙarin Musulmi yanzu suna cikin siyasa da ayyukan gwamnati, aƙidar ƙin jinin Musulunci ta ƙaru, kamar yadda aka sheda a tarzomar.

Wannan saboda an fi ɗaukar mataki a kan jinsi ne.

Akwai buƙatar Musulmai su ilmantar da kansu.

Babban cikas ga magance aƙidar ƙin jinin Musulunci su ne Musulmai da kansu.

Shugannin al'ummomin Musulmi, waɗanda ba su fahimci yadda aƙidar ƙin jinin Musulunci ke gudana ba, kuma an riga da an wanke musu ƙwaƙwalwa kan cewa ƙin jinin Musulunci daidai yake da wariyar launin fata, ba sa bai wa gwamnati da masu tsara manufofi wani misali na zahiri mai yiwuwa don magance aƙidar ƙin jinin Musulunci tsakani da Allah.

Ƙyamar Musulunci a hukumance ya fi yin mummunan tasiri a kan Musulmi. Yayin da ba sa saka rai da komai na daga hidimdimun da suka dace ta fuskar addini da al'ada daga hukumomin gwamnati, ba su fahimci cewa rashin samun waɗannan hidimdimun kai tsaye yana haifar da tafiya ba tare da su ba ta fuskar zamantakewa. A maimakon haka, sun saba da kallon komai ta mahangar "jinsi" da kuma amincewa da matsayin da ake kai kafin yanzu.

Babban koma-baya da tafiyar ta ci karo da shi, shi ne fassarar da kungiyar yan majalisar dokoki Musulmi na duka jam'iyyu (APPG) ta yi a shekarar 2017, kan aƙidar ƙin jinin Musulunci da ta ce, wani "nau'i ne na wariyar launin fata", abin da ya rusa duka nasarorin da muka samu, waɗanda suka samu karɓuwa sosai kuma ƴansiyasa da shugabanni Musulmai suka tallata su yadda ya kamata.

Muna da tamu fassarar da muka yi wa kalmar pic.twitter.com/rMW2vyUzv9

— Kungiyar An-Nisa Society (@AnNisaSociety) 7 ga watan Auguta, 2024

Fafutikarmu ta yakice aƙidar ƙin jinin Musulunci daga wariyar launin fata ta samu koma-baya da wannan fassarar.

Abin da zai biyo baya

Abin da zai biyo bayan tarzomar ƙin jinin Musulunci, ina tsoron cewa ƙasata za ta koma gidan jiya na kallon al'ummomi marasa rinjaye a matsayin kungiyoyin "jinsi" sannan su dinga ɗaukar mu gabaɗayanmu tamkar wata dunƙulalliyar al'umma da ta ƙunshi mutane mabanbanta.

Abin da hakan zai zama shi ne idan gwamnati ta ɗauki wani mataki na ganowa da magance musabbabin tarzomar, za a kalle su ne ta mahangar jinsi. Aƙidar ƙin jinin Musulunci za ta saje da wariyar launin fata sannan ba za a samu ƙwaƙƙwaran mataki a hange da dabarunsu ba.

Amma fa sake gabatar da tsofaffin matakai da dabaru masu nasaba da jinsi da suka kasa haifa wa Musulman Birtaniya ɗa mai ido tsawon gwamman shekaru ba mai yiwuwa ba ne.

Ba ni da wani ƙwarin guiwar cewa za a samar da wasu manufofi a hukumance da za su magance ƙyamar Musulmi a inda ta bayyana, da ya haɗa da dandalin sada zumunta,da fagen siyasa da kuma hukumomi, ana bari a ci zarafi da kuma ƙasƙantar da Musulmi.

Amma fa sake gabatar da tsofaffin matakai da dabaru masu nasaba da jinsi da suka kasa haifa wa Musulman Birtaniya ɗa mai ido tsawon gwamman shekaru ba mai yiwuwa ba ne.

Amma Dokar Daidaito ta samar mana da matakan magance aƙidar ƙin jinin Musulunci ta yadda ake tafiyar da mu da kuma yi mana ayyukanmu, akwai buƙatar mu yi amfani da shi yadda ya kamata. Yanzu muna da dokoki da za su magance aikata laifin ƙin jinin Musulmi, amma dole sai mun matsa wa ƴansanda da Tsarin Shari'ah lamba su yi amfani da su. Wannan wata dama ce ta kawo sauyi.

Gwamman shekaru, idan da mun ɗauki matakan da suka dace domin magance aƙidar ƙin jinin Musulunci, kuma da mun jajirce wajen samar da kungiyar farar hula ta Musulmi mai tafiya da zamani da za ta iya biya mana tarin buƙatunmu kuma ta iya tsaya mana cikin ƙwarewa - da wataƙila ba mu samu kanmu a halin da muke ciki yanzu ba.

Marubuciyar, Khalida Khan, tana daga cikin waɗanda suka assasa kungiyar An-Nisa Society kuma Daraktarta ce. Kungiyar mai mazauni a Birtaniya, wacce ke aiki wajen gina al'ummar Musulmi farar hula mai tasirin gaske. A matsayita ta mai rajin kare haƙƙin bil adama kuma ƴar gwagwarmaya sannan marubuciya a kan al'amuran da suka shafi addini, da yi wa jama'a hidima da kuma ayyukan sa kai, kuma mashawarciya ce ga kafofin watsa labarai da masu bincike. Khan har ila yau ita ta ƙagi kalmar aƙidar ƙin jinin Musulunci a hukumance, domin ta gano manufofi da aikace-aikace da ke nuna wa Musulmi wariya da ƙyama.

TRT Afrika