Zipporah Ongera ta ce ta sha fama da tsangwama saboda nakasarta. Hoto: Reuters      

Daga Kevin Phillips Momanyi

Zipporah Ongera mai shekara 22 ba ta san dadin amfani da hannayenta biyu ba domin da hannu daya aka haife ta, amma hakan bai hana ta jin dadin rayuwa ba kamar kowa.

Daga cikin abubuwan ban sha’awa a game da ita, akwai girki da kafa - musamman girka abincin da ake kira ugali da ake yi da masara a kasar Kenya da wasu kasashen Gabashin Afrika.

“Duk da cewa na shiga damuwa da farko, sai mahaifiyata ta nuna min in cire damuwar. Ta koya min cewa in dauki rayuwata yadda ta zo min,” in ji ta a lokacin da take bayyana wa TRT Afrika yanayin tasowarta.

Ta ce ita kanta mahaifiyarta din ta sha fama da tsangwama saboda ta haifi nakasassshiya, inda wasu suke ganin hakan a matsayin aibu.

Tsangwamar ta kara kamari ga Zipporah da mahaifiyarta ne a lokacin da mahaifinta ya tafi ya bar su.

“Da aka haife ni, sai aka bayyana wa mahaifiyata cewa ni annoba ce ga danginmu da ma garin baki daya. Wai ba su taba ganin inda aka haifa mutum da hannu daya ba. Ina da kimanin shekara bakwai sai mahaifina ya watsar da mu. Mahaifiya ta ce ta cigaba da wahalar dawainiya da ni,” in ji ta.

Samun karfin gwiwar cigaba da rayuwa

Da take bayyana mahaifyarta a matsayin babbar mai karfafa mata gwiwa, Zipporah ta bayyana yadda ta koyi amfani da kafarta wajen girki da sauran aikace-aikacen gida.

“Zan iya yin komai; zan iya yin girki, wanki da shara. A hankali na koya kusan yadda zan rika gudanar da komai. Ba na jin wani bambancin da duk sauran mutane.”

Zipporah Ongera ta kammala karatunta na digiri, sannan ta sha bayyana wa a lokutan baya yadda ta sha fama da tsangwama.

Ta kammala digirinta ne a bangaren Kimiyyar Kwamfuta. Sai dai duk da hakan, tana fuskanci kalubale wajen samun aiki, kasancewar masu daukar aikin suna ganin ba za ta iya ba.

“Nakan tuna lokacin da wani mai mana gwajin daukar aiki ya tambaye ni ko zan iya rubutu da kwamfuta. Sai na shiga mamakin ta yaya zai tambaye ni ko na iya rubutu da kwamfuta bayan na kammala digiri a Kimiyyar Kwamfuta?

"A karshe dai duk da na yi rubutun, ban samu aikin ba. Na shiga damuwa sosai, amma hakan bai sanyaya min gwiwa ba. Sai na cigaba da rayuwata kawai.”

‘Babban burina in dafa wa mahaifina abinci’

Da wahala ka ga Zipporah a cikin damuwa ko rashin karsashi. A kowane lokaci ka same ta, za ka ganta a cikin fara’a ne da natsuwa da yarda da kanta.

Akwai abubuwan da take da sha’awa cimmawa a rayuwa. Ta sha fama da kalubale, amma har yanzu ko a jikinta.

“Dafa wa mahaifina abinci ne babban burina. Na dade ina fatar samun damar nuna masa yadda na girma, kuma nake gudanar da rayuwata. Ko kadan ban tsane shi ba, ina matukar son shi. Allah ne Ya zabe shi ya zama mahafina. Ina da tabbacin watarana zai ci abincin da na dafa.”

Zipporah Ongera ta ce kullum burinta nuna cewa nakasa bai hana komai.  

Zipporah ta bayyana wa duniya yadda take rayuwa cikin walwala. Ta buga riguna da take raba wa ga nakasassu. Ta ce burinta ta karfafa gwiwar mutane.

Ta sanya wa rigunan take, “FLAWSOME.’ Wanda ya kunshi kalmomin flaws wato kalubane da awesome, anda ke nufin abin sha’awa.

“Mahaifiyata ce mafi mutum muhimmanci a rayuwata. Ta karfafa min gwiwar yarda da kaddara. Ba don ita ba, ta duniyar ba za ta min dadi ba.”

Zipporah mace ce da ba za ta taba rumgume hannayenta ta yi shiru ba. Ta san tana da iyaka, amma ba ta taba daina yunkurin tsallake iyakokin ba.

“A tunanina kowane dan'adam yana da tasa matsalar, ko dai a zahiri ko a badini. Kawai abin da ake bukata shi ne a cigaba da fafutika.”

TRT Afrika