Kungiyar Shosho Jikinge tana taimaka wa tsofaffin mata hanyar koyon dabarun yaki. Hoto / TRT Afrika  

Daga Job Samwel

A sakamakon gajiyar da suka yi na kasancewa cikin wadanda masu aikata laifuka ke kai musu hari a wuri mafi hadari a Nairobi babban birnin kasar Kenya, ya sa wasu tsofaffin mata daukar darasin koyon wasan dabarun nuna jarumtaka don kare kawunansu daga mahara.

Yankin Korogocho na daya daga cikin matsugunan birnin Nairobi da babu ci gaba inda ake yawan samun rahotannin fashi da kai hare-hare.

"Mun kafa wannan kungiya ce a shekarar 2007 lokacin da muka fahimci cewa masu fyade da barayi na yawan kai wa tsofaffi mata hari." a cewar shugabar kungiyar Shosho Jikinge Beatrice Nyariara .

''Mafi karancin shekaru a cikin kungiyar ita ce mai shekara 60 a duniya yayin da babbar cikinmu ita ce mai shekara 94.'' in ji shugabar

Kocin yawon bude ido

Dabarar harbi da naushi ta hanyar tsira ko ceton kai ta samo asali ne a lokacin da wani dan yawon bude ido ya kawo ziyara yankin, inda ya ji halin da tsofaffi mata da maza ke ciki a yankin.

Ya sha alwashin horas da su dabarun kare kai da wayar da kan su a halin da ake ciki tare da taimaka musu fatattakar maharan.

Korogocho yana daga cikin wurare mafi girma da babu ci gaba a Nairobi, Hoto / Reuters

“Ya ce mana mu kafa kungiya, sai ya gabatar da mu ga matarsa wadda ta kware a wasan nuna jarumtaka bayan wasu kwanaki, ta ce mana ana kiran wasan da Karate, ta horar da mu tsawon watanni shida."in ji Nyariara.

Ta kara da cewa ''a makonni biyu na farko mun ji zafi sosai saboda motsa jiki da muka yi na atisayen. Jikinmu duk ya tsufa, saura kadan mu hakura da wasan.

Suna kiran kungiyarsu da Shosho Jikinge - wasu kalmomi da aka hada daga harshen yaren Kikuyu da Swahili da ke nufin 'kaka ki kare kanka'.

Atisaye na koyon Naushi

Jakar naushi ta taimaka musu wajen iya kai bugu yayin da suke yin atisaye kan yadda za su kai wa mahara naushi sannan su yi kururuwar neman taimako.

Mai horarswar ta koya musu yadda za su kai hari kan kasan kugu da ta tsakanin kafafu, ko ta kan hanci yayin da za su yi kururuwa don neman taimako.

Kazalika, horon yana mayar da hankali ne wajen gano sassan jikin da za a kai wa hari domin ji wa maharan ciwo mafi tsanani.

Tsofaffin matan suna wasan nuna jarumtaka. Hoto / TRT Afrika

Taron horon ya hada har da koyon yadda ake kururuwa don neman taimako da gudu daga wurin da aka kai hari.

“Muna samun horo na sa’o’i biyu a duk rana, sau hudu ko biyar a mako. Bayan haka, kowannenmu tana zuwa neman abinci na yau da kullun don tallafawa iyalanta. Idan akwai wanda shi ma yake son ya taimaka mana ta kowace hanya za mu yi maraba da hakan,” in ji Grace Ng'ang'a.

Nan da nan labari game da horon da kungiyar ke samu ya bazu a yankin da babu wani ci gaba a cikinsa kuma tuni hakan ya sanya tsoro a zukatan masu son kai hari sannan tun daga lokacin aka samu sassauci a matsalar fyade da ake yi wa tsofaffi.

Saukin matsaloli

“Wannan kungiya ta taimaka mana matuka. Atisayen da muke yi, ya kara man karfin gwiwa. Sata da fyade ga tsofaffi sun ragu.

"Mun kuma samu karfin yin noma da kuma shuka kayayyakin lambu duk da shekarunmu. Za mu koyawa jikokinmu kare kansu." a cewar Rose Adhiambo

Kungiyar ta soma sana'a hada jakunkunan hannu da sauran kayayyakin ado na mata. Hoto/ TRT Afirka

Tuni dai kungiyar ta raba ayyukanta da suka hada da samun tsarin yin tanadi wanda zai ba su damar fara sana’ar hada jakunkuna da kayan adon mata na hannu.

“Kowane mako, muna ba da shilin na Kenya 20 ($0.13). Wannan kudin yanzu ya ba mu damar hada wadannan jakunkuna.

Akalla muna samun wani abu ko da kadan ne. Haka kuma idan dayanmu ta yi rashin lafiya ko kuma ta rasu, muna ba da wani abu kadan daga abin da muka tara don taimaka wa iyalanta.” In ji Nyariara.

TRT Afrika