Wannan ya hada da ayyukan ilimi da lafiya, wadanda za su samu nakasu sakamakon martanin bankin kan dokar hana badala. Hoto: AFP
Daga Hamza Kyeyune

Bankin Duniya yana amfani da wasu kudade da zai bai wa Uganda bashi, da suka kai dala biliyan biyu, don tursasa kasar da ke gabashin Afirka ta sauya dokar haramta luwadi da auren jinsi.

Zuwa yanzu, Uganda ta nuna tirjiya a wannan tataburza da kasar da take da rinjayen Kiristoci, inda bankin na duniya yake nuna karfi da amfani da wani batu da ba shi da alaka da tsarin samar da kudi don ayyukan ci gaba.

Tataburzar ta fara ne a watan Mayu, yayin da shugaban Uganda Yoweri Museveni ya rattaba hannu kan Dokar Haramta Luwadi, dokar da ya jaddada cewa ta wajaba domin kawar da al'adar 'yan luwadi masu neman sauya tunanin mutane.

Sabuwar dokar ta kunshi hukuncin kisa a inda abu ya kazanta, wanda ya hada da jima'i tsakanin masu jinsi guda tare da wanda bai kai shekara 18 ba, ko kuma mu'amalar da ta haifar da wani ya kamu da cutar da ba a warkewa, kamar HIV.

A hirar da na yi da 'yan majalisar dokoki da jami'an gwamnatin Uganda, tunaninsu shi ne Bankin Duniya da yake da mazauni a birnin Washington DC, wanda kuma Amurka take da karfi a cikinsa, ya wuce gona da iri.

Asuman Basalirwa, wanda ya gabatar da kudurin dokar a majalisa, ya fada min cewa Uganda ba ita kadai ce kasar da take da dokoki kan mu'amalar da ta saba wa dabi'a ba, “yawancin kasashen Afirka suna da dokokin. To, me ya sa suka ware Uganda?".

Basalirwa da kuma sauran 'yan majalisu suna da hujjojin da ke nuna cewa Bankin Duniya yana neman hanyar "dakatar da ba wa Uganda bashin kudi ne, shi ya sa yake amfani da wannan dokar a matsayin dalilin dakatar da ba mu kudi".

Abin da Bankin Duniya ya fada na cewa dokar Uganda ta haramta luwadi, "ta saba wa muradun Bankin Duniya", tamkar suna nuna cewa 'yan Uganda suna bukatar neman izinin Amurka kafin kafa doka a kasarsu.

Bankin Duniya mai ba da rance ga kasashen duniya, ya samar da dala biliyan $5.4 na kudaden da Kungiyar Cigaban Duniya ta International Development Association (IDA), ta bai wa Uganda har zuwa karshen 2022.

Wannan ya hada da ayyukan ilimi da lafiya, wadanda za su samu nakasu sakamakon martanin bankin kan dokar hana badala.

Hannun Amurka

Kusan a ko yaushe Amurka tana tabbatar da dan kasarta ne yake jagorantar Bankin Duniya, kuma ita ce ke amfani da bankin wajen tursasa Uganda.

Tuni Amurkan ta sanya takunkumin bulaguro kan jami'an Uganda, sakamakon dokar hana luwadin.

Martanin Uganda bai zo da mamaki ba, domin ta yi watsi da matakin a matsayin munafurcin Amurka, inda ta ce "Masu kaunar mulkin mallaka ne suka yi wa Bankin Duniya matsin-lamba, kamar yadda suka saba".

Rashin ba da kai da gwamnatin Uganda ta yi, duk da yiwuwar rasa biliyoyin daloli na kudin aiwatar da ayyuka, ya faru ne sakamakon cewa dokar ta samu rinjayen goyon bayan al'ummar kasar mafi yawansu masu bin addinin Kiristanci.

'Yan majalisar dokokin sun kare dokar saboda ita ce hanyar kare al'ummarsu daga ta'adar badala ta kasashen Yamma.

Kuma akwai alamun rashin adalci a yadda Amurka, da ma Bankin Duniya suke fayyace mene ne 'yancin dan'adam.

Dan majalisa Basalirwa ya zargi Bankin Duniya da nuna bambanci, kuma ya yi mamakin yadda ake daukaka batun 'yancin 'yan luwadi kan batun 'yancin 'yan Ugandan da aka keta nasu 'yancin.

Ya fada min cewa, "Tsawon shekaru Bankin Duniya ya yi shiru. Me ya sa suke so su mayar da duka duniya ta dauka cewa 'yancin 'yan luwadi yana da fifiko, kuma wai dole a yaki dokar da za ta takaita 'yancin."

Tursasawar Bankin Duniya

Da yawan 'yan Uganda suna kallon matakin na Bankin Duniya na amfani da samar da kudi don tursasa muradunsa, a matsayin wani farmaki kan 'yancin kasar wajen kafa dokoki. Akwai matsaya kan cewa dokar wani zabi ne na jama'ar Uganda ta hanyar 'yan majalisunsu.

Wannan ra'ayi na al'ummar Uganda shi ne abin da jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Adonia Ayebare ya bayyana, inda ya kira matakin na Bankin Duniya da zalunci da karfa-karfa. Ya yi imanin cewa lokaci ya yi da bankin zai sake tunani kan mu'amalarsa ta aiki.

Ministan Uganda na harkokin waje, Okello Oryem, shi ma ya yi suka kan fuska biyu na banki, inda ya ce, "A Amurka, jihohi da dama sun yi dokar da ta saba ko ta takaita ayyukan 'yan luwadi. Me ya sa suka ware Uganda da tsana?"

Babu makawa, matakin na Bankin Duniya zai cutar da tattalin arzikin Uganda a gajeren zango.

Na yi tattaunawa da Dr Fred Muhumuza, kwararre kan binciken tsare-tsare, wanda ya ba da bayanin cewa matukar Bankin Duniya ya dakatar da bashin na tsawon lokaci, abubuwa da dama za su iya faruwa.

Dr Muhumuza ya ce min, "Za mu iya rayuwa ba tare da bashi ba, idan muka sauya tsarin kashe kudinmu, da ayyukan da muke son mu yi a yanzu, da nemo wasu hanyoyin samun kudi".

Yawancin irin tunanin na jami'ai da masana, ba sabon abu ba ne. Da ma can akwai tunanin neman wasu hanyoyin nemo bashi.

Kasashen Afirka ya kamata su kara haraji na cikin gida, don samar da kudin yin ayyuka. Kuma yanzu ya kamata hakan ya faru.

Marubucin, Hamza Kyeyune, babban masani ne kan Sadarwa kuma kwararren dan jarida ne a Uganda.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar ra'ayoyi, da mahanga, da tsarin editan TRT Afrika.

TRT Afrika