Alexandra Manyika da Noah Jotum sun kuduri aniyar canja yadda ake kallon masu talla a tituna. Hoto: TRT Afrika    

Daga Ronald Sonyo

Alexandra Manyika da Noah Jotum suna cikin dubban matasan da suke talla a titunan Babban Birnin Tanzania, Dodoma, sai dai su sun zabi wata hanyar zama daban a cikin abokanan kasuwancinsu.

A kasar da matasanta ke fama da matsanancin rashin aikin yi, sai matasan suka zabi fara sayar da turare cikin shiga ta ’yan gayu.

Da sannu sai suka fara zama fitattu, inda mutanen kasar suka fara gane su cikin sauki, har suke kiran su da sunaye daban-daban. Wasu na kiransu suke yi da mawakili-wanda ke nufin lauyoyi a harshen Swahili.

Yadda suka fara?

Abotarsu ta fara ne tun suna kwaleji, lokacin da Alex ke karatun zama malami, shi kuma Noah ke karatun zama nas.

Bayan sun kammala karatu, da kuma yadda suka dade ba su samu aiki ba, sai suka yanke shawarar fara sayar da turare a titunan Babban Birnin Kasar.

"Muna kaunar yin shiga mai kyau. Sai muka tambayi kanmu, me za mu iya yi da zai bambanta mu da sauran masu talla?” in ji Alex.

Alex ya ce yadda suke shiga mai kyau ya taimaka musu wajen jawo musu kwastomomi.

“Kwastomomi suna son sayan turarenmu ne saboda yadda muke shiga mai kyau,” in ji Noah.

Tsakanin kwalliya da tara kudi

Amma shin yaya suke iya cigaba da sayan kayayyakin nan da suke caba kwalliya haka da ribar da suke samu daga talla?

Noah ya ce yawancin kayayyakinsu gwanjo ne da suke saya a tsakanin $50 zuwa $100.

Alexandra Manyika da Noah Jotum sun fara abota ne a jami’a. HOTO: TRT Afrika

“Mun dauki tallar nan da muke yi da muhimmanci. Ta dalilin sayar da turare, yanzu mun samu jari, har mun fara fadada kasuwancinmu zuwa wasu harkokin daban," in ji Alex.

Da aka tambaye su kwana suke yi kafin su maimaita kaya, sai dukansu suka kwashe da dariya, kafin Alex ya ce: " Yakan kai wata daya haka, amma a wasu lokutan, mukan maimaita wadanda suka fi mana kyau akalla sau biyu a mako."

Alex da Noah sun zama fitattun a birnin Dodoma kasancewar idan dai kana yawo, to akwai yiwuwar za ka iya haduwa da su watarana a ko ina, a kowane lokaci.

Amma wuraren da suka fi tsayawa ko zuwa akwai kasuwannci, ofisoshi da wuraren shakatawa da na taron mutane, inda suke tallata kayansu ga kwastomomi.

“Akwai damarmaki da dama. Abu mai muhimmanci shi ne ka yi yunkurin wani abu. Ba dole sai mai ilimi ba. Kawai dai ya kamata iliminka ya taimaka maka ne wajen inganta duk abin da kake yi,” in ji Noah.

“Muna haduwa da sama da mutum 500 a kullum, kuma kowa da irin tunaninsa. A duk lokacin da muka hadu da wani kalubale, mukan tattauna shi a hanyarmu ta komawa gida da yamma. A nan ne muke tattauna batutuwa, mu shawarta yadda za mu fuskance su,” in ji Noah.

Daga kammala karatun koyarwa da na nas zuwa tallar turare a tituna, Alex da Noah sun zama ababen kwatance a kasar Tanzania, inda suke yin wani abu daban da abin da suka karanta a makaranta.

Burinsu shi ne su inganta kasuwancinsu, sannan su taimaki al’umma.

“Muna so mu taimaki al’ummarmu. Amma sai idan mun samu damar fadada kasuwancinmu, nan ne za mu samar da aikin yi ga wasu,” in ji Alex.

Fatuma Omary, daya ce daga cikin mutanen Dodana da ta dade tana sayan turare a wajensu. Fatuma ta ce tana jin dadin kasuwanci da matasan, inda ta kara da cewa yanayin shigarsu ce ta jawo hankalinta zuwa gare su.

“Turaren da suke sayarwa masu kyau ne, domin suna da kamshi mai kyau, amma abin da na fi so a game da su shi ne yadda suke da tsafta idan aka kwatanta su da sauran,” in ji Fatuma lokacin da take bayyana dalilinta na zaben turarensu.

“Wani lokacin, nakan kira su in ce su kawo min turare har gida ko wajen aiki,” in ji ta.

TRT World