Ginin hedkwatar Ƙungiyar Haɗin Kan ƙasashen Afrika a Addis Ababa,/ Photo: Reuters Daga Mohamed Guleid       / Photo: Reuters

Daga Mohamed Guleid

Afirka, nahiyya mai ɗimbin arziƙi, amma tana fama da talauci da cututtuka da kuma tashin hankali. Duk da tarin damammaki da take da shi, Afrika na ci gaba da kasancewa a ƙangin rarrabuwar kai mai tarihi da kuma gwagwarmayar neman ƴancin kai daga wajen Afrika.

Amma wani kira da babbar murya ya karaɗe nahiyar - kiran da ke buƙatar sake fasalin rayuwarmu. Lokaci ya yi da za mu kare cibiyoyinmu don su samu damar zama daidai da kowa a faɗin duniya.

Ba za a ci gaba da kawar da kai a kan Ƙaruwar muryoyi da ke kira game da buƙatar a samar da wata tafiyar kishin Afrika mai ƙarfin gaske ba.

Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika (AU) tana da muhimmiyar rawa da za ta taka a wannan gwagwarmaya ta kishin Afrika. Amma fa, AU na fuskantar matsaloli wajen cim ma matsaya da haɗin kai tsakanin ƙasashe mambobinta saboda dalilai da yawa.

Da farko, abubuwan da mulkin mallaka ya gadar mata sannan kuma iyakokin ƙarya da aka shata sun haifar da mummunan rarrabuwar kai tsakanin ƙasashen, abin da ya haddasa muradun ƙasa mabanbanta, da banbancin al'adu da aƙidun siyasa. Waɗannan rarrabe- rarraben suna kawo tarnaƙi wajen cim ma matsaya ɗaya a kan muhimman batutuwa.

Har wa yau, banbance banbancen tattalin arziƙi da matakan ci-gaba mabanbanta tsakanin ƙasashe mambobi suna samar da buƙatu mabanbanta.

Ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi kan muhimmantar da yarjejeniyoyin kasuwanci da ƙawancen tattalin arziƙi da suka bambanta da na ƙasashen da ke fama da talauci da ƙarancin abubuwan more rayuwa.

Abubuwan da mulkin mallaka ya gadar sun haifar da munanan rarrabuwar tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen Afrika Photo: Getty

Rarrabuwar tattalin arziƙi

Muradun yanki da na siyasa da kuma gwagwarmayar neman iko a yankin sun taka muhimmiyar rawa. Wasu ƙasashen sun nemi yin mamaya ko samun ƙarfin-faɗa-a-ji a nahiyar, abin da ya haifar da gogayya a maimakon haɗin kai.

Saɓani na yawan faruwa, musamman game da iyakoki, da rabon arziƙin ƙasa da kuma aƙidar siyasa, ya kawo tasgaro ga cim ma matsaya ta gabaɗaya.

Yau, matakin da AU ke bi wajen cim ma matsaya, wanda ya ta'allaka sosai da tsarin diflomasiyya na masalaha, yana zama mai nawa kuma cunkusasshe.

Wannan zai iya haifar da tsaiko wajen ɗaukar mataki a kan lokaci da kuma cim ma yarjejeniya a kan muhimman batutuwa yayin da ƙasashe mambobi ke fafutikar kare muradunsu na ƙashin kansu.

Daga ƙarshe, katsalandan daga waje, har da shisshigi daga manyan ƙasashen duniya ko kuma tsoma baki daga ƙasashen waje, ka iya dagula lamurra, sauyawa ko yin tasiri kan matakan da za a ɗauka a cikin AU.

Idan aka gwama lamura da suka shafi tarihi, da tattalin arziƙi, da yanayi ƙasa da siyasa da bin tsari da kuma wasu abubuwa daga waje, AU na fuskantar lamari mai sarƙaƙiya, inda cim ma matsaya ta bai-ɗaya, a kan mahimman al'amurra ke ci gaba da zama mai cike da ƙalubale.

Ƙoƙarin samar da haɗin kai na buƙatar kawar da waɗannan ƙalubale masu fuskoki da dama don samar wa Afrika da ƙungiya mai ƙarfi kuma dunƙulalliya domin ci-gaban bai-ɗaya.

Kafa Cibiyar Nazarin Kishin Afrika da aka yi kwanan nan, a Jami'ar Lukenya ta ƙasar Kenya, wani muhimmin lamari ne.

Hadafin wannan cibiyar na ilmantarwa, da gudanar da bincike na ƙirƙira, da kuma yauƙaƙa musayen al'adu ya zama wata alƙibla ce ta haɗin kan ƙasashen Afrika.

Aiki tare tsakanin ƙasashen Afrika, musamman ta fuskar kudu maso kudu, har yanzu abu ne da ba a cika gani ba.

Zirga zirgar jiragen sama a cikin nahiyar ya ƙaranta sosai, abin da yake taƙaita cinikayya tsakanin ƙasashen yankin, wanda a halin yanzu yake da kaso 14%.

Wannan lamarin ya nuna irin harkokin tattalin arziƙin da ba a ci gajiyarsu ba da suke kwance a ƙasashen Afrika.

Babban Taron Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika na watan Fabrairu 2022. Photo: Reuters

Dunƙulalliyar Nahiyar Afrika

Hangen Farfesa Patrick Loch Otieno Lumumba na nahiyar Afirka mara shinge, misali ne na aƙidar kishin Afrika - nahiyar Afrikar da zirga zirga tsakanin ƙasashen Afrika ba ta samun tarnaƙi daga bambance bambance barkatai. Hange ne da aka assasa shi bisa alfaharin dunƙulewar nahiyarmu waje ɗaya.

Sai dai kuma, tabbatar da wannan hangen jan aiki ne. Ɗaruruwan shekaru na rabe raben mulkin mallaka ya bar Afrika da wani mummunan tabo.

Tafiyar ta kishin Afrika na fama da ɗawainiyar warkar da waɗannan tabban na tarihi, da farko ta hanyar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika da kuma haɗa hannu.

Tuƙewarta, wannan tafiyar na da hadafin kawar da duk wani shingen da ke kawo tarnaƙi ga kasuwanci da zirga zirga a nihiyarmu.

A bankaɗo harkokin tattalin arziƙi na Afrika, da ƙarfafa aiki tare da kuma kawar da shingen da ke kawo cikas ga Kasuwancin Afrika suna da muhimmanci. Wajibi ne Cibiyar Nazari Kan Kishin Afrika ta samar da dabarun da za su bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika.

Amma, bari mu fuskanci gaskiya. Nasarorin da muka samu kawo yanzu ba su yi ko kusa da yadda ya kamata mu kai ba.

Hukumar Tabbatar Da Kasuwanci Babu Shinge Ta Afrika (AfCFTA) da alama za ta yi tasiri sosai, ya rage wa ƙasashe mambobi su ƙara ƙaimi wajen haɗe dokoki, da da ƙara adadin kayayyakin aiki da kuma haɗe manufofi.

Ya kamata kafofi irin su Cibiyar Nazari Kishin Afrika su zarce da'irar ilimi. Kamata ya yi su samar da wani ƙawance da zai haɗe kan iyakoki da harsuna.

Musayen al'adu, da haɗin kai wajen samar da ilimi da kuma haɗin guiwa wajen bincike suna da muhimmanci wajen samar da fuska ɗaya tsakanin ƙasashen Afrika.

Bugu da ƙari, inganta sufuri da sadarwa yana da muhimmanci wajen bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika.

Inganta sufurin jiragen sama da na da motoci da kuma na jiragen ruwa ba zai taƙaita ga bunƙasa kasuwanci ba ne kaɗai, zai ƙarfafa musayen al'adu da tattaunawa tsakanin mutanenmu mabanbanta.

 Kyautata abubuwan more rayuwa a nahiyar zai tallafa wa kasuwanci sannan kuma ya ƙarfafa musayen al'adu. Photo: Reuters

Ya kamata Cibiyar Nazari Kishin Afrika ta zama wata kafar tattaunawa kan manyan batutuwan da ke kawo tarnaƙi ga ci-gaban Afrika.

Wajibi ne tattaunawa da ke mayar da hankali kan shugabanci, ci-gaba mai ɗorewa da kuma fahimtar zamantakewa da siyasa su zamo kan gaba a fafutikarmu ta samar da nahiyar Afirka haɗaɗɗiya, yalwatacciya kuma dunƙulalliya.

Rungumar fasahar zamani ya zama muhimmin abu wajen cika burin kishin Afrika. Ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Kishin Afrika a Kenya ya nuna muhimmin mataki a yunƙurinmu na samar da haɗin kai da aiki tare.

Amma, tafiyar da ke gaba na buƙatar jajircewa daga duk ƙasashen Afrika.

Lokaci ya yi da za a wuce saɓanin tun na tarihi, mu rungumi abubuwan da suka haɗa mu, sannan mu fuskanci samar da Afrika mai bunƙasa - nahiyar da take tsaye ƙem a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata, ci-gaba da jajircewa.

Marubucin, Mohamed Guleid marubuci ne kuma jami'in tsare-tsare na ƙasa na shirin NEDI, Shirin Raya Arewa Maso Arewaci da Gabashi.

Togaciya: Ra'ayoyi da marubucin ya bayyana ba dole su zo daidai da ra'ayi, fahimta da manufofin TRT Afrika ba.

TRT Afrika