Kenya ta shahara da namun daji. Hoto: Reuters

A wani kungurmin daji da ke wani wadi a Kenya, wani likitan dabbobi ne ke lallaɓawa kafin harba allurar bacci ga wani rakumin dawa wanda ya fadi kasa a hankali, daga nan aka daure idanuwansa da kafafunsa.

Wannan mataki na farko na aiki mai hatsari da Hukumar Kula da Namun Daji ta Kenya ta yi na kwashe dabbobin da ke fuskantar barazanar karewa zuwa wani yanki da za a dinga ba su kariya da ke da nisan kilomita 140 daga wajen da suke.

An ajiye rakumin dawar da aka sumar a wani gidan gona na Sergoit tare da wasu su bakwai don zama na tsawon kwanaki 10 saboda su saba da wajen, kafin a kai su sabon wajen zaman su.

Ana dauke nau'in rakumin dawa na Rothschild, jinsi na musamman, zuwa Wajen Adana Dabbobin Dawa na Ruko da ke lardin baringo a wani bangare na rage rikici tsakanin al'ummu.

A yayin da kasar ta Gabashin Afirka ta suna da rayuwar namun daji, yankunan arewacinta irin su Baringo suka fi yin shuhura da labaran 'yan bindiga, da rikici tsakanin kabilu.

Al'ummun Pokot da Ilchamus da ke rikici da juna a Baringo, sun dade ba sa ga maciji da juna, a wasu lokuta rikicin nasu na kaiwa ga amfani da makamai.

Satar dabbobi

A tsakiyar shekarun 2000, dattawan Pokot da Ilchamus sun dauki matakai da hannayensu, sun kaddamar da wani shiri na sauya matsugunin rakuman dawa na Rothschild ko Nubian zuwa Ruko waje mai nisan kilomit 280 arewa da babban birnin Nairibi.

Manufofin guda biyu ne: sake dawo da dabbobin da ake wa barazana zuwa yankin da suka kaurace wa a baya, d akuma dawo da zaman lafiya ga jama'ar yankin su biyu.

Dattawan na sa ran cewar rakuman dawan mafiya tsayi a tsakanin dabbobi a duniya za su kawo kudi da 'yan yawon bude ido, tare da samar da ayyukan yi ga matasa a yankin - kamar a wani waje a Kenya - ana gwagwarmaya wajen samun ayyuka.

Yawan rakuman dawa na ci gaba da ragu wa a duniya, kamm=ar yadda masu bayar da kariya ga dabbobin dawa ke fada. Hoto:Reuters

Kuma, wata mai shekara 34 da ke kula da namun daji Rebby Sebei, ta ce kamar wannan matakin ya yi kyau sosai.

"Shekaru 20 da suka gabata, Pokot da Ilchamus sun yi rikice-rikice saboda satar dabbobi, inda aka dinga samun rasa rayuka, dabbobi tare da tirsasawa jama'a su bar yankunansu."

"Wannan waje ya zama kamar kufai, wajen da muke tsaye a nan filin daga ne na 'yan bindiga."

Amma a yanzu, wadannan halittu na taimaka wa wajen tabbatar da akwai zaman lafiya a yankin.

Zuwan sabbin rakuman dawa

A 'yan shekarun nan an ga raguwa adadin rakuman dawa sosai a Kenya, sakamakon farauta da yadda dan adam ke kara kusantar yankunansu.

A yayinda rakuman dawan Sergoit suka daidaita a bayan akori kura, sai aka dinga kai su dazuka a hankali, mutanen Pokot da Ilchamus sun gudanar da bikinin tarbar dabbobin.

Bayan awanni 16, bayan barin su Sergoit, saboda yadda suka haura gadoji marasa kyau da kuma gajerun wayoyin lantarki, a karshe dai rakuman dawan sun iso gida.

Kafin a saki rakuman dawan a dajin Ruko, za a ajje na wani dan lokaci don su saba da wajen, yankin da a yanzu yake da rakuman dawa 20, dukkan su jinsin Rothschild da Masai.

A lokacin da mutane suke waka da rawa don murnar zuwa sabbin rakuman dawa, Douglas Longomo, manomi dan shekara 27 ya ce ya yi amannar al'ummun sun sauya halayensu.

"An dauki lokaci na fahimtar cewa tsare dabbobin da ba su kariya na da muhimmanci ga hadin kan mutane," in ji Longoma.

'Ana buƙatar ƙarin raƙuman dawa'

Ya kara da cewa da yawa ba sa iya ganin matakin kawo karshen arangamar da ta illata wadin na tsawon shekaru.

"A yanzu muna ganin yadda muke ganin muna rayuwa tare, z amu iya zuwa ko'ina ba tare da tsangwama ko jin tsoro ba."

James Parkitore daga Ilchamus ya sake jaddada kalaman Longomo.

Ya ce "Ina tunanin rikicin ya zo karshe yanzu saboda muna mu'amala tare da juna."

"Ina fata wadannan rakuman na dawa za samar da ayyukan yi da dama ga jama'ar yankin," in ji Parkitore, ra'ayin da Longomo ya bayyana.

Sebel ta kara da kira da a kula sosai, sai dai kuma, cewar a yayinda daduwar 'yan yawon bude ido ke taimaka wa, har yanzu akwai 'yar takaddama a tsakanin al'ummun biyu.

Amma ta ce "akwai zaman lafiya, kuma muna bukatar mu kawo karin rakuman dawa da yawa zuwa nan."

TRT Afrika