Facebook na alfahari da masu amfani da shi su biliyan uku a duniya baki daya. / Hoto: AP

Daga Johnson Kanamugire

Facebook, dandalin sada zumunta na intanet mafi girma a duniya mallakin Meta da ke Amurka, na cika shekaru 20 da kafuwa a ranar 4 ga Fabrairu. Idan da a ce kasa ce ta zama, da ya zama kasa mafi yawan jama'a a duniya, mai alfahari da mazauna sama da biliyan ɗaya.

Mark Zuckerberg, mutumin da ya samar da dandalin daga gidan kwanan dalibai na Jami'ar Havard, ya zama hamsakin mai kudi, amma bai ƙoshi ba.

Ya san cewa manyan kasashe, kamar kamfanoni, na rushewa, kuma ya nutsu wajen tunanin samar da wani tsari don tunkarar makoma, wani abu da zai tattara masu amfani da yawa, musamman duba da yadda ake yawan samun abubuwan kunya kan amfani da bayanan masu amfani da shafukan intent, wanda hakan ya sanya kamfanin karkata ga saɓa wa tsarin amfani na Arewacin duniya.

Tacewa, suka da kai karar kamfanin kotu ba su yi wani babban tasiri kan karfi da mamayar da ya yi ba, wanda ta kai ga ya mallaki WhatsApp da Instagram, duk da yana fuskantar gogayya daga irin su TikTok, YouTube, Twitter da Snapchat.

Cakudawa

Sai dai kuma, cakuduwar wadannan batutuwa na sama na iya bayyana tambayar warwatsuwar sabbin masu amfani da Facebook a kudancin duniya, musamman ma a Afirka.

Wannan wani mataki ne na nasara da ya samu tun 2016, inda suka dinga kokarin ganin an samar da tsarin da yankunan da ba su da karfin intanet sun zama ana damawa da su wajen amfani da intanet.

Facebook ya fuskanci taciya, suka da kai su kara kotu. Hoto: Reuters

Kamfanin ya jagoranci yawaitar amfani da shafukan sada zumunta a Afirka, yana kawo sauyi a yadda daidaikun mutane masu sana'o'i, kasuwanci da kamfanoni ke gudanar da ayyukansu har zuwa ga wajen iyakokin kasashensu.

Kirkirar wani abu ne yake kan gaba wajen amfani da shi, ya kuma bude hanyoyin samar da sabbin abubuwa, yana bayar da damar inganta tattalin arzikin kasashe, ga kuma uwa uba hada al'ummu waje guda ta hanyar tabbatar da 'yancin bayyana ra'ayi.

Amma kuma, batutuwa irin su hana amfani da shafukan sada zumunta a wasu kasashen da matsalar yaduwar intanet na sa mutane da yawa samun damar amfani da Facebook.

Kasashen Afirka, misali su ke mafi yawan marasa amfani da yanar gizo inda suke da kaso 59 na rashin amfani da yanar gizon, kamar yadda GSMA, kamfanin sadarwa na kasa da kasa ya bayyana.

Facebook ya fara aikin warwatsa masu amfani da shi a wannan bangare na duniya, ta hanyar dadin baki da kuma alkawarin za su bayar da damar amfani d ayanar gizo ga dukkan wadanda ba su da sarari.

Daga cikin burukansa, da wahala ka ga sun tabo batun tarbiyya da sirri da suke tayar da hazo a Yammacin duniya.

Wannan ne abin da ke fayyace matsalar da suka samu a yayin kaddamar da SHirin Amfani Kyauta mai wata manufa ta daban a India a 2016.

Kare hakkokin masu amfani da yanar gizo a India, wani tsari da ya hada da manhaja da shafin yanar gizo da ke samar da damar shiga yanar gizo kyauta, na da wata boyayyiyar manufa.

Suna bayar da dama ga kamfanin ya samu isassun bayanai da yake so ta hanyar samun yawan masu amfani da mu'amalar duk wanda ya dogara kan tsarin da sauran dandalin da ke da alaka da Facebook wajen aika sakonni da sauran su.

Har zuwa yau, abin da ke damun masu fafutuka shi ne yadda aka kawo wannan tsari Afirka tare da amincewa a aiwatar da shi ba tare da rbincike da tantancewa ba.

Matasa da yawa daga Afirka na amfani da shafukan sada zumunta. Hoto: Getty Images

Cudanya da juna ta intanet

Facebook ya kara wa shirin nasu wasu muhimman abubuwa na kara karfin aiki: wayar karkashin teku mafi girma da tsayi da ta karade dukkan nahiyar a gefe guda, a daya bangaren kuma ga tauraron dan adam da zai dinga kara kai yanar gizon ga yankuna masu nisa.

Rashin tacewa da tantancewa na sanya da wahala a gano karfin tasirin da wannan shiri ke da shi, amma wani abu da aka tabbatar da shi shi ne:

Shirin samar hanyoyin sadarwa na yanar gizon ya mayar da Facebook kamar kamfanin da ke samar da intanet, wanda haka ke baiwa kamfanin damar kula da muhimman injina da wayoyin da ke isar da yanar gizo ga jama'a, da ma bayanan masu amfani.

Bayanan da aka tattara sun zama mafi yawa na bayanan masu amfani da aka tattara, wanda ke bai wa kamfanin garantin ci gaba da mamaya da samun kudade ta hanyar tallace-tallace.

Ba Facebook ne kadai a wannan abu ba, Google, OneWeb, StarLInk na Elon Musk, da Amazon ma na amfani da wannan irin wannan hanya a Afirka tare da zuba jarin samar da yanar gizo mai rahusa, duk da sunan cike gibin yanar gizon da ake da shi a nahiyar.

Watakila Facebook ya yi nasara a kokarin samun karin masu amfani a Afirka saboda wayar da kai da gangamin da yake yi wajen tallata kansa da har ta kai ga Mark Zuckerberg ya samu nasara kan mahukunta.

Babban kamfanin na kuma samun karfin iko kan dokoki da suke magana kan kare bayanan masu amfani musamman ma a kasashen Afirka da ba su da dokokin da kuma inda ba a aiwatar da su yadda ya kamata.

Sai dai kuma, bai kamata a yi biris da batun dokoki da tsare sirri ba. Kuskure ne ga wata kasa ta mika dukkan kayan sadarwarta na yanar gizo ga kamfanin da ke yunwar samun bayanai a duniya ba tare da raba daya biyu kan gaskiya ba.

Domin dakatar da mulkin mallaka a fannin samar da yanar gizo, akwai bukatar tantancewa sosai ga wadannan zuba jari.

Marubucin John Kanamugire, marubici ne a Rwanda da ya kware kan aikin jaridar abubuwan da ke jan hankulan jama'a.

Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.

TRT Afrika