Fitattu a masana'antar shirya fina-finai ta duniya suna halartar taron bikin fina-finai na duniya karo na 20 a Maroko, wato Marrakech International Film Festival, wanda ke sake gabatar da fina-finan Afirka da nuna fasaha mai karfi a fagen fina-finai na duniya.
Tuni manyan ƴan fim na masana'antar Hollywood ta Amurka da suka taɓa lashe lambobin yabo kamar su Willem Dafoe da ya taɓa lashe lambar yabo ta Golden Globe da Tilda Swinton da ta ci Oscar da Mads Mikkelsen da ya ci lambar yabo ta Cannes Film Festival, suka halarci bikin buɗe taron na Marrakech, wanda ake gudanar da shi daga ranar 24 ga Nuwamba zuwa 2 ga Disamba.
A wannan shekarar, bikin fina-finai na Marrakech na kasa da kasa zai gabatar da fina-finai daga ko ina a fadin duniya, inda aka tantance fina-finai 75 a fannoni daban-daban daga kasashe 36.
Daya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a taron yana yiwuwa ya kasance a cikin rukunin gasar fina-finai na hukuma, wato Official Film Competition, wanda shi ne zaɓi na fina-finai na farko da na biyu daga sabbin jarumai masu hazaƙa a duniyar fina-finai.
Daga cikin fina-finai 14 da suka shiga gasar, biyar na yankin Gabas ta Tsakiya ne da Afirka da Mongolia da Turkiyya da kuma Amurka.
Masu shirya fina-finai sun ce ’yan fim 14 da aka zabo domin gasar a hukumance sun samar da wasu fina-finan masu darussa da kuma ban mamaki ... da ke zayyana hoton matasa masu neman ma’ana da ‘yanci.
Masu shirya fina-finai sun kuma ƙara ƙaimi wajen tunkarar matasa masu kallon fina-finai a cikin shirin ''masu kallon fina-finai na nan gaba, shirin Cinema for Young Audiences' '' wanda ya ƙunshi nunin faifai 13 da aka sadaukar domin matasa masu shekaru 4 zuwa 18.
Shi (bikin fina-finai) na ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi sani na duniya da ake gudanarwa a ƙasar bayan girgizar ƙasa da ta afka wa al'ummomin tsaunukan da ke kewaye da Marrakech a watan Satumba.
A daren da aka bude taron, masu shirya gasar sun nuna girmamawa ga wadanda girgizar kasar ta Maroko ta shafa.
“A makonnin da suka gabaci bikin, ba mu da tabbacin ko za mu iya kasancewa a nan. Duniyar da muke zaune a ciki ta wargaje,” in ji Ba’amurkiyar Jarumar Jessica Chastain, wacce ke zama shugabar alkalan bikin, a wani jawabi da ta yi a daren bude bikin.
Ana kallon taron a matsayin wata alama ta juriya.
A yayin bikin rufewa da bayar da kyaututtuka, za a bayar da kyautuka biyar masu daraja, inda za a ba da kyautar dala 25,000 ga darakta da furodusan da suka yi nasara a matsayin babbar lambar yabo ta bikin.
Sauran kyaututtukan su ne Gwarzon Jarumi da Jaruma.
An kirkiro bikin fina-finai na kasa da kasa a shekara ta 2001 da Sarki Mohammed VI ya kafa domin bunkasa fasahar fina-finai da masana'antar fina-finai ta kasar Maroko, kuma ya kasance wurin bayyana ra'ayoyin jama'a da gano abubuwa, wanda ya samar da gagarumin fitowar fina-finan arewacin Afirka a fagen duniya.