Daga Charles Mgbolu
Ƙayatattun hotunan buɗe taron gasar wasannin sojojin Afirka (AMGA) na 2024 a Abuja, Nijeriya a ranar Labara 20 ga watan Nuwamba ya nuna ƙyawawan launuka da al'adu da kuma haɗin kai.
Taron wadda aka yi masa take da "Haɓaka haɗin gwiwar soji ta hanyar wasanni", ya mayar da hankali ne wajen inganta haɗin kai da zumunci da haɗin gwiwar harkokin soji a tsakanin ƙasashen Afirka.
Kazalika wannan ne karo na biyu da aka soma gudanar da gasar wasannin kuma zai kai har zuwa ranar 30 ga Nuwamba, 2024 kafin a kammala shi.
Bikin buɗe taron ya samu halartar mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, inda aka gabatar da fareti kala-kala, da wasannin al'adu, da kuma kaddamar da taron AMGA 2024 ta hanyar kunna wuta.
Shettima ya yi kira ga sojojin da ke faɗin Afirka da su haɗa kai wajen magance matsalar rashin tsaro da sauran abubuwan da ke barazana ga haɗin kai da zaman lafiyar nahiyar.
''Wadannan wasanni alamu ne ga tarihi da kuma burinmu da muka sa a gaba. Suna ƙarfafa dangantakarmu a matsayinmu na ’yan Afirka kuma suna ba da gudummawa wajen inganta tsaro, da al’adu, da kuma haɗin kan Afirka,” a cewar jawabin da Shettima ya gabatar.
Gasar sojojin ta ƙunshi wasanni daban-daban, akwai na motsa jiki, da na ƙwallon ƙafa, da ƙwallon kwando, da wasan ninkaya, da harbi, da dambe, da kokawa, da kuma wasannin tsere da dai sauransu.
Masu shirya gasar sun bayyana cewa, baya ga ƙarfafa haɗin kai da dangantaka soji tsakanin ƙasashen Afirka, wasannin suna ƙara haɓaka yanayin wasannin motsa jiki.
Kazalika wata dama ce ga hazikan ‘yan wasa a cikin sojoji su baje basirarsu wajen fafatawa don kaiwa zuwa ga kololuwar mataki.
Kimanin ƙasashen Afirka 30 ne za su halarci gasar wasanni sojoji ta Afirka a shekarar 2024 tare da samun lambobin yabo.