An buga Littafin ''Things Fall Apart'' na Chinua Achebe a shekarar 1958. Hoto: Cibiyar Tunatarwa

Daga Chuma Nwokolo

Shekara 65 kenan da buga Littafin nan mai suna ‘Things Fall Apart.’

Shi ne littafi na farko da Chinua Achebe ya rubuta. Littafin ya kasance mafi shahara.

Wannan shi ne babban dalilin da ya sa na ba littafin lambar yabo na: matsayin tarihi. Labarin na almara da marubucin ya fitar ya shafi salon rayuwa da ke da alaka ga masu karatu daga kabilu dabam-dabam.

Littafin ‘Things Fall Apart’, mai harshen dabo, ya ja hankalin marubuta da manazarta a yau. Sannan wanda aka fi fassarawa da nazari a kai fiye da kowane littafin marubucin. Matsayinsa ba zai taba gushewa ba a tarihi.

Littafin ba wai kagaggun tatsuniyoyin kauyen Umuofia ba ne, labari ne da aka fitar wanda ke tafiya da tarihin yadda rayuwa take cikin littattafan tarihi.

Abubuwan da muka gada a matsayinmu na ‘yan adam sun yi nuni da cewa akwai dangantaka a tsakanin duk wani tarihi na mutane da suka shude.

A kwanan nan, na yi wani balagoru tsakanin kasashen Laberiya da Saliyo. A gefen iyakar Laberiyar ruwa ne, idan ka tsallaka babban Kogin Mano za ka ganka a Jendema.

Ranar Lahadi ne, da kyar ake samun kayan masarufi da za a iya girki, domin kauyen cike yake da shige da ficen manyan motoci da ke diban mutane.

Ana iya cewa duk wanda aka gani a wajen ya zo ne don ya samu damar a tsallaka da shi zuwa iyakar garuruwan wajen.

Akwai daruruwan kauyuka kamar Jendema a fadin Afirka, kauyukan iyakoki da suka zama wurin da mutane ke bi don tsallakawa zuwa wasu wurare.

Wurin wasan kwallo

Na dauki keke zuwa cikin Saliyo da ke da dan nisan kilomita zuwa kauyen Gohn, nan na tarar da makarantu a gefen babban titin da ya raba hanyar biyu. A daya daga cikin makarantun yara ne ke wasan kwallo a ciki.

Na shiga kauyen. Mafi yawancin gidajen na kasa ne. Gari ne da aka gina shi da asalin kasa. Gine-ginen ne da kamar sun bullo daga cikin kasa da kansu, kuma idan ka yi duba da tsanaki, za ka iya hangen Okonkwo cikin bacin rai yana tsallaka hanya don cacar baki da Nwoye.

Ana girki a dukkan bangarorin hanyar. Yara matasa uku da ke kwallo suka wuce ta gabana, na tambaye su ko za ku yi wasa a filin makaranta ne? Suka amsa da e, inda na yi alkawarin zuwa kallon su.

Mutane na ta kallo na a yayin da nake tafiya. Watakila wannan hanyar jama'a ce, amma ba ita ce babbar hanyar zuwa Laberiya ba. Babu wanda ke bi ta wannan hanya ba tare da gudanar da kasuwanci a Umuofia ba.

Matafiyi mai zumudi

Ana haka ne wani ya yi ta maza tare da tambaya ta me na ke so. Labari daga wajenka, na fada masa haka.

Wani matashi ne nake magana da shi da bai wuce shekara 30 ba, dan asalin kauyen da ya kawo ziyara daga kauye dake kusa da wannan.

Mun tambayi juna sunayenmu tare da yin musabaha, amma ya furta cewa bai san komai game da tarihi ba, haka ma babu daya daga cikin abokansa da suke zaune suke hira da ya sani. Sai ya kai ni wajen shugabansu.

Shugaban nasu dattijo ne, amma kuma yana da karfin kwakwalwa da na jiki, kuma yana kan kujerar lilo da ke rangaji a jikin turakun gaban gidan.

Yana kisingide abinsa tare da nishadantuwa kamar yadda Obierika ke nishadantar da jama'arsa.

A kewayensa akwai 'yan fada. Bai iya Turanci ko Krio ba, kuma wanda ya kawo ni wajen sa ne yake mana tafinta, inda yake bayanin ni Farfesa ne a jami'a mai nisa wanda ya zo don bincike game da tarihi da al'adun jama'ar Gohn.

Ban iya yaren ba, amma 'yan kalmomin Turanci da ake furtawa sun bayar da ma'ana, kuma na dinga gyara masa wasu shaci fadi da abun da yake na gaskiya: Ni matafiyi ne daga Asaba, na zo wucewa ta kauyensa, kuma nake son sanin tarihin kauyen.

Tasirin mulkin mallaka?

Shugaban na da raha sosai, amma zargin masu wucewa ta wajen ya yi nisa a kauyen Mende. Dansa na son ganin karin bayani sosai, kuma jama'ar da suka taru na muhawara game da MDD dangane da hatsarin tattauna tarihi da tsohon da kansa duk ya yi furfura.

Watakila, wannan ne martanin da suke mayarwa ga yadda suka sha dauri da igiyoyi da sarka a gwagwarmayar 'yan mulkin mallakar da suka zo Afirka shekaru daruruwa da suka shude.

Irin igiyar da Okonkwo ya rataye kansa da ita. Ko kuma wataklila yadda wasu kungiyoyi masu zaman kansu da ke zuwa da mummunar munufa suna bincike ne ya sanya su hakan.

Ko ma dai mene ne, shugaban ya ci gaba da lilawa a kan gadon mulkinsa, ya yarda da cewa babu wanda ya san tarhin kauyensu kamar sa. Babu, amma kuma ba zai bayar da tarihin ba.

Wannan ne ibtila'in da littafin 'Things Fall Apart' yake yaka a shafukansa; tsofaffin dakunan karatu da suke kin bayar da bayanai na mutuwa da tarihinsu a bakunansu ba tare da sun fadawa kowa ba.

A lokacin da nake tafiya, na hori mai mini tafinta, da ya yi kokarin samun tarihin wannan kauye nasu daga wajen shugaban.

Kyakkyawa tsarin gari da makotaka

Har ga dakunan hutawa ma, abubuwan da muke da su ma na ta rushewa.

Na fita daga Gohn, na kaunaci yadda kujerun itaciyar bamboo suka zama a gaban gidajen kauyen.

Wannan na nuni da kyawun tsarin gini da sarrafa kasa da safayo: ta yaya wani zai kulla gaba da makota da ya zama dole kuna samun baki iri daya, abinci da kuma yin gulma tare?

A babbar hanya, yara na ci gaba da buga kwallonsu. Yadda ake shewa ne ya ja hankalina: watakila ni wani mai leken asiri ne na boye da gasar Premier?

Yadda suke shewa da amo a Mende ya dimauta ni kamar wata waka. Abu ne mai muhimmanci yadda ba sai mun san me ake fada a kida ba za mu taka rawa.

Na kalli wasan, amma kuma nauyin rashin nasarar samun tarihi na damu na a yau. Na koma dakina a Jendema, ina mamakin idan wani zamani mai nisa a Mende za su iya sanin tarihinsu daga littafin 'Things Fall Apart'.

Marubucin wannan makala Chuma Nwokolo, dan Nijeriya ne lauya ne kuma marubuci da ke Legas.

Inkari: Ra'ayin da marubucin ya fada ba zai zama lallai ya zama daidai da ra'ayin TRT Afirka ba.

TRT Afrika