Shugaban Amurka Joe Biden a tsakiya, a wajen gangamin zabw a Majami'ar Mother Emanuel AME da ke Charleston, Carolina ta Arewa a ranar Litinin 8 ga Janairn 2024. Hoto: (Sam Wolfe/Bloomberg via Getty Images).

Daga Youssef Chouhoud

Jam'iyyar Democrat a Amurka na kan gaɓa mai hatsari. A yayin da take rasa goyon baya daga Amurkawa Larabawa da Musulmai da matasa saboda goyon bayan Isra'ila da ke yaƙi a Gaza, shugabanni da dama na kallon wannan barazana ce ga sake zabar Joe Biden a zabe mai zuwa.

Muhawarar da ake yi ta mayar da hankali ga cewa adadin Larabawa da Musulmai ba su da yawan da za a nuna damuwa da su game da jefa kuri'a a zaben.

Kuma matasa ma ba su cika fita zaɓe ba kamar sauran rukunin jama'a, a saboda haka me ya sa ake jin tsoro, ake mantawa da dattawa Amurkawa da suke jefa ƙuri'a da yawa.

Amma kuma akwai wani bangare na al'umma da Democrat ba za su yi wasa da shi ba, su ne Amurkawa Bakar Fara.

Yadda jam'iyyar Democrates take a cakude, da kuma duba ga yankunan da Biden ya fi samun magoya baya, za a ga yadda jam'iyya ke da=garo kan al'ummu masu launi fata daban-daban.

A babban zaben 2020, kaso 60 na kuri'un da aka jefa wa Biden sun fito ne daga fararen fata, idan aka kwatanta da sama da kaso 85 na Trump.

Ba don bakaken fata da ke goyon bayan Biden ba, da ko tikitin takara a jama'iyyarsa ba zai samu ba a wjaen zbane fidda gwanin da aka yi a watan Mayun shekarar.

Wadannan masu jefa kuri'ar dai ba sa kallon yiwuwar komawa Biden kan mulki a karo na biyu da karsashi.

Tun kafin 7 ga Oktoba ma, farin jinin Biden a wajen Amurkawan da ba farar fata ba ya fara raguwa, saboda yadda gwamnatin ta gaza cika alkawaran da ta yi iri su batun 'yan sanda, batun aikata manyan laifuka da hukunta su.

'Yan majalisar yankuna a Amurka sun bi sahun manyan kungoiyoyin kasar wajen kira ga Biden da ya nuna cikakken goyon byan ofishinsa ga kare hakkokin jefa kuri'a. Hoto: (Alex Wong/Getty Images).

Amma kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan ta bayyana cewa gaza ma na taka rawa a kuri'un bakaken fata game da Biden.

A karshen watan Agustan 2023, Cibiyar Binciken Addinin Jama'a ta gano cewa kaso 77 na Amurkawa Bakaken Fata za su zabi Biden a yayin karawa da Trump. Akwai raguwar kaso 15 daga goyon bayan da ya samu daga bakaken fatar a zaben 2020.

Ya zuwa karshen watan Nuwamba, Genforward sun gano cewa kaso 63 na Amurkawa Bakaken fata ne suke da niyyar zabar Biden.

Haka kuma kuri'ar da NBC ta yi ta jin ra'ayin jama'a ta nuna abu makamancin haka inda kaso 61 na wannan jama'a suka amince da kwazon Biden.

A yayin da wadannan zabuka kawai na bayyana ra'ayin jama'a ne, wasu batutuwa na magana kai tsaye ga tasirin rikicin Gaza wanda ke shafar boyon baya ga Biden a tsakanin al'ummun Bakaken Fatar Amurka.

Akwai nuna bacin rai daga kungiyoyin farar hula, 'yan boko da sauran jama'a game da yadda Biden ke goyon bayan kisan kiyashin da ake yi a Gaza.

Suka mafi muni ga manufofin Biden ya zone daga pastoci 1,000 bakar fata da suke tilastawa gwamnatin d ata yi kira ga tsagaita wuta.

A baya-bayan nan ma shugaban Cocin African methodist Episcopal sun yi nisa inda suka yi kira ga Amurka da ta dakatar da taimaka wa Isra'ila.

Kungiyoyin masu fafutuka irin su 'Black Lives Matter' ma sun bayyana matsayinsu kan rikicin Gaza, gwagwramayar 'The Movement for Black Lives' na nuna goyon baya ga Kungiyar Kubutar da Gwagwarmayar Falasdinawa.

Mace na jefa kuri'a a yayin da Democrtas da Republican ke gudanar da zabukan cikin gida na fitar da dan takarar shugaban kasa a Michigan a ranar 27 ga Fabrairu, 2024 (REUTERS/Dieu-Nalio Chery).

Amma ba wai wadanda suka fi mayar da hankali ba ne suke bayyana bijirewar su. Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da New York Times/Sienna suka gudanar a watan Disamba ta bayyana cewa Amurkawa Bakar Fata sun fi nuna tausayi ga Falasdinawa sama da farar fata da Hispaniyawa.

Dadin dadawa, a jihar Michigan mai muhimmanci, kuri'ar watan Disamba ta bayyana sama da kaso 60 na bakar fata da ke Detroit na goyon bayan tsagaita wuta a Gaza - kuma an fitar da rahoton daga jin ra'ayin jama'a na watanni biyu, inda aka amu kashe fararen hula 10,000.

Tabbas, babu wanda ya san tarihin yaushe gwagwarmayar bakaken fata ta faro a Amurka amma za ku yi mamakin irin yada ake nuna goyon baya ga Gaza.

A can baya a 1964, misali Malcolm X, a wajen taron Hadin Kan Afirka ya bayar da shawarar kare "hakkokin Larabawa 'yan gudun hijira su koma Falasdin".

Shekaru kadan bayan haka Kungiyar bakaken fata ta 'Black Panther Party' sun bayyana karara suna goyon Falasdinawa.

Domin tabbatarwa, a wancan lokacin Amurkawa Bakar Fata ba su hade kai da kungiyar Falasdinu ba.

A tarihi da ma yau, halayya game da Falasdinawa da Yahudawa na da wahalar fahimta, inda dangantakar ta dogara ne kan dadaddiyar alakar Yahudawa da Afirka.

Wannan harshen damo na iya tafiyar wahainiya a matsakaici da dogon zango, sai dai kuma, Amurkawa bakaken fata da sauran 'yan asalin kasar musamman ma millenial da Gen-Zers, sun yi nisa wajen nuna adawarsu ga manufofin Amurka kan Isra'ila da Falasdin.

Haka kuma, wadannan halaye na smaun karbuwa a wajen Amurkawa matasa Yahudawa.

Wannan sauyi ya zama barazana ga jam'iyyar Democrat. Wadannan masu jefa kuri'a matasa sun karkasu kuma sun damu matyuka game da adalci a zamantakewa - za su zama mafi yawa a masu jefa kuri'a a Amurka ba wa a wani lokaci mai tsawo ba, a'a a lokacin zaben shugaban kasa da ke tafe.

Don haka, a yayin da sakamakon manufofin kasashen waje na Biden zai zama ya yi zangon mulki daya, kuma goyon bayansa kan cusgunawa Gaza da Isra'ila ke yi na iya illata jam'iyyar har bayan 2024.

Idan 'yan Democrat na son ci gaba da samun cikakken goyon bayan jama'arsu, to dole ne su dauki matakan kawar da zaluncin da ake yi a Falasdinawa na sama da shekara 75. Alkawarin karya da dadin baki kawai ba za su warware matsalar ba.

To me Biden da 'yan jam'iyyar Democrat za su yi na kubuta daga wannan annoba ta rasa magoya baya da ke samun su?

A ra'ayin wasu, a gaskiyance, babu wani abu da Biden zai yi ya ake dawo da goyon bayan da ya samu a November. Amma wasu na iya goyon bayan kudirin shugaban na sake tsayawa takara idan har ya kawo tsagaita zuwa ta dindindin a Gaza, sannan ya dakatar da bayar da taimakon soji ga Isra'ila, da kuma fadada kai kayan agaji ga Falasdinawa.

A dogon zango, dole ne Jam'iyyar Democrat ta fahimci: babu batun komawa kamar yadda suke a baya. Idan tafiya ta zo, za a gano yadda masu jefa kuri'a na babnare biyu za su kalli Isra'ila.

Idan 'yan Democrat na son ci gaba da rike goyon bayan da suke samu daga bangarori daban-daban, to dole su dauki matakan kawo gyara a rashin adalci da zaluncin da ake yi wa Falasdinawa tsawon shekaru 75. Kananan kalamai da alkawura da ba a cika wa ba za su yi tasiri ba.

Marubucin, Youssef Chouhoud, Mataimakin Farfesa ne a Kimiyyar SIyasa a Jami'ar Christopher Newport inda yake kuma hulda da Cibiyar Kare Hakkokin Dan Adam da Warware Rikici ta Reif.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika