Daga Bonisile Makhubu
Da a ce dukkan kasashe za su tsara dokokin da sa za su kare mutanensu daga cutarwar zukar taba sigari, da mun daina rasa sama da mutum miliyan takwas duk shekara.
Daga cikin wadanda suke mutuwar, miliyan 1.3 ba mashaya sigarin ba ne, amma hayakin ke kai wa gare su, kamar yadda WHO ta bayyana.
Samar da wasu hanyoyin rage cutarwar, ta fi kyau a kan tsara dokokin haramta shan sigarin baki daya, sannan ta fi a kan kawai a rika wayar da kan mutane a kan daina ta'ammali da ita, sannan ita ce hanya mafi kyawu domin rage yawaitar mace-mace masu alaka da shan taba sigari.
A cikin taba sigari akwai kusan sinadarai guda 7,000, wadanda suke jawo cututtuka da daban-daban, sannan daga ciki akwai guda 69 da ke jawo cututtuka masu alaka da kansa.
A Afrika, kasashe kadan ne kawai suka runguma tare da kula da wasu hanyoyin ta'ammali da sinadarin nicotine din bayan zukarsa ta hayaki.
Wasu kasashe irin su Eswatini ba su ce komai ba, ko kuma akalla a ce ba su nuna damuwa da matsalolin da zugar taba sigarin je jawowa ba.
Tsarin daina sha baki daya
Abin da suke yi a lokuta da dama shi ne shawartar masu sha din da su daina. Amma me zai faru idan ba su daina ba? Ko kuma yaya batun wadanda hayakin ke cutarwa da ba mashayanta ba?
Kasar Eswatini da wasu kasashen guda 42 na Afrika sun shiga yarjejeniyar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kula da ta'ammali da sinadarin nicotine wato Framework Convention on Tobacco Control (FCTC), wanda ke kula da ta'ammali da taba sigari, da bayar da shawara ga wadanda suke da sha'awar daina ta'ammali da ita, da sanya hotunan gargadi a kwalayen sigari da kuma hana tallarta. Amma duk da haka, ba ta wani sauya zane ba.
Bari mu yi la'akari da kasar Afrika ta Kudu da wasu kasashen na Afrika da tuni suka fara amfani da tsarin rage cutarwar taba sigari wato Tobacco Harm Reduction (THR).
Afirka ta Kudu ta amince da amfani da sigari mai amfani da lantarki wato e-cigarretes a a hukumance.
Ita ma Kenya ta bi sahu wajen tsara yadda za ta cutarwar tabar, sannan ta fara yunkurin assasa dokar shan tabar e-cigarettes a hukumance.
Wadannan hanyoyin za kuma su nuna nuna cewa gwamnatocin kasashen Afrika sun damu matuka da inganta lafiyar mutanensu da kare su daga illar hayakin taba sigari.
An kalubalanci gwamnatocin Afrika su tsara hanyoyin rage cutarwar hayakin sigarin, sannan a gefe guda kuma su kula da lafiyar al'umma.
A lokacin da ake gudanar da taron rage cutarwar hayakin taba sigari a Kenya, mai taken kara amon sautin rage cutarwar hayakin taba sigari wato 'Amplifying the voice of Harm Reduction Advocacy Across Africa', Shugaban Kungiyar Likitocin Afrika, Dokga Kgosi Letlape ya yi bayanin alfanun samar da hanyoyin rage cutarwar hayakin taba sigari.
Amfani da na'urar vaping
Wannan hanyar ta fi kyau a kan tsara dokokin haramta shan sigarin baki daya, sannan ta fi a kan kawai a rika wayar da kan mutane a kan daina ta'ammali da ita," in ji shi.
Samun hanyoyin shan tabar bayan zukarta da ake yi irin su vaping da e-cigarette suna rage illoli da cutarwarta, a daidai lokacin da miloyoyin mashayan suka kasa dainawa.
Wadannan hanyoyin ba wai ba su da illa ba ne baki daya, sai dai rahotanni sun nuna cewa suna da sauki idan aka kwatanta da illolin zukar taba sigari inda babbar matsalar ita ce ta hayakin.
Hukumar Kula da Cututtuka masu Yaduwa CDC ta ce e-cigarettes ba su kai cutarwar zukar hayakin taba sigari ba ga manya wadanda ba sa dauke da juna biyu ba.
Sai dai suna da illa sosai ga masu juna biyu, yara da matasa wadanda ba sa shan sigari.
Kasar Eswatini tana cikin kasashen da ba su yi wani abin a-zo-gani-ba a game da rage cutarwar shan taba sigari duk da cewa tana rasa mutum 600 duk shekara a kan cututtuka masu alaka da taba sigari.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, "Kusan kashi 70 na wadannan mace-macen, mutane ne masu shekaru kasa da 70."
Wadanda ba sa shan sigari
Kusan rubu'in wadanda suka rasun ba mashaya taba sigari ba ne. Mutane ne da suke shakar hayakin tabar, inda mata da kananan yara suka fi yawa.
Daga cikin manyan illolin da zukar taba sigari zai haifar a nan gaba shi akwai talauci da rashin lafiya da rashin walwala.
A shekarar 2021, shirin Majalisar Dinkin Duniya na United Nations Development Program (UNDP) ya hada hannu da gwamnatin kasar Eswatini domin tabbatar da matasa manyan gobe ba su zama mashaya taba sigari ba, da kuma rage rashin lafiya da talaucin da shan sigari ke haifarwa.
UNDP ta gabatar da wani rahoto ke nuna yadda ta'ammali da taba sigari ke kawo tsaiko ga kasar Eswatini wajen habaka bangaren kiwon lafiya da habaka tattalin arzikinta, wanda hakan ke hana kasar cigaba.
An kalubalanci musamman masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya, su dabbaka hanyar rage cutarwar da sigarin ke haifarwa a matsayin hanya babba ta wayar da kan mutane a nahiyar.
Hanyar kiwon lafiya
Masana a bangaren kiwon lafiya da suke kira da a bi hanyoyin rage cutarwar sigari, sun ce hanyoyi ne da take tafiya tare da kokarin inganta lafiyar al'umma ta hanyar rage cutarwa, da wayar da kan al'umma a kan muhimmancin lafiya da kuma karfafa gwiwar masu ta'ammali da kwayoyi da iyalansu domin su rayuwa cikin koshin lafiya.
Akwai cin rai ganin yadda kasashen duniya ke ta kokarin nemo hanyoyin rage cutarwar wajen magance matsaloli da dama, musamman a bangaren ta'ammali da miyagun kwayoyi da sauran halaye mau masu hatsari.
Daga cikin wadannan hanyoyin akwai shirin sauya allura wato Needle Exchange Programmes, da shirin kula da allurori wato supervised injection sites, da PrEP (Pre-Exposure Prophylaxis), da Nicotine Replacement Therapy (NRT), da amfani da tabar Vaping ko tabar E-Cigarettes, da kuma sanya ido a shan magunguna.
Kasashen Afrika za su iya aro wasu daga cikin wadannan hanyoyin, wadanda ke bin mutane har inda suke da kuma yi musu yadda suke so sannan za su iya bude wata hanyoyin kula da kiwon lafiya da walwalar jama'a, ciki har da riga-kafi da jinya da waraka.
Akwai bukatar masu ruwa da tsaki su kasance suna da masaniya sosai a kan cigaban zamani na kimiya, sauye-sauyen da ake samu da kuma hanyoyin da za a bi wajen samar da duniyar da ba sa shan taba sigari a baki daya.
Marubucin, Bonisile Makhubu dan jarida ne da ke zaune a Eswatini.
Togaciya: Ba dole ra'ayin marubucin ya zo daidai da ra'ayi ko ka'idar aikin jarida na TRT Afrika.