Bangaren fasahar kirkirar saututtuka ya samu sauye-sauye a shekarun da suka gabata. Hoto: Getty Images

Daga Muzhinga Kankinda

Nahiyar Afrika tana da dadadden tarihin fasahar kirkirar saututtuka na daruruwan shekaru. A wannan makalar, saututtuka na nufin duk wani irin sauti ko murya da aka kirkira kuma ake watsawa domin isar da sako.

Ya kunshi waka, magana, rediyo, nadar saututtuka da watsa labarai ta rediyon intanet da sauransu. A takaice, sauti na taka nuhimmiyar rawa a tarihin al'adu da addini, da siyasa da yanayin mutanen Afrika da fasahar kirkirarsu.

Yana kuma taimakawa wajen isar da sako tsakanin nahiyar da sauran yankuna da nahiyoyin duniya. Fasahar sauti ta farko a Afrika ita ce fasahar tsararrun magana. Ta kunshi ilimantarwa da bayar da labari a cikin tsararrun magana.

Duk da cewa ya dan ja baya kadan, amma har yanzu wasu kabilun Afrika suna cigaba da amfani da tsararren magana wajen isar da sako.

Ya kunshi karin magana, kirkirarrun tarihin magabata da tatsuniyoyi da wakoki da wakokin baka wadanda a wasu lokutan ake amfani da kayan kida kamar ganguna da kaho da sauransu.

Bambance-bambancen al'ada

Waka na cikin saututtuka a Afrika. Tana cikin al'adun mutanen Afrika, domin tana bayyana yanayin kabila da yanki da bambance-bambancen al'adu a nahiyar.

A Afrika, waka tana da amfani daban-daban, kamar nishadantarwa da sadarwa da ilimantarwa da waraka da ma karfafa gwiwa.

Rediyo, wanda nau'in sauti ne wanda bai dade ba sosai a Afrika kasancewar ya zo ne a farkon Karni na 20 ta wajen turawan Mulkin Mallaka da kuma ci gaban zamani, shi ma ya taimaka wajen ilimantarwa da farfaganda da yada labarai da nishadantarwa da fafutika.

Haka kuma yana taimakawa wajen yada samar da hadin kai a tsakanin mutanen Afrika. Duk da haka, rediyo na fuskantar kalubale da dama, ciki har da gasa tsakanin tashohin da fama hukumar tace tashoshin.

Gabatar da shirye-shirye ta intanet

A dayan bangaren kuma, zuwan intanet yana barazana ga cigaba da amfani da kafofin sadarwa na dauri irin su rediyo.

Daya daga cikin wadannan hanyoyin sadarwar ta intanet akwai rediyon intanet wato podcast. Rediyon intanet wata hanya ce ta sauraron shirye-shirye ko sauke su a intanet.

Rediyon intanet yana cikin sababbin hanyoyin yada labarai da ke barazana ga tsofaffin hanyoyin yada labarai. Hoto: AP

Wadannan sababbin hanyoyin yada labarai na zamanin suna kara samun karbuwa a 'yan shekarun nan saboda ta wadannan hanyoyin, mutane suna samun damar sauroron labarai da sauran bayanai da yada su cikin sauki.

Tarihin fasahar saututtuka a Afrika ya kunshi hada saututtuka da kirkira da isar da sako. Wannan bai rasa nasaba da kasancewar saututtuka a Afrika sun taimaka wajen gyara al'adu da siyasa da tattalin arzikin nahiyar.

Sun kuma bayar da gudunmuwa sosai a al'adun duniya baki daya. A yanzu, abin farin ciki shi ne yadda 'yan Afrika suka fara amfani da fasahar kirkirar wajen bude kungiyoyi da sauransu don amfanar junansu.

Daga cikin wadannan kungiyoyin akwai Kungiyar Masu Gabatar da Shirye-shirye ta Rediyon Intanet da masu Fasahar Saututtuka (APVA), wadda ita ce kungiya da take shirya taron karrama masu irin wadannan fasahohi mafi girma, watakila ma ita kada ce a Afrika, mai suna African Podcasters and Voice Awards, wato APVA a takaice.

Taron karramawar ta APVA taro ne da ake yi duk shekara domin karrama gwanayen fasahar kirkirar saututtuka a Afrika da ma wasu kasashen.

Karramawar na taimakawa wajen karfafa gwiwar masu fasahar, tun daga masu gabatar da shirye-shiryen rediyon intanet da masu shirya saututtuka da tsararren magana daga Afrika da ma kasashen waje, domin bayyana fasaharsu ga duniya.

Lallai karramawar APVA ta zo a daidai lokacin da aka fi bukatarta- lokacin da gidajen rediyon intanet ke kara samun karbuwa.

Haka kuma ta zo a daidai lokacin da za ta daukaka darajar masu fasahohin nan a Afrika, su kuma yi yaki da kalubalen da suke fuskanta a harkar.

Bikin AVPA na 2023 wanda Kungiyar Masu shirye-shirye ta rediyon intanet suka shirya a Zambia. Hoto: Kungiyar Masu shirye-shirye ta rediyon intanet.

Bayan haka, masu fasahar kirkirar da masu bayar da labarai za su samu wata damar kirkirar saututtuka masu inganci, har da bayyana al'adu da fasahar kirkirar nahiyar.

A daya bangaren kuma, karramawar APVA tana ba masu fasahar damar sanin juna da kulla alaka a tsakaninsu.

Haka kuma karramawar ta zama wata dandamalin baje kolin fasahohi da karfafa gwiwa domin masu fasahar kirkirar saututtuka da bayar da labarai domin su bayyana godunmuwar da suke bayarwa wajen yada labarai a kafofin sadarwa na Afrika.

Hakan ya taimaka wajen taimakon masu fasahohin su yi yaki da matsalolin da suke fuskanta. Yanzu haka, Kungiyar APVA ta fara wayar da kan mutane a kan muhimmancin saututtuka a matsayin kafar bayar da labarai da ilimantarwa da nishadantarwa da gyara halayyar mutanen Afrika.

Misali, daga cikin tsare-tsaren kungiyar akwai yunkurin kulla alaka a tsakanin masu fasahohin, sannan masu fasahar sun samu wata inuwar tattara kan su a waje daya domin samun hadaka da taimakon juna domin ci gaban bangaren.

Ba karramawar ba ce kawai

Misali irin wadannan wuraren shi ne shafin APVA na twitter da taron bikin karramawa da ke tattara masu bayar da labarai da dama a inuwa daya domin su tattauna a tsakaninsu.

Misali, taron karramawa ta APVA ta 2023, mai taken, "Muryoyin gaba" da ya tattara masu fasahar kirkira a Zambia da Kenya da Nijeriya inda suka dade suna tattauna abubuwan da suka shafi fasahohin bayar da labarai da saututtuka da hadin kai a tsakaninsu.

Bayan haka kuma bayar da irin wannan karramawa za su taimaka wajen karfafa musu gwiwa domin su kara kaimi wajen aikinsu.

Yanzu haka an fara samun cigaban da ake bukata.

Misali, kusan masu gabatar da shirye-shirye ta rediyon intanet guda 2,320 da masu tsara magana ne aka zabe domin shiga gasar karramawar ta 2023.

Sannan zaben yana ba masu fasahohin damar jin ra'ayoyin masu sauraronsu domin samun damar yi musu abin da suke so.

Masu shirye-shirye ta rediyon intanet da na masu fasahar wakokin baka da sauran fasahohi suna gabatar da kayatattun shirye-shirye irin su shirin rediyon intanet na rayuwa wanda Labang ke gabatarwa wato Life with Lebang, wanda shi ne ya lashe karramawar gwarzon shekara, da shirin The Mothers wanda Grace ke gabatarwa da African Woman da That Zed da The Tech Talk Afrika da sauransu su.

Taron bikin ta APVA ba wai karramawa ba ce kawai domin tana kuma darajar fasahohi da kirkirar mutanen Afrika, kamar sauran hanyoyin yada labarai irin su talabijin da fim. Taron kuma yana kara ba masu fasahohin damar bayar da labaransu tare da isar da sakonsu zuwa ga duniya.

Taron waje ne da tsofaffin hannu da kuma sababbin shiga haduwa. Dandamali ne da ke taimakawa wajen bayyana kirkira da daga martabar fasahohin kirkira a Afrika.

Marubucin wannan mukala, Muzhinga Kankinda, marubuci ne daga Zambia kuma yana cikin wadanda suka rubuta littafin The Economic Case of Investing in Podcasters and Voice Artists.

Togaciya: Abubuwan da aka bayyana a cikin wannan makala ba dole ba ne ya zama ya yi daidai da ra'ayi da ka'idojun arikin jarida na kafar TRT Afrika.

TRT Afrika