Kungiyar HCI ce kungiyar tallafi ta Musulmi ta kasa da kasa mafi dadewa a Canada.

Daga Mahmuda Khan

A Afirka da Asia, kauyuka da dama suna fama da karancin ruwa mai kyau, wanda hakan ba wai yana hana su abubuwan yau da kullum ba, amma yana tasiri kan kiwon lafiya da da karin yiwuwar kamuwa da cututtuka da hana su samun damarmaki da ilimi da rayuwar yau da kullum.

Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana, akalla mutum biliyan biyu a fadin duniya ke shan ruwan da bayan gida ya gurbata.

Irin wadannan al’ummomi da aka ware na fuskantar wasu irin matsaloli da suka shafi tura ‘ya’yansu ko kuma matansa dauke da robobi domin tafiyar da ba ta kiyastuwa don debo ruwa, akasari tafiyar mil da dama.

Irin wadannan tafiye-tafiye masu nisa kan jefa mata cikin barazana daban-daban da suka hada da garkuwa da su inda yara kuma kan fuskanci matsaloli da suka hada da karancin ruwan jiki da kuma gamuwa da mugayen namun daji kamar su kada.

Matsalar karancin ruwa mai tsafta ta yi kamari, inda matsalar ke bukatar daukin gaggawa ganin cewa mutum miliyan 771 suke fama da karancin ruwan.

Wata kididdiga mai tayar da hankali da UNICEF ta yi ta nuna cewa zuwa 2025, kusan rabin jama’ar duniya za su samu kansu a yankunan da suke fama da matsalar karancin ruwa.

Samun kyakkyawan fata

Tsawon shekaru, kungiyar bayar da agaji ta Canadian relief charity Human Concern International (HCI) da wasu kungiyoyi na ta yin wannan kokari domin samar da rijiyoyi da kuma kula da su a fadin duniya, inda suke inganta rayuwar jama’a.

Kaddamar da rijiya a irin wadannan yankuna wani biki ne na musamman, inda ake murna kan wani muhimmin sauyi a rayuwa. Irin wadannan rijiyoyi na taimakawa matuka inda suke samar da ruwa ga gidaje sama da dubu biyu.

Sai dai samar da ruwa mai tsafta ya wuce batun haka rami domin yin rijiya. Akwai bukatar nazarin girman al’umma da adadin ruwan da suke bukata da kuma yadda za a dore.

Akwai shirye-shirye na horaswa da ilmantarwa ga mazauna yankuna, inda ake ilmantar da su kan dabarun yadda za su kula da fasahar amfani da ruwa.

Ta hanyar horas da jama’ar gari, suna zama masu kokarin tattali da kuma alkinta rijiyoyin da ake yi musu. Da zarar an kammala, ana bayar da kwangila ga wasu kungiyoyi wadanda za su tabbatar da kula da samun ruwa mai tsafta ga kauyuka.

A wasu lokutan, rijiyoyin da ake ginawa da fasaha kamar rijiyoyin burtsatse suna samar da ruwa mai tsafta a lokutan da ake wahalar ruwa ko kuma fari.

A wasu wuraren, saka na’urar cire gishirin ruwa mai amfani da sola kan zama wani sauyi ga wuraren da suke da ruwan gishiri.

Amfani da taurarin fina-finai

Domin magance matsalar karancin ruwa, kungiyar HCI ta kulla yarjejeniyar da Engin Altan Düzyatan, wanda fitaccen dan wasan kwaikwayon Turkiyya ne da ya shahara kuma mai rajin kare muhalli wanda ya yi suna a fim din nan mai dogon zango na TRT mai suna Diriliş: Ertugrul.

Altan ya yi amfani da tasirinsa wurin kawo sauyi da kuma wayar da kai kan matsalolin muhalli.

A 2019, Altan ya kasance daraktan wani fim mai suna “Be Witness” domin karin haske kan yadda al’ummomi marasa gata ke fama da matsalolin ruwa a Turkiyya da kuma Afirka.

Kungiyar HCI da Altan sun kaddamar da wani shiri na musamman domin ganin cewa sun yi yaki da karancin ruwa.

Hadin gwiwar HCI da Altan, ta yi tasiri matuka ga masu kallonsa a Arewacin Amurka, inda aka samu halartar dubban mutane a wasu tarukan nishadi da aka gudanar a muhimman birane a fadin Canada da Amurka.

Ta hanyar wadannan taruka masu tasiri, Altan da HCI sun samu goyon baya inda suka jawo hankalin mutane daga bangarori da dama da hada kansu domin samun daidaito a bangaren samar da ruwa.

Aiki mai daraja

An samu ci gaba matuka inda aka yi nasarar tara kudin da suka haura dala miliyan daya domin samar da ruwa a yankunan Asia da Afirka.

Akwai iyalai da dama wadanda suka bayar da gudunmawarsu ga wannan aiki, ko dai a matsayin wata sadaka ga nasu da suka rasu ko kuma a matsayin wata shaida ga darajar sunan danginsu.

A Musulunci, samar da ruwa ana daukarsa a matsayin Sadaqatul Jariya.

Tasirin irin wannan gudunmawar na ci gaba da tafiya sakamakon dubban mutane suna ci gaba da amfana a kullum daga ruwan da ake samu daga wadannan rijiyoyi.

Ta hanyar yin wannan aikin mai daraja, tasirin wanda ya bayar da gudunmawa na nan har abada, wanda hakan zai yi sanadin sauyawa da kuma daga rayuwar mutane da dama tsawon shekaru.

Ta hanyar gina rijiyoyi, da saka sabbin fasahoji da kuma kara inganta cudanya da al’umma, HCI na tallafa wa al’ummomi domin samun dorewa a rayuwa.

Amma masu ba da gudummawa su ne masu samar da ci gaba mai ɗorewa, suna haifar da sauyi da inganta rayuwar mutane marasa adadi.

Marubucin, Mahmuda Khan, babban darakta ne a kungiyar Human Concern International (HCI), wadda ita ce kungiyar tallafi ta Musulmi ta kasa da kasa mafi dadewa a Canada. Mahmuda na da digiri a bangaren tsimi da tanadi kuma ya shafe sama da shekara goma yana aiki a kungiyar.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta gabatar ba sa wakiltar ra'ayoyi da manufofin TRT Afrika.

TRT World