Zeby aya fi mayar da hankali ne ga 'yan Afirka mazauna kasashen waje./Hoto: Aaron Zeby

Daga Firmain Mbadinga

Djollo Aaron Zeby wani mai zane ne dan kasar Italiya amma dan asalin Ivory Coast, wanda ya cika babban burinsa - hada sana'ar zane ta Afirka da zayyanar zamani.

Ya bai wa wannan sana'ar zayyana tasa suna Afroekletism. Yana nuna surorin fuskokin Afirka, fenti da kwaba kasar tukwane a yanayi mai kayatarwa kamar launin rawaya (Kalar da ya fi so), ruwan kasa ko ma launin fari.

Kayan da ake samarwa daga Afroekletism sun riga sun samu karbuwa a wurin jama'a.

Aaron Zeby na son kawata sassakar fuskokin Afirka./Hoto: Aaron Zeby

Ana sassaka ne yayin gudanar da wannan aiki, a yi musu fenti tare da malkwada su yadda ake bukata, sannan sakamakon daukar awanni da yake yi wajen aiki da hankalinsa da ayyukansa, masoya ayyukan sana'ar sassaka ta zamani na nuna sha'awarsu sosai.

Suna ma jan hankalin kafafen watsa labarai da ma mutanen da suke ganin zane na gundurarsu.

Djollo Aaaron Zeby na son kawar da matsalar damuwa da ke addabar wasu mutanen ta hanyar ayyukansa.

Aaron Zeby na son kawata sassakar fuskokin Afirka inda za su zama ba wai a fagen al'adu kawai ake amfani da su ba.

Ya ce "A koyaushe na yi amanna cewa akwai tazara a kasuwanni game da adon cikin gida na Yammacin Afirka. Afroekletism ce hanyata ta kirkirar wani abu da ya bambanta da saura wanda ke jan hankalin kowa, kuma kowa zai iya ajiye shi a gidansa."

Aaron Zeby na fitar da surori masu kyawu ta hanyar ayyukansa./Hoto: Aaron Zeby

Ilhama

A farkon wannan shekarar ne a lokacin da Aaaron Zeby ke kwance a asibiti ya samu ilhamar yin wannan sana'a ta Afroekletism, a lokacin wata cuta da ta kusa raba shi da kafarsa ko ma rayuwarsa.

Matashin, mai shekaru 30 wanda har zuwa wannan lokaci yana aikin sadarwa, ya samu ilhama daga wani bidiyo da ya kalla a wayarsa game da kirkirarriyar basira.

Mutum ne da a koyaushe yake kaunar zane-zane, kuma ya alakanta shi da al'adun nahiyarsa ta asali.

Ya raya a zuciyarsa cewa zai iya zana kwarangwal na wasu surori, sannan ya kara musu ado kafin yi musu fenti.

Aaron Zeby mutum ne da a koyaushe yake kaunar zane-zane. /Hoto: Aaron Zeby

Yadda ya faro

Masanin falsafa na Faransa Albert Camus ya ce "Muna rayuwa da dabaru wadanda idan muka yi aiki da su za su sauya rayuwarmu baki daya."

Ta hanyar aiki da wannan kalami ne Djollo Aaron Zeby yake ta kokarin jan hankalin duniya da zane-zanen Afirka.

Sai baban Afroekletism ya samu lafiya ya fita daga asibiti, inda ya fara tunanin kirkirar sura ta farko.

A abun da ya samar a karon farko, ya so ya samar da wasu ka'idoji da za su yi masa dan jagora.

Ya bayyana cewa "Ina cakuda abubuwa da suke da alaka da Voodoo, wanda wani bangare ne na al'adun Afirka, duk da dai ba ni da tushe da shi. Na kuma sake ziyartar tatsuniyoyin Afirka da almara don samar da nawa aikin."

Aaron Zeby

Aaron Zeby ya kara da cewa "Ina son isar da wadannan al'adu masu kyau ga kowa ta hanyar wannan aiki da nake yo mai kayatarwa, musamman ma ga 'yan Afirka da ke zaune a kasashen ketare, wadanda aka haifa a tsakanin al'adu biyu.

A aikinsa na farko, Aaron Zeby ya zana fuskar dan adam, ya yi mata fenti launin rawaya da bakin baya na kai, wand aya kira "Adam". Wannan aiki ya bayar da labari mai cike da alamomi.

Mai sana'ar zanen ya bayyana cewa "A matsayi na na dan malamin coci, na so na siffanta Adam, mutumin da aka fara halitta, wanda ke wakiltar dukkan dan adam. Wannan Adam din na dauke da tuffa, ya zama ya dimautu da tuffah din tasa, wand ake nufin fasahar kere-kere, ilimi da cigaba."

Ya kuma ce "tare da wannan aiki, ina son karfafa gwiwar mutane su yi tunani game da zabi da ake kiran su ga shi a rayuwa, saboda shi wannan Adam, saboda zabin da ya yi na daukar tuffa, sai ga shi rayuwa ta janye hankalinsa gaba daya."

Aaron Zeby

Aaron Zeby ya kuma ce wata daya bayan kaddamar da shafin intanet, wanda ta nan yake bayyana wa duniya aikin nasa, ya samu ra'ayoyin mutane da dama, ya samu masu saya ciki har da 'yan wasan kwallon kafa da suka fito daga ko'ina.

Amma kuma, matashin dan Afirka da Italiya ya ce yana fuskantar suka saboda amfani da kirkirarriyar basira don zayyana hotunan nasa.

Amma kuma idan aka yi la'akari da yadda Afirka take da masu son al'adunta, har yanzu bai fuskanci wata matsala ko kyara ba.

Domin makoma, Aaron Zeby na shirin cimma duk wata bukatar kayan da aka nemi a saya don bai wa mutane su.

Yana kuma fatan ya samu hadin kai da manyan masu sayar da hotuna tare da aiki da kwararru masu zane na Afirka.

Duk da cewa Afroeklestic na farko da ya samar sun fi karkakata ga fenti da sassaka, Aaaron Zeby na da wata dabara na fadada zanensa zuwa ga bangare dinka kayan sawa.

TRT Afrika