Manyan jagororin diflomasiyya daga kasashen Musulmi na ayyukan kalubalantar girmamar Kyamar Musulunci a karni na ashirin da daya. / Hoto: AA

Daga Ian Proud

Karni na 21 ya shaida daduwarnuna kyamar Musulunci a kasashen Yamma, wanda a lokaci guda, suka nemi kakaba salon rayuwar Yamma da zabar bangare a rikice-rikicen da ake yi a duniya.

Babban batun ma shi ne Musulmai jami'an diflomasiyya sun bazama wajen zama dattawan duniya inda suke wanzar da zaman lafiya mai girma a ban kasa.

Biyo bayan kulla yarjeneniya da Turkiyya ta jagoranta, an saki wasu 'yan kasar Thailand biyar da aka tsare a Gaza.

Wannan ne misali na baya bayan nan na yadda kasar Musulmi ta dauki matakin samar da diflomasiyya tare da cike gibin da Amurka da kawayenta na Yamma suka bari.

Watanni biyu da suka gabata, A Disamba, Suugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da "sulhu mai tarihi" tsakanin Ethiopia da Somalia bayan shiga tsakanin da Ankara ta yi.

A 2022, Turkiyya ta karbi bakuncin tattaunawar Zaman Lafiya ta Istanbul, wadda ta kusa kawo karshen rikicin Ukraine wata guda bayan fara shi, amma Amurka da Ingila suka dakile wannan yunkuri.

Turkiyya ta kawo Rasha da Ukraine zuwa waje guda don yarda kan Yarjejeniyar Hatsi ta Tekun Maliya don bayar da kariya ga ayyukan jigilar hatsi da takin zamani, ciki har da wanda za a kai kasashe masu tasowa.

Sauran kasashen Musulmi na yin nasu kokarin. Turkiyya da Saudiyya sun shiga tsakanin don sakin fursunonin yaki 'yan kasashen Yamma da aka kama a Rasha a watan Satumban 2022.

A 2023, Saudiyya ta karbi bakuncin tattaunawae Zaman Lafiya a birnin Jedda game da rikicin Ukraine. hadaddiyar Daular Larabawa ta taka babbar rawa wajen sakin fursnonin Rasha da na Ukraine, da ma gawarwakin sojojin da aka kashe.

A baya bayan nan Qatar ta shiga tsakani a matakin farko na tsagaita wuta a Gaza kuma an samu rahotannin sun karbi bakuncin tattaunawar farko tsakanin Rasha da Ukraine da manufar kawo karshen yakin na shekaru uku.

Tsawon shekaru Qatar ta zama cibiyar tattaunawa tsakanin Amurka da Taliban kafin kasashen Yamma su dauki matakin ficewa daga Afganistan gaba daya a 2021.

Kyamar Musulunci da Yammacin duniya

Manyan jagororin diflomasiyya daga kasashen Musulmi na ayyukan kalubalantar girmamar Kyamar Musulunci a karni na ashirin da daya.

Ba a shekarar 2001 aka kirkiri nuna kyama ga Musulunci ba, amma harin ta'addanci na 11 ga Satumba a Cibiyar Kasuwanci ta DUniya da ke New York a birnin Washington ya sanya karuwar ta a Amurka da ma Yammacin duniya.

Kyamar Musulunci na amfani da bayanai na karya da ke da cutarwa ga Musulmai da darajar Musulunci, ana yawan yayata hakan t=ta hannayen masu tsaurin ra'ayi da ke yada karya. bayan harin 9/11 a makon an kashe wasu mutane uku a Amurka, daya daga ciki Ba'amurke mai bin addinin Sikh da aka yi zaton dan gudun hijira ne Musulmi saboda kalar fatarsa da gemunsa.

Wannan lamari ya ci gaba har zuwa yau. Rahoton da Cibiyar Pew ta fitar ya bayyana cewa hare-haren nuna kyama ga Musulmai a Amurka ya haura na 2001 a 2016. Bayan fara yaki tsakanin Hamas da Isra'ila a watan Oktoban 2023, sai abin ya kara tsamari.

Nuna kyama ga Musulunci ya kara karfafa goyon bayan duniya ga yaki da ta'addanci da Amurka ke jagoranta a duniya wanda aka fara bayan harin na 9/11, wanda aka kaddamar da afkawa Afganistan da kuma yakin Iraki na biyu.

An yi kiyasin wannan ya janyo wa Amurka kashe dala tiriliyan takwas da kuma janyo asarar rayukan mutane 900,000, mafi yawan su ba su ji ba ba su gani ba.

Hakan ya janyo hanzarta daukar matakai cikin gaggawa, inda ake kashe wadanda ake zargi ba tare da tuhumar su a kotunan shari'a ba, wadanda aka yi garkuwa da su a kasashe waje tare da kai su gidajen kurkukun Amurka don tuhuma. A 2008, an tirsasa gwamnatin Birtaniya neman afuwa saboda goyon bayan irin wadannan matakai da Amurka ta dauka.

Nuna kyama ga Musulunci ya yi yawa a sosai a siyasar Birtaniya. An zargi jam'iyyar Leba mai mulki a Birtaniya da nuna kyama ga Musulunci a baya.

A shekarar 2021 an tilastawa jam'iyyar Masu Ra'ayin Rikau da ta yi mulki a Birtaniya daga 2010 zuwa 2024 ta nemi afuwa bayan wani rahoto mai zaman kansa ya bayyana cewa "halayyar kyamar Musulunci na ci gaba da zama matsala".

A matakin kasa da kasa, ana yawan suka kasashen Musulmi saboda gazawar dabbaka dimokuradiyya da zargin raunin kare hakkokin dan adam.

Kare hakkokin dan adam da dimokuradiyya ne tubalan da Turai ke amfani da su don hana matsawar Turkiyya zuwa ga shiga Tarayyar Turai, wanda abu ne mai da kamar wuya.

Duk da haka, ma'aikatan Turkiyya sun taimaka wajen habakr tattalin arzikin Jamus ta Yamma, amma idan aka kalli zaman su a matsayin 'Gasterbeiter' (Ma'aikata Baki) za a iya cewa alaka ce ta tatsa da nuna bambancin launi.

A 2022 a yayin gasar Kwallon Kafa ta Cin Kofin Duniya a Qatar manyan mawakan Yamma irin su Sporty Spice da Rod Stewart sun cashe yadda suke so.

Ya zama ruwan dare ga kafafan yada labarai na Yamma su bayar da rahoto kan zuba jarin biliyoyin daloli na Saudiyya a bangaren wasanni a matsayin sabuwar hanyar sauya labaran keta hakkokin dan adam - ko boye tasirin gurbata muhalli a ayyukan diban man ta da ake yi.

Kasashen Musulmi na fuskantar kiran su da masu kama-karya inda ake kwatanta su da da China da Rasha ana cewa duk daya suke.

'Yan kasashen Yamma sun dimautu da kokarin da gwamnatoci ke yi na samar da 'yanci da tafiya tare da kowa.

Kuma, yawan rahotanni game da kasashen Musulmi ba su da wata daraja ga bambancin addini da al'adu da suke da shi, kuma ba sa wani kokarin baiwa Musulmi damar jin cewa an karbe su a cikin al'ummar Birtaniya ko wani waje.

Fuska biyu a kalaman Yamma

An samar da wani sabon salo a Yammacin duniya a shekaru ashirin da suka gabata - dokokin - sabon tsarin duniya.

Wadannan dokoki babu su a cikin wani kundi na kasa da kasa, kamar Yarjejeniyar MDD ta 1945, wadda ta nemi a wanzar da zaman lafiya, kare mutunci, adalci da kula da lafiya.

Diflomasiyyar Yammacin duniya ta zabi ta dauki wadanda suke yin nasara a rikicin kasa da kasa.

Wani dan karamin tsagi a Yammacin duniya ne kawai yake amfani da wadancan dokoki na kasa da kasa, wanda Amurka ke musu jagoranci, don su tabbatar da wacce kasa ce take tare da mu, wacce ce ba ta tare da mu, a ambatar George W Bush.

Karni na 21 ya shaida tafiya ta gaba daya daga diflomasiyyar da aka saba gani a tattare da Kasashen Yamma.

Birtaniya da dukkan kasashen tarayyar Turai ba sa kallon kawunansu a matsayin wanda ba ya takalar kowa, masu shiga tsakani a rikicin duniya.

Maimakon haka, sun yi watsi da shiga tsakani, suna neman su zama masu nasara ne kan duk wani da ke rikici da suka fahimci makiyinsu ne.

Mun ga haka a yakin Rasha da Ukraine, inda manyan kasashen duniya ke ganin nasarar Ukraine da ba mai samuwa ba ce ta fi maimakon a ce a samar da zaman lafiya ta hanyar sulhu.

Kuma kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza, inda suka kashe sama da mutane 48,000 da ba su ji ba ba su gani ba, Amurka da Birtaniya, sun gaza dakatar da Netanyahu da ke kara zama mai hatsari.

Tabbas, sabon zababben shugaba Trump ya nemi ya tsame Netanyahu daga tuhuma kan takunkuman Kotun Kasa da Kasa Mai Hukunta Manyan Laifuka da da kuma yin barazana ga duk wanda ya nemi ya ce a hukunta Netanyahu a kotu.

Kasashen Muslmai sun shiga wannan fage na kasa da kasa don nuna dattako.

Abin mamaki shi ne yadda a cikin shekaru ashirin da Nuna Kyama ga Musulunci ya kara yawa kuma aka samu sauyin tarbiyya daga Yammacin duniya daga diflomasiyya ingantracciya, sai kuma Musulmai masana diflomasiyya suka dauki ragamar samar da zaman lafiya a duniya.

Marubuci, Ian Proud tsohon Jami'in Diflomasiyyar Birtaniya ne kuma wanda ya rubuta 'A Misfit in Moscow: How British Diplomacy in Russia Failed'.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika