Yadda rashin jituwar mutane da namun dajin Nairobi ke barazana ga adana dabbobin

Yadda rashin jituwar mutane da namun dajin Nairobi ke barazana ga adana dabbobin

Rashin jituwar mutane da dabbobin dajin na matukar barazana ga yunkurin Adana dabbobin a yankin Afirka ta Gabas.
Kasashen Afirka ta Gabas sun fi fuskantar matsalolin rashin jituwa tsakanin mutane da dabbobin dajin. Hoto / Reuters / Photo: AP

Daga Edward Qorro

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda yake nuna wani zaki yana yawo shi kadai a kusa da gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi na kasar Kenya, ya kara bayyana irin yadda rashin jituwa tsakanin mutane da dabbobin dajin ke kara yawa.

Faifan bidiyo wanda kyamarar gida ta dauko ya nuna lokacin da zakin ya tsallake katangar gidan wasu mutane, sannan ya yi awon gaba da karen gidan da sanyin safiya.

Irin wannan yanayi na yadda namun dajin suke kai farmaki a garuruwan mutane ba sabon abu ba ne a yankin Afirka ta Gabas, inda mayar da martani da mutanen suke yi, ya yi sanadiyar kashe dabbobin da dama.

Dabbobin da suka fi fuskantar wannan matsalar su ne giwa da zaki da kada. Yawancin matsalar suna ta'allaka ne da mamaye muhallan dabbobin da mutane suke yi.

Matakan da ake dauka ba sa aiki

Masana a bangaren namun dajin sun yi gargadin cewa yawanci matakan da ake dauka na wucin gadi ne, kuma ba za su iya magance matsalar ba

Masana a bangaren namun dajin sun yi gargadin cewa yawanci matakan da ake dauka na wucin gadi ne, kuma ba za su iya magance matsalar ba.

"Muna bukatar a dauki matakai masu kyau da tsari ne kamar killace makiyayan giwaye da dabbaka tsarin kasa da sufiyo," inji Farfesa Noah Sitati na Asusun World Wide Fund for Nature (WWF) a tattaunawarsa da TRT Afrika.

A cewar masanin, giwa suna son kai farmaki a gonakin masara ne saboda sinadaran da masara da shi mai gina jiki.

"Wannan ba zai yiwu ba idan an killace dabbobin," inji shi.

Sitati ya bayyana cewa kasar Tanzania ta yi dokoki a karkashin shirin National Corridor Action Plan, wanda yake kula tare da killace dabbobin daji.

"Har yanzu rashin jituwar mutane da dabbobin daji babbar matsala ce, amma ina tunanin samar da wannan tsarin zai rage aukuwar lamarin," inji shi.

Tsara kasa da katange filaye

Duk da kasar Tanzania ta fitar da wadannan dokoki, kasashen da suke makwabtaka da ita a Gabashin Afirka din ba su yi irin wannan dokar ba.

Tanzania ta samu nasara ta hanyar tsara kasarta da kuma gina takanga domin raba kasar, sannan kuma an yi yarjejeniyar hana shiga yankin da aka ware wa dabbobin a karkashin Cibiyar Binciken Dabbobin Daji wato Tanzania Wildlife Research Institute (TAWIRI).

A cewar masanin, Tanzania na samun nasara sosai ta hanyar fitar da tsare-tsarenta a kan alaka tsakanin na'ukan dabbobin daji da muhallansu da kuma kaurarsu domin sauya muhalli.

Sai dai ya ce akwai bukatar a kara nazarin dokokin domin su kara bayyana zahirin yadda abubuwa suke a yanzu.

"Haka kuma akwai bukatar a gina katanga a wasu wuraren," in ji shi.

Duk da kasar Kenya ta gina katanga a zagaye da wasu daga cikin gandun dajinta, Tanzania ba ta yi haka ba.

Kiyasi na nuna cewa akwai muhallan dabbobin daji kusan 62 da burtalinsu a Tanzania.

Tsarin da ba ya aiki

Lokacin da wasu na'ukan giwaye suka fara cika Gandun Dajin Shimba Hills National Reserve da ke Kenya, sai da hukumomi a kasar suka kwashe su, suna kai su Gandun Dajin Tsavo East National Park.

An kwashe akalla giwa 150 aka sauya musu matsuguni a lokacin.

"An kashe makudan kudade a lokacin domin sai da aka yi amfani da helikwafta, amma duk da haka ba a samu yadda ake so ba domin wasu giwayen sun bace, wasu kuma suka samu rauni," inji shi.

Haka ma an yi irin hakan a Gandun Dajin Maasai Mara Game Reserve.

Barazana ga rayuwa

Kada da dorinar ruwa ne dabbobin da suka fi kashe mutane a Afirka, kamar yadda wani masani John Noronha na Kungiyar Tuhifadhi mali asili da ke karkashin USSAID ya bayyana, inda ya ce dabbobin guda biyu ne suka fi fuskantar rikici da mutane a Tanzania.

Sun yi sanadiyar jawo raunuka akalla guda 642.

"Rayuwa tare a tsakanin mutane da dabbobin daji yana da matukar muhimmanci domin tabbatar da adana dabbobin a Tanzania. Sai dai tafiyar da rayuwarsu a tare yana matukar haifar da matsaloli masu yawa," inji shi.

Wani binciken da ake yi na National Human - Wildlife Conflict Management Strategy (2020 - 2024), ya bayyana rashin tsarin kasa da sufiyo a matsayin babban makasudin matsalar.

Binciken ya kara da cewa a tarihi, ba a cika ba tsarin kasa muhimmanci ba, ko kuma ba a cika amfani da shi ba a inda akwai, sannan ko ana amfani da shi, ba a lura da yiwuwar rikici tsakanin mutane da dabbobin.

A gomman shekarun da suka gabata, Tanzania ta fuskanci rashin akalla daya bisa ukun dazukanta, wanda hakan ke kara yawaitar dabbobin fa suke fuskantar barazana.

TRT Afrika