Sassaken kan wata matashiya mai girman santimita 19. Hoto: AP

Daga Yahya Habil

A makon farko na watan Disamba, kasar Switzerland ta dawo da wani sassaken tarihi na kasar Libya mai shekara 2,000.

Sassaken na kan wata matashiya ne, wanda aka sace a birnin Cyrene na Libya mai dadadden tarihi, sannan aka gano shi a wani wajen adana kayayyakin tarihi shekara 10 da suka gabata, sannan kuma yanzu aka dawo da shi bayan Ma'aikatar Al'adu ta Switzerland ta mika shi a Ofishin Jakadancin Libya da ke birnin Bern.

Wannan nasarar ta bude wata kofa a yunkurin kasashen Afirka na fafutikar dawo da kayayyakin tarihinsu da Turawa suka sace, wadanda yawanci aka sace a lokacin mulkin mallaka da aka yi a nahiyar.

Sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba a game da dawo da kayayyakin tarihin da Turawa suka sace daga Afirka, wadanda ko kunya ba sa ji waje nuna su a gidajen adana kayayyakin tarihisu.

Misalin wannan shi ne sassaken Rosetta Stone. Masu binciken kayayyakin tarihi da sauran masu bincike suna amfani da wannan sassaken wajen auna tarihin Masar.

Duk da cewa asali an sace shi ne daga Rundunar Sojin Napoleon ta Faransa. Daga bisani dutsen ya wayi gari a Birtaniya, bayan sojojin Birtaniya sun ci Faransa da yaki a Masar a shekarar 1801.

Sassaken 'queen mother ' na Kamaru

Wani misali na kayayyakin tarihi da aka sace daga Afirka aka kai Turai shi ne sassaken Ngonnso, wanda ake kira da "queen mother" na mutanen Nso.

Sylvie Vernyuy Njobati ta dade tana fafutikar dawo da sassaken Ngonnso da yanzu haka yake Berlin. Hoto: Marc Sebastian Eils/SHF

Sassaken ya dade a kasar Jamus, inda ya kwashe sama da shekara 100 a can babu alamar dawowa saboda yadda hanyoyin dawo da shi suka yi tsauri. Bayan haka, sassaken yana cikin akalla kayayyakin tarihi guda 40,000 da aka sace daga Kamaru, yanzu suke gidajen adana kayayyakin tarihi a kasar Jamus.

Sylvie Vernyuy Njobati ta dade tana fafutikar dawo da sassaken Ngonnso da yanzu haka yake Berlin. Hoto: Marc Sebastian Eils/SHF

Adadin kayayyakin tarihin da aka sace daga Afirka ba abin mamaki ba ne kasancewar duk inda aka yi wa mulkin mallaka sai an sace wani abu, ko dai a sace kasa ko arzikin kasar ko kayayyakin tarihi.

Abin nufi a nan shi ne, masu mulkin mallaka ba sa barin kasa face sun saci wani yankin na kasar ko arzikin kasar, idan kuwa haka ne, me zai hana su sace 'kananan' abubuwan kamar kayayyakin tarihi?

Kasashen Turawa ma ba su sha ba a game da irin wannan satar, don haka me ya sa za a yi mamaki idan sun sace na kasashen Afirka?

A shekarar 1796, lokacin da Janar Napoleon ya je yaki kasar Italiya tare da sojojin Faransa, ya tarar da wasu kayatattun kayayyakin fasaha ciki har da Michelangeloda Vinci.

A lokacin da aka yi yarjejeniyar tsagaita ta Bologna, sai ya kwace sama da sassake da sauran kayayyakin fasaha da sama da 100.

Don haka ba abin mamaki ba ne idan Napoleon da ya aikata hakan a Masar, inda ya sace Rosetta Stone a 1799.

Bayan haka, kasancewar yawanci a zamanin mulkin mallaka ne satar ta faru, hakan ba ya nufin cewa a zamanin mulkin mallakar ne kadai, domin har yanzu ana ci gaba da mulkin mallaka da sace kayayyakin ta bayan fage.

A 2022, an tuhumi tsohon Shugaban Gidan Adana Kayayyakin Tarihin Louvre, Jean-Luc Martinez da hada baki wajen boye asalin wasu kayayyakin tarihi wadanda alamu suka nuna daga Masar aka yi fasakaurinsu, a lokacin hatsaniyar yankin Larabawa na 2011.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa masu binciken Faransa da dama sun yi zargin cewa an sace daruruwan kayayyakin tarihi a lokacin hatsaniyar yankin Larabawa ta shekarar 2011, inda aka sayar da su a gidajen adana kayayyakin tarihi, wadanda yawanci ba sa tambayar daga Ina aka samo su.

Kuma akwai kamshin gaskiya a batun, domin sassaken fitacciyar sarauniyar Girka, Persephone, an sace shi ne daga birnin Cyrene na Libya a shekarar 2011, aka kai Birtaniya, duk da cewa daga baya an dawo da shi bayan sun samu nasara a kotu.

Wannan lamarin da sauran ire-irensu na nuna cewa har yanzu ana cigaba da sace kayayyakin tarihi.

Dalilin da ya ke nuna alamar cigaban lamarin shi ne yadda a karshe dai a Turai kayayyakin suke karewa, inda a lokuta da dama ake nuna su a gidajen adana kayayyakin tarihi manya domin samun kudin shiga.

Wannan bai da bambanci da tsarin da aka bi a zamanin mulkin mallaka, inda kasashen Turai suke samun kudin shiga daga arzikin kasashen Afirka.

Abin farin ciki shi ne kasashen Afirka sun fara bude ido, inda suke ta fafutikar ganin an dawo musu da kayayyakinsu. Sai dai a lokuta da dama, ba sa samun nasara.

Sojojin Birtaniya sun yi gwanjon wasu tagulla na Masarautar Benin da aka sace a 1897 a Turai. Hoto: AFP

Kiraye-kirayen da kasashen Afirka ke yi na a dawo musu da kayayyakinsu na kara samun karbuwa, domin wannan ne kadai hanyar da za a bi wajen dawo da su.

Akwai kasashen Turai da dama da suka amince za su dawo da kayayyakin tarihin da suka sace, kamar Tagulla na Masarautar Benin (wadda ke Kudancin Nijeriya a yanzu).

Ya kamata sauran kasashen Afirka su yi koyi da Nijeriya wajen kwato kayayyakinsu kamar yadda kasar ta kwato tagulla da dama a gidajen adana kayayyakin tarihi na wasu kasashen Turai.

Babbar lemar kasashen Afirka, Tarayyar Afirka wato AU ma ta fara nuna damuwa a game da batun, inda ta fara shigewa gaba wajen ganin an kwato kayayyakin.

A shekarar 2022, a taron Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka wato EU-AU da aka yi a birnin Brussels, Shugaban Tarayyar Afirka, Macky Sall ya nanata muhimmancin dawo da kayayyakin tarihi da aka sace aka kai Turai, domin a cewarsa, suna "nuna asalin yankin."

Sai dai duk da haka, akwai bukatar AU din ta kara kaimi domin tabbatar da an samu nasara, a matsayinta ta babbar wakiliyar nahiyar.

Kuma ya kamata kasashen Afirka su cire kunya da kawaici domin suma wadanda suka yi satar ba sa jin kunyar nuna kayayyakin, kamar yadda suke nuna sassaken kan gwarzon kwatar 'yancin kasar Aljeriya a gidan adana kayayyakin tarihi na Louvre.

Lura da irin wadannan rashin adalcin da aka yi wa kasashen Afirka wajen nuna kayayyakinsu a gidajen adana kayayyakin tarihi a Turai, bai kamata kasashen Afirka su yi kasa a gwiwa ba wajen kwato kayayyakinsu.

Marubucin, Yahya Habil, dan jaridar wucin gadi ne ma Libya, wanda ya fi mayar da hankali a kan harkokin Afirka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afirka.

TRT Afrika