Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a ranar 2 ga Maris na 2024 a birnin Los Angeles da ke California. (David McNew/Getty Images).      

Daga Lincoln Rice

Tun a watan Oktoban bara da Isra'ila ta kaddamar da farmaki a Gaza, ta hanyar amfani da makaman da akasarinsu daga Amurka take samu, Amurkawa da dama sun fara tunanin yiwuwar daina daukar nauyin kisan gilla da kudinsu.

Amurka tana ba Isra’aila agajin soji na sama da Dala biliyan uku duk shekara, sannan ta kara yawan agajin tun daga Oktoban bara da aka fara yakin.

Sannan daga Yakin Duniya na biyu, Amurka ta ba Isra’ila taimakon soji sama da wata kasa a duniya, inda adadin kudin da Amurka ta kashe wajen tallafin sojin ya kai Dala biliyan 317.

Bayan cire tallafin Social Security da na Medicare, wadanda dukansu wasu kudade ne da ake warewa kuma ake kashewa daban daga kudaden haraji, Kungiyar War Resistance League ta ce ayyukan soji ne ke lakume kusan kashi 45 na kasafin kudin kasar. A Kasafin Kudin Shugaban Kasa Biden na shekarar 2025, wannan kason na nufin Dala triliyan 2.25.

Dukkan kudin nan ana samunsu ne daga kudin harajin mutanen Amurka, ko suna so, ko ba sa so. Amma yanzu an fara samun masu nuna turjiya.

Kin biyan haraji

Kungiyar Kin biyan haraji wato The National War Tax Resistance Coordinating Committee (NWTRCC) ya samo asali a shekarar 1982, inda wasu kungiyoyi masu ra’ayi iri daya suka hadu domin adawa da harajin soja.

A takaice, abin da suke so shi ne a daina biya dukkan haraji ko wasu daga cikin harajin Gwamnatin Tarayya.

Sanin hakikanin adadin wadanda ba sa son biyan harajin da kamar wuya, amma dai za su iya haura mutum 10,000. Kafin farmakin Gaza da Isra’ila ta yi, shafin intanet na NWTRCC na samun masu ziyarar musamman guda 40,000 duk shekara, amma yanzu muna samun kusan 20,000 duk wata.

A farko-farkon watan Nuwamba, da mutane suka fara ganewa tare da fahimtar da’awar NWTRCC, sai da shafinmu ya tsaya cak. An sake samun hakan sau biyu a karshe-karshen shekarar 2023, har sai da ala dole muka bunkasa shafin.

Mutane suna ziyartar shafinmu ne domin su fahimci yadda za su rage wasu daga cikin harajin da suke ba gwmanati. Sannan suna so su fahimci girman laifin da zai hau kansu idan suka ki biyan harajin.

A Amurka, laifi ne mutum ya ki biyan haraji. Amma a cikin gomman shekarun da suka gabata, kasar ba ta gurfanar da mutane da yawa ba bisa laifin kin biyan haraji.

Yakin ya-ki-ya-ki-cinyewa

Bayan halin da ake ciki a Gaza, Amurka na cigaba da “yaki da ta’addanci” da ta dade tana yi ta hanyar amfani da jirage marasa matuka a kasashe irin su Afghanistan da Syria da Yemen. Haka kuma Amurka tana da sojoji a sama da sansanonin soji guda 800 a fadin duniya.

Kin biyan haraji wata hanya ce ta hawa teburin na ki. A wajen wasunmu da muka ki shiga aikin soja, muna ganin me zai sa kuma mu dauki nauyin yaki?

Wannan tambayar ce ta sa Amurkawa da dama suka daina biyan haraji a lokacin yakin Vietnan da wasu yakokin.

A shekarun 1990s ne na fara tunanin daina biyan haraji bayan na ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka na wancan lokacin, Madeleine Albright na bayyanawa a wata tattaunawa cewa dubban kananan yaran da suka mutu a Iraqi saboda yunwa “sun cancanci” mutuwa.

Tun wancan lokacin na daina biyan harajin na radin kaina. A game da harajin, Kungiyar NWTRCC tana shirya tarukan wayar da kan mutane duk mako na yadda za su fahimci matsalolin da suke tattare da kin biyan haraji.

Daga cikin masu daukar nauyin tarukan har da Kungiyar Lauyoyi da Kungiyar Ma’aikatan Lafiyar Falasdina na San Francisco.

Yawancin masu shiga fafutikar matasa ne ’yan kasa da shekara 30, sannan akwai mutane daga kowane bangare na duniya.

Yawanci ta Instagram ne suke samun bayani game da tafiyar, inda shafinmu yake ta samun karbuwa. Kafin farmakin Gaza, masu bibiyan shafinmu ba su wuce 500 ba, amma yanzu mun kusa 20,000.

Zanga-zanga a kan kashe kudade a aikin soja

A Ranar Haraji (15 ga Afrilu) ta bana, dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a sassa daba-daban na Amurka-Chico da California da Manhattan da New York domin nuna adawa da kudaden ake kashe wa ayyukan sojin kasar.

Hotuna daga zanga-zanga a kan kekuna mai taken #WarTaxResistance da ake yi Kudu maso Yammacin Wisconsin a Afrilun 2024, ciki har da ya yi shiga irin ta Captain America. Hoto daga NWTRCC.

Da yawan masu zanga-zangar sun nuna rashin jin dadinsu a kan yadda suke biyan harajin, sannan suka bayyana wasu matsaloli da ke tattare da kasafin kudin kasar.

Ba mu da asalin kididdigar yadda ake kashe kudaden masu biyan harajin, amma dai ko ma menene, kashe Dala tiriliyan biyu a ayyukan soji ba daidai ba ne.

Misali, a yammacin Ranar Haraji, masu adawa da biyan harajin a Portland da Oregon sun rika daga alamaun rashin jin dadin kisar gilla.

A birane da dama, da kungiyoyi da dama sun rika yin kuri’ar kasafin kudi, inda ake ba mutane kudi a ce su kasafta a bangarorin da suka fi muhimmanci.

A Kudu maso Yammacin Wisconsin, wani daga masu zanga-zanga shiga ya yi irin ta Captain America, ya hau keke ya tukawa har zuwa Babban Birnin Jihar, inda ya rika tsaya a kananan garuruwan da ke hanya yana wayar da mutanen yankunan a kan kin biyan haraji.

A takaice, kin biyan harajin ba yana nufin mutum ya daina yin abin da rataya a wuyarsa ba ne na biyan hakkin. Abin da suke yi shi ne, kudin da suka tara a sanadiyar kin biyan harajin, suna amfani da su ne wajen tallafa wa wasu kungiyoyi da ba su da isassun kudi.

Sannan kowa na kai nasa kudin ne ga kungiyar da take bukatar kudin a kusa da shi. Misali, Shenandoah Valley Taxes for Peace da ke Harrisonburg a Virginia suna shirya taron karkatar da kudin haraji zuwa ga kananan kungiyoyi da suke kira da suna “Redirection Vigil” a wajen shakatawa ta LOVE da ke kusa da Kasuwar Manoma ta Harrisonburg.

Suna karbar kudaden harajin da aka karkatar zuwa wajensu ne zuwa ga kungiyoyin zaman lafiya da neman adalci.

A Oakland da ke Caliornia, Kungiyar Northern California War Tax Resistance & People’s Life Fund ya karkatar da $67,000 da suka tara ga kananan kungiyoyin da suke aikace-aikacen gayya a unguwanni da taimakon marasa galihu a duk ranar 17 ga Afrilu.

Haka ma masu kin biyan harajin sukan karkatar da kudadensu zuwa ga batun kula da matsalolin sauyin yanayi.

Sojin Amurka ne kan gaba wajen amfani da man fetur a duniya. Jirgin F-35A, idan ya kure gudunsa, a awa daya yana kona fetur din da mai mota da bai cika zirga-zirga ba zai kona a shekara biyu.

Bayan haka, yarjejeniyar kula da sauyin yanayi, kamar ta Paris ta cire ayyukan sojoji a cikin dokokin kula da abubuwan da suke jawo sauyin yanayi.

Da suke bayyana alakar ayyukan sojin Amurka da illa ga muhalli, masu fafutikar kin biyan harajin sun fara aiki tare da kungiyoyin kare gurbacewar muhalli domin kara karfin ayyukansu.

Duk da cewa laifi ne mutum ya ki biyan haraji da gangan, babban sakamakon rashin biyan shi ne a tura wa mutum takardar laifi wadda watakila a cire wa mutun kudin harajin kai-tsaya daga bankinsa ko kuma a bukaci inda yake aiki su cire kudin su tura wa gwamnati kai-tsaye.

Idan aka kama ko aka ci tarar wani mamba a fafutikar, wasu suna tara masa kudi domin yam aye gurbin kudin da ya kashe, ko ya rage zafi.

Marubucin: Lincoln Rice shi ne kodinetan Kungiyar National War Tax Resistance Coordinating Committee (NWTRCC) tun daga shekarar 2018, kuma shugaban Kungiyar war tax resister tun 1998. Ya yi digirinsa na uku a addinin Kirista a Jami’ar Marquette a shekarar 2013. Ya rubuta littafai da makala da dama da suka shafi adalcin zamantakewa da launin fata.

TRT Afrika