Daga Todd Belt
A lokacin da mutum ya yi duba ga bambancin da ke tsakanin yadda kafafan watsa labarai a Amurka ke bayar da rahotanni, cikin sauki za a fahimci yadda Amurkawa ke aminta da wani batu ko da kuwa babu wasu manyan dalilai.
Kafafen watsa labarai mallakin masu ra'ayin rikau sun cika da zargi da yada jita-jita, kamar bayyana cewar 'yan jam'iyyar Democrats sun yi magudi a zaben 2020 kuma 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba na aikata laifuka sosai.
Ta yaya batun ya kai haka, kuma shin wannan yanayi na kafafan watsa labarai mallaki masu ra'ayin rikay ya yi tasiri kan zaben shugaban kasar Amurka na 2024?
Kafin shekarun 1980, mafi yawan Amurkawa na samun labarai daga manyan tashosh uku da ake kira "Big 3"; ABC, CBS da NBC. Babu wani babban bambanci tsakanin dukka ukun wajen kauce wa bangaranci, kuma dukkan su suna aiki da ka'idojin aikin jarida da manufar rike kambin nagarta.
Amma sai wasu abubuwa uku suka faru, wadanda suka kai mu ga halin nuna bangaranci a fagen sadarwa.
A shekarun 1980, manyan tashoshi uku sun dauki matakin dakatar da daukar nauyin shirye-shiryensu na labarai da kudaden da suke samu daga shirye-shiryen nishadantarwa, wanda ke nufin labaran ma sai sun kawo riba domin ci gaba da wanzuwa.
A aikace, hakan na nufin cewa labarai za su sauya salo zuwa na nisashadantarwa, aka koma ganin salon kawo rahotannin labarai da bai damu da bin diddigin batutuwa da manufofi ba.
Abu na biyu kuma shi ne tashoshin tauraron dan adam da ke watsa shirye-shirye tsawon awanni 24, wanda ya sake ta'azzara wannan al'amari inda tashoshi suke rike masu kallon su tsawon dare da rana.
Abu na uku kuma shi ne mutuwar Akidar Adalci (wanda ke bukatar kawo ra'ayoyi mabambanta wajen batutuwan siyasa) a karshen 1980 wanda ya kawo ganin labaran siyasa da ba su da daidito tsakanin bangarori.
Tasowar tashar Fox News
Wannan cigaba ya jayo daukakar tashar Fox news da sauran tashoshin masu ra'ayin rikau, wadanda suka ci gaba da wanzuwa da yaduwa kamar yadda muke gani a yau.
A shekarun 1990, mamallakin babban mamallakin kafafan watsa labarai na kasa da kasa Rupert Murdoch ya dauki mai baiwa jam'iyyar Republican shawara kan sadarwa Rober Ailes don kafa tauraron dan adam na Fox News. Fox sun gano za su iya nishadantar da masu kallo ta hanyar amfani da kawo tsoro da bacin rai, wanda ya fi aiki a kan tsofaffi da suka damu kan sauyawar duniya.
Fox sun rungumi taken "adalci da gaskiya" amma ra'ayoyin da take yada wa na masu tsaurin ra'ayi ne. Tsawon lokaci, Fox ta ci gaba da zama masu ra'ayin rikau, kuma ana bayyana ta a matsayin mai magana da yawun Republican.
Matsawa daga nuna bangaranci zuwa yada karya ya zo daidai da lokacin da Trump ya karbi mulki a karkashin Republican a 2016.
A lokacin shugabancin Trump, mai ba shi shawara Kelllyanne Conway ya siffanta gwamnatin da cewa tana samun 'nata bayanan na gaskiya" - wanda Fox ke kara rurutawa.
A yayinda Trump ke hawa mulki a karkashin Republican, sai aka dinga samun yawaitar kafafan watsa labarai. Binciken da Yochai Benkler ya yi tare da abokansa ya bayyana yadda shafin yanar gizo na Breibert ya zama babbar matattarar yada labarai a tsakanin kafofin watsa labarai na masu ra'ayin rikau a lokacin yakin neman zabe a 2016.
Zaben 2024
Wadannan kafafan sadarwa sun fara sosai, daga na rubutu kamar The Epoch Times, zuwa shafukan yanar gizo da tashoshin sautin magana. Ba tare da wani tace wa ba, wadannan cibiyoyi sun fara tafiya a karkashin abinda masu suka ke kira da hadin baki da sirri.
Zaben 2024 na da muhimmanci ga siyasar Amurka da ko za a sake rungumar Trump ko za gama watsi da shi a siyasar Amurka.
Har ta kai sai da aka tirsasa wa Fox News biyan kudin da aka kai ta kara har dla miliyan 787 saboda yada karya game da injinan da zabe da Dominion Voting Machine suka samar, kan batun sauya kuri'u a lokacin zaben 2020 (suna goyon bayan ikirarin Trump na "magudi").
Zaben 2024 na da muhimmanci ga siyasar Amurka da ko za a sake rungumar Trump ko za gama watsi da shi a siyasar Amurka. Dukkan bangarorin biyu sun ji cewa sakamakon zaben na da muhimmanci ga akidunsu na kare dimokuradiyya.
A lokacin da Trump ya bayyana cewa 'yan gudun hijira daga Haiti da ke Springfield na "cin maguna da karnuka", ba iya maimaita hakan kafafan watsa labarai na masu ra'ayin rikau suka dinga yi ba, sun yi kokarin sahihantar da ikirarin. Haka ma masu jefa kuri'a da ke bibiyar irin wadannan kafafen watsa labarai suka yi a zaben 2024?
Muna da wasu alkaluma da ke nuna yiwuwar afkuwar hakan.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da GW Politics suka gudanar, wadda n a abokaina muka jagoranta a Jami'ar George Washington, ta bayar da wani karin haske game da wasu 'yan siyasa manya da yadda tunanin mutane game da su yake da alaka da zabar su.
Manyan muryoyi a fasgen kafafen watsa labarai na masu ra'ayin rikau - a dukkan shafukansu kuma suka yi ta maimaita wa a duniyarsu - su ne Elon Musk da Joe Rogan. Elon Musk, sananne da ya mallaki kamfanin Tesla mai kera moticin da ke aiki da lantarki da SpaceX, wanda kuma ya sayi Twitter a 2022.
Kamfanin ya dawo da shafin Trump, wanda aka rufe da dakatarwa bayan zanga-zangar US capitl da aka yi a ranar 6 ga Janairu, sannan ya daga matsayin batun masu ra'ayin rikau.
Musk da kansa ya nuna Trump yake goyon baya, Joe Rogan, wanda shirye-shiryensa na podcast suka yi shuhura a Amurka, shi ma ya dinga tallata wa da nuna Trump. Alkalumanmu za su iya zama masu amfani wajen ganin yadda ra'ayoyin wadannan mutane ke da alaka da zabin dan takara a lokacin zabe.
A ra'ayin Elon Musk, kashi 85 na mutane da suke da wani ra'ayinsu sun zabi Trump, inda kashi 91 na wadnad aba su da ra'ayinsa ba su zabi Trump ba.
Idan aka dawo ga Joe Rogan kuma, kashi 76 na wadanda ke son sa, sun zabi Trump, inda kashi 78 na wadanda ba sa tare da shi ko suke da wani ra'ayi na daban, ba su zabi Trump ba.
Kazalika, mutanen da ba sa tare da Musk da Rogan na iya tunanin cewa Donald Trump ne dan takarar da ya fi cancanta a zaben 2020.
A yayin da wadannan alkaluma ba su da tabbas game da tasirin wadannan kan zabin dan takara, amma suna kuma nuni ga cewa mutanen da ke son wadannan daidaikun mutane, kuma wadanda akwai yiwuwar su mayar da hankali da bibiyar sakonninsu, to su ne suka zabi Donald Trump.
Gaskiya mabambanta
Shirye-shiryen masu ra'ayin rikau na sanya tunani a kwakwalen mutane kan su amince da abubuwan da suke so. Amma kuma, wadannan kafafen watsa labarai sun dinga yada karya, don su amfanar da Donald Trump.
To ga makomar da ake iya hange, ana ganin karkatar kafafen yada labarai ga bangaren masu ra'ayin rikau zai ci gaba.
Shin ya damu masu jefa kuri'a cewa suna shan karya ne? Salena Zito, wadda ke dakko labarai game da Trump ga The Atlantic, ta bayyana cewa: "kafafan watsa labarai ba su dauke shi da muhimmanci ba; amma masu goyon bayansa sun dauke shi da muhimmanci." To, kalaman Trump ba matsala ba ne ga magoya bayansa.
Babu tabbas a loakcin mulkin Trump na biyu karfin fada a ji na kafafan watsa labarai masu ra'ayin rikau zai kara karfi. Manyan kafafan watsa labarai irin su The Washington Post da The Los Angeles sun yanke hukuncin ba za su nuna wani dan takara da suke goyon baya ba a lokacin zaben, amma kwamitin tashe labaransu kuma sun goyi bayan Harris.
Da yawa sun dinga shaci-fadin cewa wannan mataki na da manufar kauce wa bata wa Trump rai, saboda tsoron rasa kafar sadarwa, da watakila kwangilolin kasuwanci da sauran bukatun mamallakansu biloniyoyi ke da su daga wajen gwamanatin Amurka.
Kazalika, Trump ya yi alkawarin gudanar da gwamnati da za ta kakkabe kafafen watsa labaran da bai yard da su ba - inda har ma ya dinga kiran su da 'makiyan bangarenmu" a jawabin nasarar da ya yi makon da ya wuce. To ga makomar da ake iya hange, ana ganin karkatar kafafen yada labarai ga bangaren masu ra'ayin rikau zai ci gaba.
Marubuci, Todd Belt farfesa ne kuma daraktan Digiri na Biyu Kan Gudanar da Siyasa a Jami'ar George Washington. Shi ne daya daga marubutan litattafai da suka hada da The Presidency and Domestic Policy, tare da Michael Genovese da marigayi William Lammers.
Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.