Kyautar Nobel: Ya kamata  marubutan Afirka da yawa su lashe gasar

Kyautar Nobel: Ya kamata  marubutan Afirka da yawa su lashe gasar

Tun bayan fara bayar da kyautar, 'yan Afirka shida ne suka samu kyautar Nobel a fannin Adabi.
Kyautar Nobel. / Photo: AP

Daga Toby Green

Wannan kyauta ita ce ta fi yawan kudi, da dadewa, kuma kamar yadda mutane suke fada, ita ce ta fi daraja a duniyar adabi.

Kyautar Nobel tana zuwa da makudan kudi da suka kai miliyan 11 na kudin Krone na kasar Sweden, wanda ya kai dalar Amurka dubu $993,000.

Ranar 5 ga watan Oktoba, an ayyana marubuci dan kasar Norway Jon Foss a matsayin wanda ya lashe Nobel na Adabi, saboda "sabon salon rubutun wasan kwaikwayo da zube wanda ke fito da abuwan da ba a iya fadar su”.

An dade ana ambaton sunan Fosse a matsayin dan takarar samun kyautar tsawon shekaru, don haka abin bai ba da mamaki ba yanzu. Ya samu tarin sakonnin imel, kuma ya ce zai samu lokaci ya amsa dukkansu.

Sai dai duk da haka, kyautar har yanzu tana tuna wa duniya cewa akwai 'yan Afirka da dama da ba a ba su kyautar ba mai matukar daraja.

Jon Fosse ne ya ci Kyautar Nobel Prize a Adabi ta 2023. / Hoto: Reuters

Tun bayan fara bayar da kyautar, 'yan Afirka shida ne suka samu Nobel na Adabi.

Amma kuma Wole Soyinka (dan Nijeriya; 1986) shi ne kadai bakar fata da aka bai wa kyautar. Wanda ya ci kyautar a kwanakin baya, Abdulrazak Gurnah dan Tanzania, mahaifansa 'yan Yemen ne.

Kafin nan, JM Coetzee (dan Afirka ta Kudu), da Nadine Gordimer ('yar Afirka ta Kudu), da Doris Lessing (dan Zimbabwe) duka fararen fata ne 'yan Afirka da suka ci kyautar. Naguib Mahfouz daga Masar, shi ma ya ci kyautar a 1988.

Masu karance-karancen adabin Afirka ba sai sun yi dogon tunani ba kafin su gano tarin marubutan Afirka da aka yi watsi da su a batun ba da kyautar a shekarun baya, da ma na yanzu.

A lokacin samun 'yancin kai na shekarun 1960, da 1970 da 1980, sunaye uku sun yi fice a matsayin 'yan takarar samun kyautar Nobel: Chinua Achebe na Nijeriya, Léopold Sédar Senghor na Senegal, da Aimé Césaire (na tsibirin Martinique).

Achebe ya yi suna a matsayin "uba ga adabi Afirka”, saboda shahararren littafin da ya rubuta "Things Fall Apart", wanda aka wallafa a 1958.

Littafin ya zamo littafin adabin Afirka da aka fi karantawa, saboda ya nuna yadda mulkin mallaka ya haifar da rusa tsarin rayuwar al'ummar Igbo ta Nijeriya.

Labari ne kan Okonkwo, wanda aka kashe saboda kokarin kare al'adun Igbo, kuma an kalli labarin a matsayin manuniya kan yadda mulkin mallaka ya lahanta Afirka.

An wallafa littafin Chinua Achebe da ya fi shahara a shekarar 1958. / Hoto: Reuters

A labarin, yayin da aka binne Okonkwo, kwamishinan gunduma na Birtaniya ya yi tunanin yadda wannan batu zai iya zama babi ko “akalla wani sakin-layi” a littafinsa mai suna "Kwantar da Wutar Kabilun Gargajiyar Kurmin Neja".

Bayan wannan littafi – wanda daya ne cikin littafai 100 da suka fi kasuwa a tarihi, Achebe ya wallafa littafai masu yawa, har da "No Longer at Ease" da "Arrow of God". Amma duk da haka, ba a ba shi kyautar Nobel ba.

Wole Soyinka ya ci kyautar Nobel Prize a 1986. / Hoto: AP

Da yawan mutane sun ce ya samu ne saboda makalar da ya rubuta kan littafin "Heart of Darkness" na Joseph Conrad, inda ya yanke hukuncin cewa shahararren littafin ya nuna wariyar launin fata.

Shi kuwa Senghor ya zamo shugaban kasa na farko a Senegal, bayan samun 'yancin-kai. Amma kafin nan, a shekarun 1940s da na 1950s, shuhurarsa ta kai matakin ta wanda ya kirkiri rajin kishin bakar fata, tare da Aimé Césaire.

Kishin bakar fata yana da manufar gina tananin farkar da Bakar fata a fadin Afirka da 'yan Afirka mazauna waje, don su yaki mummunan tasirin 'yan mulkin mallaka daga Turai.

Kishin bakar fata ya samu karbuwa tare da tunanin kishin Afirkanci, kuma yana da tasiri kan rubuce-rubucen yaki da mulkin mallaka na Frantz Fanon.

Sai dai kuma, a shekarun 1960s, wasu Bakaken marubuta sun soki tsarin 'yan kishi da cewa suna nuna sassauci da yawa.

Duk da alfanun siyasa da na adabi kan wake-wake da rubuce-rubucen Césaire da Senghor, ba dayansu da aka ba wa kyautar Nobel, ko aka taba sanya wa cikin manyan 'yan takara.

A shekarun baya-bayan nan, neman yin adalcin ga marubutan Afirka ya mayar da hankali kan sabbin 'yan takara su biyu: Ngũgĩ wa Thiong’o (na Kenya) da Maryse Condé (na tsibirin Guadeloupe).

An sha tunanin Thiong’o zai lashe kyautar a shekarun 2000 da na 2010, duk da ba a ga hakan ba a shekarun baya-bayan nan, saboda ganin shi ma zai kare irin yadda Achebe ya kare.

Ngũgĩ wa Thiong’o na Kenya daya daga cikin marubutan Afirka wanda wasu suke cewa ya cancanci Kyautar Nobel Prize. / Hoto: Reuters

Marubucin ya wallafa littafai masu kayatarwa game da farkon shekarun samun 'yanci, da suka hada da "A Grain of Wheat". Thiong’o ya zama mutum mafi muhimmanci a rubutun adabi kan fafutukar Afirka kan mulkin mallaka cikin shekaru 40 na baya, tun buga littafinsa na "Decolonizing the Mind".

CIkin shekarun baya-bayan nan, an yi ta tattaunawa kan Maryse Condé game da kyautar. Marubucin dan tsibirin Guadeloupe ya karantar a Guinea, da Ghana da Senegal a shekarun 'yancin-kai (1960-72), kafin ya fara karantar da adabi a manyan jami'o'i a Amurka.

Condé shi ne mawallafin da ya rubuta kagaggen labarin tarihi kan mulkin mallaka a Afirka mai sun "Ségou", da kuma littafin da ya biyo baya, "The Children of Ségou".

Maryse Condé. / Hoto: Reuters

Kamar Farfesa Thiong’o a shekarun 2000s da farkon shekarun 2010s, an yi ta ambaton sunan Maryse Condé dangane da kyautar Nobel cikin 'yan shekarun da suka gabata, amma ba abin da ya biyo baya.

Tun bayan shekaru 65 da fara harkar rubutun adabin zamani tun lokacin da Chinua Achebe ya wallafa littafin Things Fall Apart, alkaluman a fili suke kuma ba su da dadi. 'Yan Afirka su shida ne suka ci kyautar Nobel, inda mutum daya ne kawai baki.

Amma abin da yake zahiri shi ne, kamar yadda masoyan Thiong'o suka fassara batun, ba wai saboda Ngũgĩ (ko Condé) suna bukatar kyautar Nobel ba, amma a zahiri Nobel ne ke bukatar su.

Toby Green farfesa ne a nazarin tarihin Afirka a jami'ar King’s College da ke London.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar ra'ayi, mahanga, ko tsarin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika