Daga Firmain Eric Mbadinga
Kunkuru suna cikin halittun da suke fuskantar barazana a duniya. Domin tseratar da su, tare da tabbatar da sun cigaba da wanzuwa, halittun na ruwa suna samun kula ta musamman a wani waje da ake kira Cibiyar Taimakon Farko na Kunkurun Ruwa wato First Aid Sea Turtle Centre da ke birnin Sfax na Tunisia
Daga cikin na’ukan kunkurun da suka samu kula a cibiyar, akwai kunkuru mai suna Rose, mai shekara 20.
An kama Rose ne da ragar kamun kifi. Tuni aka mayar da Rose din cikin teku a Gabashin kasar Tunisia domin sake sabuwar rayuwa.
Bayan an yi musu magunguna a cibiyar, idan suka watstsake, su kai komawa cikin teku, ana mayar da su ne tare da wata na’urar da za a rika bibiyarsu, tare da kare su daga cutarwa ko da kuwa sun yi nisan kiwo.
Cibiyar tana karkashin kulawar shirin Med Life Turtles project. Sai dai jami’an cibiyar sun bayyana cewa bayan an mayar da kunkurun teku, suna cigaba da fuskantar barazana fadawa komar masunta, da gurbacewar teku da sauyin yanayi.
Bayan jinya da ake musu, kamar Rose, kunkurun sukan dauki wata uku ko sama da haka a karkashin kulawar cibiyar, wadda take amfani da na’urar fasahar beacon domin sanin duk inda suke bayan sun koma cikin teku.
Haka kuma shirin yana taimakawa wajen wayar da kan mutanen yankin tekun Gabes a Gabashin Tunisia, inda mafi yawan mutanen yankin suka fi ta’allaka da kamun kifi.
Hamadi Dahech masunci ne mai shekara 29 da ya ceci Rose a Satumban 2023.
“A da, da ba mu da masani, mun sun kasance suna cin kunkuru, sannan ana amfani da kunkurun wajen tsafi da magani. Amma yanzu, bayan wayar mana kai da aka yi, kunkurun sun samu damar cigaba da rayuwarsu,” inji Dahech a lokacin da ake mayar da Rose cikin teku.
Kunkuru kan kai girman tsakanin 90 cm zuwa 213 cm, da kuma nauyin tsakanin kilogram 135 zuwa 535.
Akalla na’uin kunkurun ruwa kamar Rose guda 10,000 masunta suke kamawa a yankin tekun Gabes.
Wannan adadin ke nuna cewa lallai akwai dimbin halittar ruwan a yankin me masana’antu masu yawa da fitar da sinadarai cikin teku-bayan barazanar da suke fuskanta.
Karlia Mpendaga daga kasar Congo, ta ce tana sha’awar naman kunkuru, amma kuma tana so halittar ta cigaba da wanzuwa.
“Duk da cewa ina sha’awar naman kunkuru, ina da tunanin akwai bukatar a rika cin naman kunkurun da lura domin kada a karar da su. Na yi amannar cewa shirin tabbatar da adanawa tare da inganta su abu ne mai kyau domin kunkuru na yin kwai sau biyu ko uku a shekara. Kuma duk guda daya na yin kwai ya kai 15,” inji ta.
“Ke nan idan ana cin kunkurun sosai, nau’ukan halittar za su fasukanci barazanar bacewa baki daya,” in ji ta.
Tun daga lokacin da aka assasa cibiyar a shekarar 2021, akalla kunkuru guda 80 ne aka yi wa jinya, sannan aka mayar da su cikin teku, kamar yadda shugaban cibiyar, Imed Jribi ya bayyana wa manema labarai.
Bayan harkokin masunta da gurbacewar ruwa, wata babbar bazarana da kunkurun suke fuskanta shi ne dumamar yanayi kamar yadda masana suka bayyana.