Daga Meried Bekele
Afirka na kan wata gaba mai muhimmanci. Tare da yawan mutane matasa nau'i daban-daban, dimbin albarkatun kasa, da yadda ta kulla alaka da duniya, nahiyar na da damar sake fasalin matsayinta a fagen juya tattalin arzikin duniya. Amma kuma yiwuwar samun damar ba zai isa ba.
Bambancin koma baya da samun cigaba ya ta'allaka kan wasu manyan turaku guda uku: manufa, aiwatarwa, da sana'a.
A littafina, 'Ethiopia Incorporated', na yi bayanin yadda wadannan sabbin tsare-tsare suka sauya fasalin tattalin arzikin Ethiopia d ayadda za a iya amfani da su a sauran kasashen Afirka.
Amma wannan ba tattaunawa ba ce kawai ta ba ki - Na shaida wadannan ka'idoji a lokacin da na ke samar da hanyoyin yanar gizo na 'IE Networks' a daya daga cikin kamfanonin sadarwar zamani na Ethiopia.
Kamfanin 'IE Networks' da aka samar a 2008, a yanzu na da ma'aikata kwararru 200, kuma ya hada hannu da manyan kamfanonin duniya da ake ayyuka a Ethiopia.
Rayuwata a matsayin mai sana'a ta sake jaddada amanna da na yi da makomar Afrka, za ta zama a hannun wadanda ke da hangen nesa sosai, za su aiwatar da manufofi ba tare da tsoro ba, kuma za su rungumi sabbin kere-kere da zamananci.
Hangen gaba da yau
Kasa - ko kasuwanci - ba tare da manufa da aka tanada ba, a dauki matakin magance rikici maimakon fasalta makomarsa. Niyyata ba wai kafa wata cibiyar Fasahar Sadarwa ba ce, sai dai samar da kamfanin da zao kawo sauyi a fagen sadarwar zamani a Ethiopia da ma wajen kasar.
Mafi yawan labaran masu dadi game da tattalin arzikin Afirka - ko a fannin samar da kayayyaki na Ethiopia, ko a sauyn fasahar sadarwa a Rwanda, ko a fannin sarrafa kudade a Nijeriya - sun fara ne da dabbaka manufa.
Dole ne shugabanni, na gwamnati da 'yan kasuwa, su bayyana manufofinsu karara don kawo cigaba ba wai na biyan bukatun kai ba.
CIke gibin da ke tsakanin tunani da gaskiyar al'amari
Manufa ba tare da aiwatarwa ba mafarki ne da tsakar rana. A mafi yawancin lokuta, Afirka na zama koma baya ne ba wai saboda rashin tsari da dabaru ba, sai saboda raunin aiwatar da manufofin.
A yayin fara ayyukan fasahar kere-kere da sadarwa, muna bukatar ajje wa a zukatanmu cewar babban kudiri da niyya kadai ba za su isa ba - muna bukatar samun kwararan ma'aikata, dokokin aiki, da magance kalubalen gudanar da ayyuka a kasuwar da ke habaka.
Ayyuka da dama ba s ayin nasara saboda sun ki bayar da muhimmanci ga aiwatar da manufofinsu.
Kasashen da suka ci gaba, irin su Mauritius ko Bostwanam sun yi aiki sosai don tabbatar da cewa hukumomi, tsare-tsare, da karfafa gwiwa da ke tattare da manufofinsu na dogon zango.
Aiwatarwa na bukatar dokoki, aiki da gaskiya, da kokarin daukar darasi daga matsalolin da aka samu.
Habaka kirkira da cigaba
Ginshiki na karshe shi ne sana'o'i - babban injin sauyin tattalin arziki.
A fadin Afirka, matasa masu kirkira na warware matsalolinsu da tasirin duniya.
Domin habakar sana'o'i, dole ne a samar da tsare-tsare da z asu taimaka wa ayyuka, tare da rage wahalhalun samun takardu d aizini, habaka hanyoyin samun jari, da samar da yanayin taimaka wa masu daukar ganganci don neman smaun nasara.
Gwamnatoci, masu zuba jari, da hukumomin ilimi gaba daya na da rawar taka wa wajen habaka al'adar da ke wa samar da kasuwanci kallon abu a kasa ta baiwa fifiko.
A lokacin da na fara kasuwancina, na san cewa kasuwar ba ta samun yadda take so, amma na kuma san cewa nasara na bukatar abubuwa sama da bayyana manufa - tana bukatar juriya, tunani mai kyau, da sabo.
Yau, nasararmu shaida ce da ke bayyana cewa masu sana'o'i a Afirka na iya gina manyan kamfanoni, har ma wajen kalubalantar muhallai.
Dole ne irin wannan ra'ayi ya zama ya kankama a nahiyar. Daya daga cikin kadarorin Afirka da ba ta amfana da su shu ne matasanta.
A matsakaicin shekaru na 19, yawan jamaa'ar nahiyar matasa wani jigon tattalin arziki ne da ke jiran a yi amfani da shi.
Kogin kaifin basira na Afirka ba kadarar nahiyar ba ce kawai - dama ce ta duniya baki daya.
Daga Injiniyoyin manhajoji a Kenya zuwa ga kirkirar kayayyakin sadarwar zamani a Ghana, matasan Afirka na bayyana iyawarsa ta gogayya a duniya.
Sai dai kuma, domin matasan Afirka su yi aiki a matsayin ma'aikata na duniya baki daya, zuba jari a fannin ilimi, kayan sadarwar zamani, da manufofin aiki daga nesa sun zama wajibi.
Duniya na fuskantar sauyi ga aikin da jama'a ke yi, kuma Afirka na da damar zama a tsakiya don samun wannan sauyi.
Tare da bayar da horo da haduwa waje guda, miliyoyin matasan Afirka na iya shiga fagen tattalin arzikin duniya - ba a matsayin masu saya kawai ba, sai a matsayin masu samar da kayayyaki da ayyuka.
Mafita ga labarin Ethiopia, kamar sauran Afirka, har yanzu ana rubuta yadda za a fita din. Kasar ta samu cigaba sosai a bangaren habakar tattalin arziki, amma kalubalen na nan.
Ta hanyar rungumar manufofi, aiwatar da su, da sana'o'i, Ethiopia - da ma Afirka baki daya - na iya nemo mafitar samar da cigaba mao dorewa.
Lokacin daukar mataki ya yi, makomar Afirka ba za ta dogara kan taimako daga kasashen waje ba, ta dogara ne ga karfin manufofinta, ladabin masu aiwatar da manufofin, da kaifin basirar masu sana'o'i.
Mafi muhimmanci, matasan nahiyar, ta hanyar amfani da karfinsu ne za su samar da cigaban - idan an ba su damarmakin da suka dace.
Marubuci: Meried Bekele, marubciya ce, mai sana'a kuma mai aiki kan hanyoyin sadarwar yanar gizo.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.