Daga Pauline Odhiambo
A matsayintsa na mai zane-zane wanda ke da burin faɗaɗa hanyar isar da saƙo, Olayinka Stephen Aragbada na yawan fito da abubuwan da ke cikin zukatan ɗan adam.
Ayyukan zane-zane na 'yan Nijeriya Najeriya suna da inganci, da ke nuna abubuwan da ake zanawa masu kauri, waɗanda ke bayar da labaransu.
Shawara ko kuma tunani kan labarin da za a yi ya kasance wani abu ne mai wahala, sai da Olayinka ba ya taɓa manta da kimiyyar kwatanta abubuwan da suka dace da zanen.
"Irin zanen da nake yi yana da alaƙa da bil'adama, inda yake fitar da alaƙa tsakanin ɗan adam tsakanin ɗan adam da kuma abin da ke cikin zukata," kamar yadda mai zanen na zamani ya shaida wa TRT Afrika.
Zane-zanen Olayinka na "Sirri" ya fito ne a cikin wani nunin da ya shahara a duniya a intanet. Daga cikin masu sha'awar aikin nasa akwai mawakiyar Amurka Alicia Keys, wacce ta bayyana aikinsa a matsayin "kyakkyawa".
Bambancin wakilcinsa na "baƙar fata" a Afirka ta zamani wani dalili ne da ya sa waɗannan zane-zane ke daɗaɗa wa masu fasahar fasaha da kuma ƴan ƙasa baki ɗaya.
Olayinka ya ce "Ina ganin yana da sauƙi mutane su san aikina saboda na sanya abubuwan da suka faru a baya, na yanzu, da kuma na gaba cikin aikina. Na yi imani cewa hakan ne ya sa ya fi ban sha'awa da kuma jan hankali ga masu kallo," in ji Olayinka.
An baje kolin zane-zanen Olayinka a wurare da dama a Nijeriya da kasashen ketare, inda aka sayar da yawancin zanen nasa kan dubban daloli a kasuwar fasaha ta duniya.
Fasihin yana amfani da gawayi da fenti na acrylic a matsayin matakan farko, kuma yana amfani da wukar mahauta don bai wa aikinsa kyakkyawan tsari da tasiri mai ban mamaki.
Olayinka, wanda ya zama kwararre a shekarar 2019, ya nuna sha’awarsa ta fasaha tun lokacin yarinta.
Ya yi karatu a Polytechnic ta Ibadan a Najeriya, daga baya kuma a Jami'ar Obafemi Awalolo da ke jihar Osun, inda ya yi kwas a fannin fasaha.
Kamar yawancin masu fasaha a Afirka, Olayinka yana jin takaicin tsadar kayan fenti a nahiyar. Amma samun larbuwa da yake yi tana faranta masa rai.
"Ina godiya da damar da aka ba ni na tallata fasahata a shafukan sada zumunta, wanda ya ba ni damar yin hulɗa da masu sayen aikina a fadin duniya," in ji shi.
Shawarwarinsa ga masu son yin zane-zane shi ne su kasance suna zane na asali da kuma shigar da kowane fanni ciki.
"Ka kasance masu tawali'u don haɗawa da ƙwararrun masu fasaha kuma ka koya daga wurinsu ba tare da lalata gaskiyarka ba," in ji shi. "Har ila yau, ku amince da tsari kuma ku yi haƙuri da juriya a aikinku."