Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, wadda ake mata kirari da kasar da ta fi kowacce arzikin albarkatun ƙasa a duniya, tana cikin tsaka mai wuya, biyo bayan rantsar da sabon shugaban ƙasar a baya-bayan nan.
An ƙiyasta ma'adinan ƙ=kasar da ba yi amfani da su ba kan dalar Amurka tiriliyan 24, wadanda ba kawai arzikin al'ummar Kongo za su iya sauyawa ba, har da ba da gudunmawa mai gwaɓi ga ci gaban nahiyar Afirka baki ɗaya.
Sai dai duk da haka, hanyar da za ta kai ga samun wannan ci gaba na fama da tarin ƙalubale na rashin kwanciyar hankali a tsawon shekaru da dama da kuma rikice-rikicen siyasa da almundahana da tattalin arzikin kasar.
Tabon tarihin
Tushen ƙalubalen da Kongo ta faɗa ciki ya samo asali ne tun daga taron Berlin na shekarar 1885, inda manyan ƙasashen duniya suka raba Afirka a tsakaninsu.
Sarki Leopold na biyu na Belgium ya ƙwace ikon wani yanki mai fadin gaske a tsakiyar Afirka, inda ya sanya wa suna kasar Kongo Free State.
Wannan shi ne mafarin babi mai duhu a tarihin Kongo, wanda ke tattare da hare-hare da mulkin kama-karya da rashin mutunta ƙima da darajar ɗan'adam wajen adalci a zamantakewa.
Gwagwarmayar al'ummar Kongo ta neman ƴancin kai ta kasance jigo ruyuwarsu ta yau da kullun, inda aka shafe tsawon shekaru da dama ana zaluntarsu ta fuskar siyasa, ana kuma aikata laifuka ba tare da wani hukunci ba.
Tabon wannan tarihi na ci gaba da yin tasiri a fagen tattalin arziki da siyasar ƙasar.
Durƙushewar tattalin arziki
Gadon irin satar albarkatun ƙasar da aka yi sun wuce abin da tahiri ya yi nuni akai, kamar yadda John Perkins ya bayyana a cikin wata maƙala da ya rubuta mai suna, "Confessions of an Economic Hitman."
Perkins ya fallasa muguwar guguwar durƙushewar tattalin arziki wanda aka yi amfani da tasirin gwamnatoci wajen biyan bukatun kamfanoni da manyan mutane masu arziki.
Waɗannan ƙwararru da aka biya ƙudade sun yi mafani da dabaru iri-iri da suka haɗa da bayanan rahotannin karya kan kuɗi da magudin zaɓe da ƙwace, har ma da tashe-tashen hankali.
Ko shakka babu masana'antar haƙar ma'adinai ita ce ta fi fuskantar wannan lahani mai munin gaske da yawancin ƙasashen Afirka ciki har da Kongo ke ciki.
Ba za a iya misalta tasirin irin durkushewar tattalin arzikin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ba.
Tasirin satar albarkatu ya cutar da al'ummar yankin, kazalika ya ta'azzara talauci da rikice-rikicen siyasa.
To a yayin da al'ummar kasar suka shiga wani sabon babi tare da samun sabon Shugaban ƙasa, magance wadannan al'amurra da suka shafi tsarin ƙasar ya zama wajibi don samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Albarkatun kasa da ba a yi amfani da su ba
Tarin albarkatun ƙasa, gami da ma'adinai na kuza mafi girma a duniya da ɗimbin sinadarin Cobait, za su samar da damarmaki da ƙalubale ga Kongo.
Duk da cewa wadannan albarkatu suna da karfin da za su iya daukaka tattalin arzikin Kongo da kuma amfanar da daukacin nahiyar Afirka, rashin kula da kuma satarsu sun kasance tushen duk wani tashin hankali da ake fuskanta.
Bikin rantsar da sabon shugaban ya haifar da tambayoyi masu mahimmanci game da yadda kasar za ta yi amfani da arzikinta ta yadda za ta amfanar da al'ummarta.
Shin sabon jagorancin zai ba da fifiko wajen tafiyar da gaskiya da kulawa ga albarkatun ƙasa, wajen tabbatar da cewa fa'idojin sun isa ga al'umma da dama?
Ko kuwa za a ci gaba da satar da albarkatun ne kamar yadda aka saba, ta yadda za a kara fadada tazarar da ke tsakanin talaka da mai kudi?
Yaki da Talauci
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke haifar da talauci a DRC shi ne rashin zaman lafiya da ake fama da shi na tsawon shekaru na yaƙe-yaƙe da rigingimun siyasa.
Tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin ayyukan yi da matasa suke fama da shi, ya dada haifar da tashe-tashen hankula da kawo cikas ga ci gaban kasar.
Dole ne sabuwar gwamnati ta magance waɗannan matsaloli da suka samo asali tun daga tushe don share fagen samun sauyi mai dorewa.
Tattaunawa da bangarorin da ke dauke da makamai da saka hannun jari a shirye-shiryen samar da ayyukan yi, da kuma samar da yanayin da zai dace da masu saka hannayen jari daga kasashen waje duk matakai ne masu muhimmanci da za su tinkare kalubalen tattalin arziki.
Ta hanyar mayar da hankali kan rage radadin talauci da samar da ayyukan yi ga matasa, gwamnati za ta iya samar da gidauniya ta ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Mafitar da ke gaba
Don warware matsalolin da suka dabaibaye kangin tarihin satar albarkatun kasar, dole ne sabon shugaban ya yi mai da hankali sosai wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Samar da hanyoyin da za su bi diddigin kudaden shiga daga hakar albarkatun kasa da aiwatar da matakan yaki da cin hanci da rashawa, da kuma cudanya da abokan hulda na kashen waje don tabbatar da ana gudanar da harkokin kasuwanci yadda ya kamata.
Samar da cikakken shirye-shiryen ayyuka, makamancin katin rahoton da mukalar Perkins'memoir ya ambato, zai iya taimakawa wajen zama kayan aikin da zai sa ido kan ci gaba da kuma inganta sadarwa da masu ruwa da tsaki.
Wannan alƙawarin tabbatar da gaskiya ba wai kawai zai sanya ƙwarin gwiwa a cikin gida ba har ma da jawo hankalin masu zuba jari na waje da ke ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci.
A yayin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kango ke shiga wani sabon babi tare da sabon shugabanta da aka rantsar, idanun duniya na kan tattalin arzikin kasar.
Tasirin tarin albarkatun ƙasa, haɗe da tarihin yadda aka yi amfani da su, na nuna irin sarƙaƙƙiyar da ke gaba.
Dole ne sabuwar gwamnatin ta gudanar da waɗannan ƙalubalen tare da tsayawa tsayin daka don tabbatar da gaskiya da riƙon amana da ci gaba mai ma'ana.
Farfadowa daga koma baya
Fatan dai yana tattare da yiwuwar kasar Kongo ta fita daga cikin rigingimun da ta yi a baya da kuma yin amfani da dukiyoyinta domin amfanin al'ummarta.
Tare da tsare-tsare masu muhimmanci da ɗaukar nauyi daga gwamnati da haɗin gwiwar ƙasashen duniya, DRC za ta iya ba da hanya ga kyakkyawar makoma mai haske da wadata.
Tambayar ko yaushe ita ce: Shin rantsar da sabon shugaban zai samar da begen da ake buƙata domin jan hankalin al'ummar ƙasar wajen samun sauyin tattalin arziki? Lokaci ne kawai zai nuna.
Marubucin wannan maƙala, Mohamed Guleid, ya kasance marubuci a harkokin da suka shafi Afirka, kana shi ne shugaba da ke kula da ayyukan NEDI na ƙasa, wani shirin Ci gaban yankin Arewa maso Gabashin Afirka.
Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko manufofin TRT Afirka ba.