Hayaki na tashi sakamakon harin bam ta sama da Isra'ila ta kai wata unguwa a wajen birnin Beirut ranar 17 ga watan Nuwamban 2024. Hoto: AFP

Gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden na ƙara zage damtse wajen ganin an tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

A baya-bayan nan ne mai shiga tsakani na Amurka Amos Hochstein ya tattauna da Nabih Berri, kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon mai ƙawance da kungiyar Hezbollah, kan kudirin tsagaita wuta da Amurka ta yi, da ke neman kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa.

Dukkaninsu Hezbollah da gwamnatin Lebanon sun ba da izinin tsagaita wuta a bisa sharadi, kuma Hochstein yanzu yana Isra'ila don ganin an cim ma matsaya. Ko yaya, ci gaba da ta'azzarar yaƙin na haifar da ƙalubale ga ƙoƙarin shiga tsakani na Amurka.

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a gabashi da kudancin Lebanon a yayin da ake tattaunawa, kuma tana son 'yancin daukar mataki' kan kungiyar Hezbollah a duk wata yarjejeniya.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta ɗauki alhakin kai harin makami mai linzami mafi muni a Isra'ila cikin sama da shekara guda, kuma ta ɗora wa Firaministan Isra'ila Benyamin Natanyahu alhakin shimfida ginshikin batun tsagaita.

Don haka ko yunƙurin tsagaita wuta na ƙarshe na Washington zai iya haifar da sakamako da gaske? Ga abin da ke kan hanya.

Mabambantan buruka

Da alama gwamnatin Biden ta mai da hankali sosai kan kare muradun Isra'ila sabanin inganta tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya. Wannan yana ƙalubalantar amincin tattaunawar da ke gudana.

Yi la'akari da yunƙurin da Washington ta yi na sake aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701. Ya yi kira da a rusa ƙungiyar r Hezbollah tare da ƙin amincewa da kasancewar makamai ba tare da izini ba a kusa da iyakar Isra'ila da Lebanon.

Duk da cewa yarjejeniyar ta taimaka wajen kawo karshen rikicin Isra'ila da Lebanon a shekara ta 2006, Washington ba ta nuna alamu sosai ba na ba da fifiko ga wasu muhimman tanade-tanade, kamar kawo karshen dukkan hare-haren soji na Isra'ila a kan iyakarta ta arewa.

Son kan da Washington ke nunawa yana taimakawa wajen bayyana rashin amincewar Isra'ila ga zaman lafiya. Netanyahu ya sha alwashin kai hari kan kasar Labanon duk da tsagaita wuta da aka yi, kuma munanan hare-hare ta sama da aka kai a gabashin Lebanon na nuni da cewa ana ci gaba da kai hare-hare.

Idan Washington na son hana tashin hankali a nan gaba, dole ne ta yi la'akari da manufar Lebanon ta karfafa hare-haren da Isra'ila ke kaiwa yankinta. Bayan haka, Isra'ila na da tarihin yin amfani da kariyar kai wajen ba da hujjar kai hare-hare kan Lebanon.

Wannan ya hada da gomman hare-haren da suka tura kasashen biyu shiga yaƙi a cikin watan Agusta. Akwai kuma fargaba a Lebanon cewa Isra'ila za ta iya amfani da wasu tanadin tsagaita wuta domin kai hare-hare kan kasar nan gaba.

Maimakon kawar da wannan fargaba, Washington ta ci gaba da ba da fifiko ga "yancin kare kai" na Isra'ila a cikin daftarin kudirinta. Idan har ba a sauya ba, ana iya kallon hakan a matsayin amincewa da bukatar Isra'ila ta kai farmaki kan kungiyar Hezbollah bisa ga son rai, lamarin da ke haifar da ayar tambaya kan matakin da Amurka ta dauka na shiga tsakani a halin yanzu.

Rusa Hezbollah

Na biyu, yunƙurin kwance wa Hezbollah ɗamara ba shi ne kadai zai yi tasiri a a kan samar da zaman lafiya ba. Aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 ya bukaci dukkan masu dauke da makamai ciki har da Hezbollah su bar makamansu a wani yunkuri na kawo karshen yaƙin.

Sai dai a shekarun da aka fara aiwatar da kudurin, kungiyar Hezbollah ba ta kwance damara ba. A maimakon haka ma sai ta zama runduna mai cike da makamai masu tarin yawa, waɗanda Iran ke ba da kuɗaɗe da kuma samar da su.

Akwai bukatar Amurka ta amince da gaskiyar cewa kawar da wanzuwar kungiyar Hezbollah zai yi wahala, kuma amincewarta na da matukar muhimmanci kafin duk wata yarjejeniya ta fara aiki.

Amma hakikanin gaskiya na nuna cewa Amurka tana tsara nata shirin. Misali, Washington na son sojojin Lebanon su tunkari Hezbollah sakamakon tsagaita wuta. Wannan wani mataki ne da ba shi da hurumi a cikin Lebanon amma ya yi daidai da bukatun Isra'ila na hana kungiyar ƙarfafa dakarunta.

Idan an cim ma matsaya, sojojin na Lebanon na iya bukatar tura dubban sojoji a kudancin kasar. Sai dai za ta yi kokarin kauce wa arangama da kungiyar Hezbollah, wadda kasancewarta ta soja da na siyasa ya ba ta karfin gwiwa a jihar.

Don haka, ainihin abin da Amurka ke buƙata a shiga tsakani ya wuce kwance wa Hezbollah ɗamara da kuma fito-na-fito. Shin za ta iya samun tabbacin tsagaita wuta daga Isra'ila, gami da hanzarta janye sojojin da amincewa da 'yancin Lebanon na kare kanta?

Wani mutum ɗauke 'yarsa yana wucewa ta gefen wani gini da harin Isra'ila ya lalata a Beirut ranar 18 ga watan Nuwamban 2024. Hoto: (REUTERS/Adnan Abidi).

Kalubalen da Washington ke fuskanta sun yi zurfi sosai: ko da Isra'ila ta ba da wannan tabbacin, akwai kyakkyawan dalili cewa Lebanon za ta ci gaba da nuna shakku kan sulhu.

Akwai kuma irin barnar da Isra'ila ta yi wa Lebanon a cikin watanni da dama da suka wuce. Akalla mutum 3,500 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama, yayin da sama da miliyan guda suka rasa matsugunansu.

Fashewar wayoyin hannu da aka samu a watan Satumba ya ƙara dagula al'amuran tunani a tsakanin jama'a, wadanda tuni ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Isra'ila ta yi ɓarna a gine-ginen Lebanon cikin makonni biyu fiye da abin da ya faru a cikin watanni 12 da aka kwashe ana gwabza fada a kan iyaka. Hakan ya sanya fushi da baƙin cikin a kan talakawa.

Dalilan siyasa

Wani cikas ga zaman lafiya ya haɗa da dalilai na siyasa. Jami'an Isra'ila na ci gaba da fafutukar ganin an tsagaita wuta saboda suna son neman amincewar zababben shugaban Amurka Donald Trump.

A ra'ayinsu, yuwuwar yarjejeniyar za ta karfafa wa'adin Trump na kawo karshen yakin Lebanon. A sakamakon haka, zai taimaka wa Isra'ila ta nemi goyon bayan Amurka don ƙarin yarjejeniyar daidaitawa da ƙasashen Larabawa.

Tattaunawar baya-bayan nan da aka yi tsakanin Trump da Ron Dermer, ministan kula da tsare-tsare na Netanyahu, ta bayyana karara cewa babbar manufar Isra'ila ita ce ta faranta wa gwamnatin da ke kan karagar mulki, sabanin tsagaita wuta da Hezbollah.

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon (UNIFIL) wani abu ne mai iyaka. Sojoji na ci gaba da kai hari kan jami'an nasu, kuma ana tuhumarsu da "lalata kadarorin UNIFIL da ba a iya gane su ba da gangan" a kudancin Lebanon.

Wannan yana da muhimmanci saboda Amurka tana son cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta wanda ya hada da fadada rawar UNIFIL wajen sa ido kan tsagaita wuta, da hana keta haddi daga kowane bangare.

Sai dai wannan yunkurin na fuskantar ƙaƙa-ni-ka-yi idan Isra'ila ta ci gaba da yin illa ga kasancewar UNIFIL a kusa da "Blue Line", layin da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana tsakanin Lebanon da Isra'ila.

Har ila yau, ta tilasta wa dakarun wanzar da zaman lafiya ficewa daga wuraren da suke kan iyaka. Domin tsagaita wuta, Washington na bukatar tabbatar da janyewar sojojin Isra'ila gaba daya daga kudancin Lebanon.

Wannan ya kasance sakamako mai nisa idan UNIFIL, wacce ke da alhakin tabbatar da ficewar Isra'ila, ta ci gaba da kasancewa cikin barazana akai-akai.

Don haka an fahimta, ƙalubalen sun fi ƙarfin damarmakin ƙoƙarin tsagaita wuta na ƙarshe na Washington. Ma'anar sulhu ita ce tabbatar da cewa bangarorin biyu sun bi kuma su mayar da martani cikin gaskiya. Sai dai hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a Lebanon da kuma bukatu masu yawa sun raunana lamarin don kyakkyawan fata.

Marubucin Hannan Hussain Babban Kwararre ne a wata cibiyar bincike ta Initiate Futures da ke Islamabad.

Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.

TRT World