Meta, kamfanin da ya mallaki Facebook da Instagram, na fuskantar zarge-zarge daga Tarayyar Turai saboda saba wa sabbin dokokin gogayya a yanar gizo na Turai inda yake amfani da tsarinsa na "Ka biya ko ka miƙa wuya" game da tallace-tallace.
A karshen shekarar da ta wuce, Meta ya kaddamar da "subscription for no ads" (Biyan kudin don kar a ga talla", inda suke gabatarwa da masu amfani da Facebook da Instagram a Turai zabin ko su bayar da kudi su daina ganin tallace-tallace ko kuma su dinga cin karo da su suna yi musu kutse yayin amfani da manhajojin.
Hukumar Tarayyar Turan ta bayyana cewa wannan zabi na tirsasa wa masu amfani ko su yarda a yi amfani da bayanansu ko kuma su biya kudin don kar su dinga ganin tallace-tallace. idan aka amince da bayanan farko da Hukumar ta tattara, za a iya cin tarar Meta kudin da ya kai kashi goma na dukkan ribar da ya samu a shekarar nan a fadin duniya. Duba ga kudaden da Meta yake bayyana ya samu, za a iya cin tarar dala biliyan 13.5/
Wata doka ta DMA da ke kula da gogayya da gaskiya a ayyukan kamfanonin sadarwar yanar gizo, ta fara aiki bayan kaddamar da ita da Tarayyar Turai ta yi a 2022.
Tana da manufar aiki kan manyan shafukan sadarwa na yanar gizo, dokar ta zama mai sanya idanu kan masu gadi d akula da bayanan manhajojin sadarwar, wadda ke da babban tasiri kan kasuwannin shafukan.
DMA ta tanadi ka'idojin hana mummunan amfani da bayanan masu amfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo a Turai.
A karkashin dokar DMA, ya zama dole masu gadi da ke kula da bayanan su nemi yardar mai amfani don hade bayanansa a shafuka daban-daban, sannan su samar da wani tsari na daban da ke kama da amincewa.
Ra'ayin farko na na Hukumar game da Meta shi ne yadda kamfanin ke aiki na tirsasawa masu amfani yarda da za a sarrafa bayanansu gaba daya, ba tare da ba su wani zabi ba, wand ahakan ya sbaa wa ka'idojin dokar DMA.
Rikicin META da Tarayyar Turaina karin haske kan damuwra d aake da ita ta daukar nauyin amfani da yanar gizo da tasirin hakan kan bayanan sirrin mutane.
Tallace-Tallace sun zama babbar hanyar samun kudaden shiga, suna habaka kamfanoni da dama, ciki har da manyan kamfanonin sadarwar yanar gizo, inda suke take hakkokin bayanan sirri.
A yanzu, tsarin biya ko amince na kawo sabbin matsaloli ciki har da na kasuwantar da sirrin masu amfani.
Hakan na janyo hatsarin rarrabuwar kai a fagen sadarwar yanar gizo inda boye bayanan sirri ya zama na wadanda za su iya biyan kudi kawai. Wannan kuma yanayi da ba ma son yanar gizo ta fada ciki.
Tarihin tallace-tallacen yanar gizo ga jama'a
Tallace-tallacen da aka nuna wa mutane a yanar gizo sun samu tare da ita kanta yanar gizon, ind aake amfani da dabaru wajen tattara bayanan masu amfani. Da farko dai ta ci barkatai ake yada tallace-tallacen yanar gizo.
Talla na farko ya fara bayyana ne a 994 a kan shafin yanar gizon wana mujalla, talla ne da ba ya motsi kuma ba ya nufar kowa.
Amma lamarin ya girmama ne bayan da shafukan bincike a yanar gizo suka kaddamar da smaun kudi idan aka dannan wani abu, inda ake yi talla duba ga mai amfani da yanar gizo, hakan ya sanya tallace-tallacen suka zama masu alaka da rukunan jama'a.
Bayan kaddamar da cookies ne aka samu dama sosai ta irin wannan talla da ke nufar wasu mutane. Hakan ya tabbata a tsakiyar 1990. Wasu kananan bayanai ne da aka tattara a kan shafin da mai amfani ke amfani da shi don rike bayanan mai amfanin.
Kafin kaddamar da cookies, a kowanne lokaci wani ya ziyarci yanar gizo, ba a san waye ba, kuma ba shi da alaka da kowa.
Cookies na bayar da dama ga shafin yanar gizo ya tuna da mai amfani idan ya dawo, ya sake nemo masa abinda ya danna a baya.
Masu tallace-tallace sai suka fara amfani da cookies wajen tallata hajarsu ga masu amfani ta hanyar daukar bayanansu ta shafukan yanar gizon.
A tsawon lokaci, sai tattara bayanan masu amfani da yanar gizo ya yi amfani da su sosai.
A yayin da shafukan sada zumunta suke ta habaka, suna dogara kan bayanai da halayen masu amfani wajen fitar da tallace-tallacensu.
Haka kuma, injinan da suke hasashe da nemo bayanan masu amfani da shafukan yanar gizo, sun zama injinan tattara bayanai na rukunnan mutane, suna kuma isar da tallace-tallace na musamman a ko yaushe a yainda suke ci gaba da mu'amala da jama'a.
Matsalar Tarayyar Turai
Tarayyar Turai na da matsaloli da dama game da tallace-tallacen da ke nufa wasu mutane.
Wadannan tallace-tallace na dogara ne kan muhimman bayanan masu amfani da ake tattarawa wanda hakan na iya keta alfarmar sirrin jama'a saboda ana bibiya da diban bayanansu ba tare da yardarsu ba.
Wadannan tallace-tallace na dogara ne kan muhimman bayanan masu amfani da ake tattarawa wanda hakan na iya keta alfarmar sirrin jama'a saboda ana bibiya da diban bayanansu ba tare da yardarsu ba.
Dokokin Kare Bayanan Masu Amfani (GDPR) a Tarayyar Turai sun saka wasu dokoki masu tsauri kan tattara bayaranai, adana da su da amfani da su.
GDPR ta tanadi dole masu amfani su amince kafin a yi amfani da bayanansu wajen nuna masu tallace-tallacen da suke nufar su.
Sai dai kuma, kamfanoni da dama na amfani da sharuddan amincewa masu rikitarwa ko wadanda ba a fahimta yadda ya kamata ba, wanda sau da yawa suke rikitar da masu amfani, ko su gaza fahimta yadda ya dace.
Mamayar da wasu 'yan kamfanoni suka yi wa tallace-tallacen yanar gizo irin su Meta, da ma Google, ya sanya suke da iko kan manyan bayanai, kuma suna dogara da su wajen habaka kasuwarsu a tsakanin masu amfani.
A yayin mayar da martani ga dokokin Tarayyar Turai, Meta ya kirkiri "Subcription for no ad" (Ku yi rajistar da ba a ganin talla) ind amasu amfani a Facebook da Instagram a kasashen Tarayyar Turai suke da zabi tsakanin; ko su biya kudi na wata guda don daina ganin tallace-tallace, ko su yi amfani da shi kyauta amma fa za su dinga ganin tallan d aya shafi bayanansu.
Sayar da bayanan sirri
Tare da tsarin biya ko amince, wadanda suke da kudin biya don kar su ga tallace-tallace za su iya yin hakan kuma su samu sirri, inda wadanda ba za su iya biya ba kuma za a dibi bayanansu a kuma turo musu da tallace-tallace.
Wannan na samar da matakai hawa-hawa da suke mayar da bayanan sirri su zama wasu kayan sayarwa, inda wanda ya bayar da kudinsa ba za a taba nasa ba.
Tare da wannan, tsarin na iya janyo rarrabuwar kai a fagen sadarwar yanar gizo, inda masu kudi a su dinga sayen tsari mai karfi, wadanda ba su da hali kuma, ya zamar musu dole su yi aiki da abinda suka tarar, musamman irin yadda za a dinga bibiyarsu da me suke yi. Wannan zai janyo rashin daidaito wajen amfani da yanar gizo.
Ana tsara tallace-tallacen da ke nufar mutane na zama wani makami na mallake wa da amfani da halayyarsu. tare da tsarin biya ko amince, matakin mallake bayanan jama'a ya dogara kan kokarin daidaikun mutane wajen iya biyan kudin.
Wannan na iya samun tasiri sosai a yanayin zamantakewa, musamman idan aka dinga nufar marasa galihu da tallace-tallacen yanar gizo, misali irin abinci marasa inganci.
Tasiri kan tallace-tallecen yanar gizon
Matakin Tarayyar Turai na iya yin tasiri kan masnaa'antar tallace-tallace a yanar gizo. idan aka aiwatar da shi, za a takaita kokarin masu gadi da kula da bayanai irin su Meta wajen amfani da bayanan jama'a don tura musu talla.
Duk da haka, masnaa'antar tallace-tallace ta nuna sabawa da dokokin. Kuma tana iya neman wasu hanyoyi sabbi na shirya tallansu a karkashin sabbin dokoki.
Daya daga ciki shi ne koma wa ga tsarin amfani da abinda mai aiki da yanar gizo ke nema, maimakon amfani da bayanansa.
Dadin dadawa, cigaban da aka samu na Kirkirarriyar basira da koyon daga injina na iya taimaka wa wajen inganta amfani da tallace-tallacen da ba sa nufar mutane sosai, ta hanyar nazari kan tsari da salo, ba tare da dogara kan bayanan mutum ba.
Ko ma dai menene, yana da wahala a iya hasashen ko wannan na iya kai wa ga manufar da ake son cimmawa, wadda za ta zama iri daya da ta amfani da manyan bayanan mutane wajen nuna musu talace-tallace a yanar gizo.