Hoton Babban Bankin Zambiya da ke Lusaka / Hoto: Reuters

Daga Muzhinga Kankinda

A yayin da duniya ke sauyawa daga tsarin gargajiya zuwa tsarin dijital wajen gudanar da ayyuka, Zambiya ta yi fice. Kasar tana rungumar fasahohin cigaba da ke kawo sauyi a fagen rayuwa da tattalin arziki.

Wannan guguwar sauyi ba wai ta kawo habakar arziki ba ne a Zambiya, har ma ta janyo yaduwar hanyoyin samar da ayyukan-yi da sabbin kasuwanci.

Wannan habaka ta haifar da gagarumin cigaba a sana’o’i da al’adu, da samar da arziki, tare da inganta karfin gogayyar kasar Zambiya a tattalin arzikin duniya.

Guguwar sauyin dijital a Zambiya ta kuma fadada damar samun bayanai a ayyuka ga al’umma.

Samuwar cibiyoyin kudi na dijital, da kasuwanci ta intanet, da kamfanonin intanet, sun wadata ‘yan Zambiya da damar cin moriyar arziki da ilimi da kiwon lafiya samun ayyuka daga gwamnati.

Wannan fage na habaka al’umma ta hanyar dijital ya inganta diadaito da kawo sauyi kan yadda mutanen Zambiya ke rayuwa da samun ilimi.

Sannan kuma, fasahohin dijital sun janyo dabarun sgugabanci ta intanet, da daidaita tsarin gudanarwa, da kawar da rashawa, da inganta samar da ayyuka ga al’umma.

Wani batu da ke kan gaba shi ne hukumar tara haraji ta Zambiya wadda ta kaddamar da tsarin biyan haraji ta intanet, don saukaka biyan haraji da samar da bayanai, wanda hakan ya habaka tsari da bin dokokin haraji.

Guguwar sauyin dijital a Zambiya ta haura fannin fasaha. Ta hada da batun samar da makoma wadda kayayyakin aikin dijital ke saka azamar cigaba, da kyautata rayuwa da cimma muradun cigaba mai dorewa.

Yayin da Zambiya ke cigaba a fannin dijital, akwai bukatar dabarun hangen nesa, da tsare-tsare, da hadin gwiwa don cimma daukacin damarmakin da ke hakar.

Yaduwar intanet

Duk da cigaba a fannin dijital, kasar Zambiya na fama da rashi yaduwar harkar. Kasancewar kashi 21.2% na al’ummar kasar ne suke da intanet zuwa watan Janairun 2023, Zambiya tana sahun baya a matsakaicin ma’aunin kashi 63.6% cikin 100 da ake da shi a duniya.

Hakan nan kuma, yawan amfani da kafofin sadarwar zamani yana matakin kashi 18.7% cikin 100, wanda adadi ne da ke kasa da matsakaici adadi a fadin duniya, wato na kashi 51.7% cikin 100.

A hakan, na’urorin masu aiki da intanet na tafi-da-gidanka, wadanda ywancinsu na biya ne kafin amfani, sun kai kashi 44.8% cikin 100 na ‘al’umma, wanda ya saba wa matsakaicin adadin a fadin duniya, na kashi 108%.

Jerin masu hada-hadar kudi na tafi-da-gidanka suna zaune a cibiyar kasuwanci ta Lusaka, Zambiya ranar 23 ga Fabrairun 2024. / Hoto: Reuters

Kalubalen da ke kan yaduwar intanet a Zambiya suna da sarkakiya. Akwai karancin kayayyakin aiki wanda ke janyo raja’a kan cibiyon tafi-da-gidanka. Amma kum kashi 40% cikin 100 ne na al’umma kacal suke samun sabis na 3G ko 4G.

Bugu da kari, akwai tsadar siyan data, wanda ya kai matsakaicin farashin $8.01 duk GB, wanda ke nufin samun intanet ya yi wasu tsada sosai.

A cewar jaridar Zambia Monitor, wanda ke cikin manyan gidajen labarai Zambiya, an saka kasar a mataki na hudu a jerin kasashe masu tsadar ciyan data a Afirka tsakanin watan Yuni da Satumbar 2023.

A wani bangaren, yawan masu ilimin na kashi 63.4% cikin 100, hadi da rashin kwarewa a fannin kwamfuta, shi ma yana rage amfani da intanet. Haka nan akwai karancin masu kirkira na cikin gida, da dokokin masu tauye cigaba.

Sakamakon haka, cigaban dijital a Zambiya batu ne na cigaban mai cike da damar habaka. Amma kuma yana nuna bukatar daukar matakai don dinke bambancin wajen samun alfanun harkar.

Yayin da Zambiya ke samun tagomashi a harkar, dole a sanya ido kan samar da daidaito da samar da kayayyakin cigaba, da inganta ilimin kwamfuta da intanet.

Kayayyaki da tsare-tsare

Kasancewa guguwar saiyin harkar dijital tana kawo cigaba a fadin duniya, harkar tana kawo nata kalubalen, da hadarurruka a fagen tsaron intanet, da tsare sirri, da saka-ido, da daidaito.

Wani rahoto na Bankin Duniya, ya yi nuni kan muhimman bangarori kamar rashin kudin jagorancin cigaban dijital, da karancin wayewar kwamfuta da intanet, da karanci ko tsadar samun intanet, da rauni wajen saka-ido da shugabantar harkar.

Kasar kuma tana fama da barazanar inatanet da ke iya shafar tsaron kasa, da zaman lafiya, da lumana.

Wadannan sun hada da hari kan cibiyoyin intanet, kamar yadda aka gani a 2019 lokacin da aka kai hari kan shafukan gwamnati, da cin zarafi ta intanet, da maganganun nuna tsana, da bayana karya, wadanda duka suna gusar da aminci da al’umma ke da shi kan gwamnati.

Haka kuma, rashin daidaito yana da yawa wanda ke haifar da wasu rukunin al’umma musamman na karkara da mata da matasa da masu nakasa suna gaza cin moriyar alfanun fasahohin intanet.

A bayyane yake cewa dole Zambiya ta dauki mataki kan wannn gibin domin samar da gamewa wajen amfana da guguwar sauyin dijital.

Damarmakin arziki da na zamantakewa

Guguwar sauyi a harkar dijital a Zambiya tana dauke da damar kawo babban cigaban tattalin arziki da na zamantakewa.

Karin kashi 10 cikin dari kacal a yaduwar intanet zai iya bunkasa tattalin arizikin Zambiya a ma’aunin GDP da kashi 1.12% cikin dari, a cewar rahoton Bankin Duniya.

Wannan sauyi kuma zai samar da karin ayyuka miliyan 1. Zuwa shekarar 2030 a fannoni daban daban, da habaka ayyukan kiwon lafiya, da ilimi, da taimakon al’umma.

Wannan cigaban a harkar dijital ta Zambiya wani cigaba ne da ke faruwa karkashin shugabancin Shugaba Hakainde Hichilema. / Hoto: Reuters

Ga kasar Zambiya, wadda ba ta da iyaka da teku, sauyin harkar kwamfuta zai bude kofofin sabbin cigaba, da sana’o’i da ilimi da kiwon lafiya da shugabanci.

Ayyukan dijital kamar da banki ta intanet, da shagunan inatnet masu aiki da hasken rana, da samar da kananan bashi ta inatnet, sun saukaka harkar biyan kudade ta intanet da kashi 26% cikin 100 tsakanin Janairu zuwa Afrilun 2020.

‘Yan Zambiya suna kara samun alfanu daga kasuwanci ta kwamfuta, da koyo da shugabanci da kiwon lafiya da kwamfuta, da kuma samun bayanai da nishadi.

Alal misali, kafofi kamar DotCom Zambia, da Zamgoat Products suna taimaka wa masu sana’a su cimma kasuwannin gida da waje, yayin da kafofi kamar Mwabu suke samar da abubuwan ilimi a harsunan gida.

A wani bangaren, cibbiyoyin kirkira, da na kyankyasar kayayyakin cigaba, da na gina cigaba, da na aikin tarayya, suna taka rawa a fagen cigaban kwamfuta a Zambiya.

Wadannan kafofi, kamar BongoHive da Impact Hub Lusaka, sun aba wa masu kirkira a Zambiya, da masu sana’a wani jagoranci da horo da kudade da damar hadin-gwiwa.

Wadanda suka ci moriyar sabbin kamfanoni kamar Musanga Logistics, da BongoHive, shiada ne na alfanun wadannan kafofi, da ke samar da aikin kai kaya ta hanyar ayarin kekuna.

A takaice dai, guguwar sauyi harkar dijital a Zambiya ba a fannin fasaha ta tsaya ba, ta kunshi bude hanyoyin cigaba, da tafiyar da hanyoyin da harkar za ta inganta rayuwar mutane.

Mafita

Don cin moriyar sauyin dijital da cimma manufofin cigaba, ya wajaba Zambiya ta zuba jari a kayayyakin gina harkar da kuma tsare-tsare. Ga wasu gagaruman matakai:

Wannan dabara ya kamata ta Tsarin Cigaban Kasa na takwas 8th National Development Plan (8NDP), da zai bayar da mahanga, da matafiya, da jagoranci kan shirye-shiryen dijital a fannoni daban daban.

Ta hanyar shirye-shiryen ilimi, da horo, da wayar da kai, gwamnati za ta iya daukaka ilimin dijital, tsakanin al’umma. Wadannan shirye-shirye dole su hado da kowa da kowa don kawo cigaba a bangarori bai-daya.

Tsarin sa-ido

Tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni, da tarayya wajen amfani da kayayyakin aiki, da da samar da kudade don habaka samar da babbar hanyar intanet mai sauki, da inganta gofayya da tafiya tare.

Sabunta dokoki da tsare-tsare kan tsaron intanet, da kare bayanai, da kasuwancin intanet, da shugabanci ta intante, da hakkoki masu amfani da fasaha, da kafa hukumomin sak-ido masu zaman aknsu, da gina kwarewa tsakanin fannoni da kula da karkar intanet.

Ta hanyar kula da wadannan bukatu, Zambiya za ta kara kaimi ga guguwar sauyin, da samar da kasa mai tafiya da kowa, a wannan karni na cigaban harkar kwamfuta.

Sauyin da Zambiya ka samu a harkar kwamfuta tuni ya fara samar da alfanu, da inganta samar da kayayyaki, da kirkira, da ilimi, da lafiya da shugabanci.

Shirye-shiryen dijital da suka yi nasara sun hada da shirin e-voucher ga manoma, da cibiyoyin kudi na tafi-da-gidanka, da harkokin banki ta inatnet, da koyarwa ta intanet, da bayar da labarai.

Sai dai kuma, don habaka bayar da dama ga kowa da kowa, dole Zambiya ta zuba karin jari a kayayyakin gina harkar dijital, da kyawawan tsare-tsare da kwarewa.

Hadin gwiwa da gamayya tsakanin gwamnati, kamfanoni, da kungiyoyi masu zaman kansu, da masu tallafawa harkar yana da muhimmanci wajen inganta sauyin.

Yayin da Zambiya ke cimma cigaba a fannin dijital, yana da alfanu ga kowa ya shiga a dama da shi a wannan guguwar sauyi.

Ya wajaba masana harkokin kwamfuta, da gwamnati da al’umma su goyi bayan shirye-shiryen dijital, da na koyon kwarewa, da samar da labarum da ke nuna damarmaki da tasirin harkar kwamfuta a Zambiya.

Marubucin, Muzhinga Kankinda, dan Zambiya ne wanda ke cikan marubutan littafin “The Economic Case of Investing in Podcasters and Voice Artists”.

Togaciya: Ra’ayin da marubucin ya bayyana bas a wakiltar ra’ayi, mahanga, da tsarin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika