Daga William A. Booth
Masu zaɓe a Mexico sun zaɓi ra'ayinsu bayan sun zaɓi Claudia Sheinbaum a matsayin shugaban ƙasa ta farko mace, inda ta ruɓanya ƙuri'un da abokin hamayyarta da ke binta a baya Xóchitl Gálvez ya samu.
A daidai lokacin da ake cikin fargabar rikici kan 'yan takarar da masu zaɓe - an kash 'yan takara aƙalla 34 a kakar wannan zaɓen a ƙasar.
Kusan mutum miliyan 60 ne suka gudanar da zaɓen, wanda wani lamari ne na murna. Da alama Sheinbaum ta Jam'iyyar Morena wadda ita ce jam'iyya mai mulki da kuma jam'iyyun da suka yi haɗaka da su sun yi matuƙar ƙoƙari a zaɓen.
A Birnin Mexico misali, Clara Brugada ya yi nasarar zama magajin gari da bambancin kaso 10 cikin 100 na ƙuri'u, duk da cewa masu sharhi na ganin cewa da ƙyar ya sha. Ya dace yayin da Mexico ke zabar shugabar kasa mace ta farko, shugaba mafi muhimmanci a yankin za ta kasance wata mace.
Me nasarar da Sheinbaum ta samu ke nufi ga Mexico? A wani ɓangaren, fiye da hakan.
Tsayawa inda ake
Ta yi nuni da cewa za ta ci gaba da tafiyar da tafarkin siyasar da tsohon shugaban kasar Andres Manuel López Obrador (aka AMLO) ya kafa - bayan haka, wannan kuri'a ce ga jam'iyyar kamar na dan takara.
Kuma wannan wata jam'iyya ce da ta samu nasarori a cikin shekaru shida da suka gabata waɗanda suka haɗa da gagarumaar raguwar rashin daidaito da aka samu a lokacin da ake fama damatsalar tattalin arziki (wanda shi kadai ya sa ta zama sabon abu a Latin Amurka); fadada ma'ana kan batun fansho; kuma watakila a bayyane yake, ninka mafi ƙarancin albashi.
Duk da ikirari da ‘yan adawa suka yi, wannan zaben bai shafi gurguzu wani ɓangare ba, kamar yadda muka sani.
Jawabin nasarar Sheinbaum ya kasance mai sulhuntawa. Ko da yake ta amince da adawa mai ƙarfi daga wasu sassan al'umma, ta kawo saƙon "zaman lafiya da jituwa" da kuma alƙawarin ci gaba da tafiya zuwa "Mexico mai adalci da wadata."
A yadda duniya ke kallon lamarin, New York Times ta kira nasarar Sheinbaum da nasara ta farin jini. Sai dai farin jini ya fi kama da wani nau'in siyasa fiye da manufa kuma Sheinbaum ba kamar AMLO ba ce.
Dagaske take yi, sai dai ba ta fito na fito kamar wanda ya gabace ta, kuma ta nuna alamun saka himma da samar da daidaito. Waɗannan duk wasu ginshiƙai ne na farin jini.
Anan, ina tsammanin, muna kasa bambance farin jini da da shahara. Akwai gardama da za a yi game da yadda ake tattara madafun iko, kuma ko yawan jama'a yana ƙara yiwuwar gwamnatin Jam'iyyar Morena mai zuwa za ta yi watsi da 'yan adawa.
Ɗayan daga cikin sukar da ake yi wa AMLO ita ce amfani amfani da sojoji a wurare, wanda ba lamari ne da zai sauya ba.
Wani kuma shi ne rungumar sa na samar da iskar gas don tabbatar da yancin kai na Mexico.
Ba tare da la'akari da ɗabi'a ko ingancin irin wannan hanyar ba, wannan sh ne ɓangaren da mutane da yawa ke ganin Sheinbaum za ta iya bin hanyarta domin yin abubuwa. A matsayinta na mai ilimin kimiyyar yanayi, tana jin zafin abin da canjin yanayi zai kawo wa Mexico, da kuma kudancin duniya gabaɗaya.
Alaƙar ƙasashen waje
Yana da wuya a san abin da nasarar Morena ke iya nufi ga alakar da Mexico ke da ita da sauran ƙasashen waje. A karkashin López Obrador, an mayar da hankalin Mexico sosai a ciki, kuma an ba da wasu fadace-fadacen siyasa da ke gaba - musamman idan an shirya gyare-gyaren tsarin mulki - wannan na iya ci gaba.
Sai dai akwai yiwuwar Sheinbaum saka Mexico a cikin manyan mayan ƙawancen yanki. An yi shekaru 75 masu kyau tun lokacin da Mexico ta ga kanta (aƙalla a matakin gwamnati) a matsayin mafi yawan Latin Amurka fiye da ƙasar Arewacin Amurka.
Ko shi López Obrador ya kasance mai jajircewa sosai idan aka zo batun shirye-shiryen yanki. A karshen wa'adin shugabancinsa, ya bi sahun Colombia da Chile wajen adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza. Idan kwanciyar hankali na cikin gida zai iya ba Sheinbaum wani sarari don aiki, zai kasance ga Mexico da sauran fa'idar juna ta Latin Amurka.
Guatemala, Brazil, Colombia da Chile (a tsakanin wasu) duk suna cikin fagen siyasar Mexico, kuma idan aka fuskanci tsari na masu ra'ayin riƙau na Kiristanci, wasu ƙawayen yanki za su kasance masu fa'ida sosai.
Wannan ya kawo mu ga dangantaka da Amurka, inda abu ya dogara da sakamakon zaben Nuwamba. AMLO bai san Trump ba, amma kuma bai ja baya ba musamman kan manufofin ƙaura.
Trump - kasancewarsa ɗan wariyar launin fata,- yana iya yiwuwa ba zai so ya yi hulɗa da Sheinbaum a daidai wannan matakin ba. Shige da fice ya mamaye fagen siyasa na "Colossus na Arewa" wanda ya sa Biden na iya yin aiki irin wannan.
Latin Amurka tana samar da kusan kashi 7 na ma'aunin tattalin arziƙi na duniya, amma ina shakkar ta mamaye ko da kashi 1 na labaran duniya. Tsakanin su, Brazil da Mexico sun yi daidai da tattalin arziki da Indiya.
Dr. William A. Booth is a Lecturer in Latin American History at University College London. He is currently finishing a book on the left in Latin America during the early Cold War. These are personal views and do not reflect the views of the university or of his department.
Marubucin Dakta William A.Booth malami ne da ke koyar da tarihin Latin Amurka a University College da ke Landan. A halin yanzu yana kammala littafinsa kan Latin Amurka a lokacin yaƙin cacar baka.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.