Mawakiyar Afirka ta Kudu Tyla ta doke mawaka daga Nijeriya. Hoto/Getty Images

Daga Charles Mgbolu

Har yanzu ana ci gaba da tayar da jijiyar wuya a shafukan sada zumunta kan Gasar Grammy karo na 66 da aka kammala, inda aka samu mayar da martani mabambanta kan zabar wadanda ya yi nasara a bangarori daban-daban.

Gasar ta Grammy, da aka gudanar a ranar 5 ga Fabrairu, na da mabiya da magoya baya da yawa a nahiyar Afirka da kawunansu suka rarrabu bayan sanarwar da aka fitar kan cewa mawakiyar Afirka ta Kudu Tyla ce ta lashe Kambin Waka Mafi Kyau.

Wakokin 'Unavailable' ta Davido, 'Amapiano' ta Asake da Olamide, 'Rush' ta Ayra Starr, da 'City Boy' ta Burna Boy suk ba su yi nasara ba a wannan bangare.

Nasarar Tyler ya bayar da dama ga mawakiya mafi karancin shekaru a Afirka ta lashe gasar Grammy tana da shekara 22.

Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kira Tyla bayan ta lashe kambin tare da taya ta murna.

Ramaphosa said. Ramaphosa ya ce "KIn sanya ni cikin farin ciki da alfahari, dukkan mu muna alfahari da ke. Abu ne mai kyau. Kin daukaka dukkan mu. Kin dora Afirka ta Kudu a kan taswira; mun sake hawa taswira."

Kamar yadda aka tsammata, an samu murna sosai a shafukan yanar gizo a tsakanin 'yan Afirka ta Kudu, amma magoya bayan mawaka a Nijeriya kuma sun soki sanarwar nasarar matashiyar.

Davido ya yi rashin nasara a bangarori uku a Grammy. Hoto Davido

Nan da nan Davido ya taya Tyla murna sabod anasarar da ta yi, amma bai kaucewa tattaunawar da ake ta yi a shafukan sada zumunta ba.

A sahar sada zumunta na Nijeriya an dinga yada #grammys, inda dubunnan mutane suka yi suka ga alkalan gasar kan me ya sa babu wani bangare da mawakin Nijeriya ya lashe a gasar.

Suna muhawarar cewa 'yan Nijeriya da aka nada don shiga gasar sun samu nasarar samun miliyoyin masu sauraro da saukar da wakokinsu.

'Yan Afirka ta Kudu kuma, sun dinga kare nasarar da Tyla ta samu, suna kiran ta da 'ta cancanta' kuma 'yan Nijeriya kawai bakincin faduwa ke damun su.

Mawakan kasa da kasa sun yi kira ga masu shirya Grammy, inda Jay Z ya soki masu shiryawa saboda gaza bayar da nasarar jerin wakoki mafi kyau ga mawkaiyar Amurka Beyonce.

Taylor Swift broke a record with her Grammy win by becoming the first performer to win Album of the Year four times in a row.

Jay Z, a yayin da yake karbar Kambin Tasirin Waka na Duniya a madadin mai nadar wakokin Amurka kuma dan wakar gambara Dr. Dre, ya bukaci Grammy da su dinga yin abin da ya kamata.

Shugaban Majalisar Dattawan Kamfanin 'Recordin Academy' Harvey Mason, ya bayyana cewa Academy din na zabar wanda ya yi nasarar gasar ne bayan jefa kuri'ar jama'a da ke sauraren mawakan.

Mason ya bayyana yadda ake lashe gasar Grammy. Hoto: Getty Images

"Mambobin alkalan Grammy sun saurara tare da yanke hukunci duba da ingancin waka - ba wai yawan sauraren ta ba, ba yawan sayen ta ba, ba yawan mabiyan wakar ba - haka ake yin nasara ko akasin haka a Grammy. Kwararrun mawaka ne ke zabar abokan sana'arsu."

'Yan Nijeriya da aka nada don shiga gasar sun sha naushi a wajen bikin, inda Davido da Burna Boy kawai suka fadi a bangaren lashe Waka Mafi Kyau a Duniya inda 'Feel' ta Bela Fleck, Edgar Meyer da Zakir Hussain, da ke fito da Rakesh Chaurasia a cikinta suka yi galaba a kan su.

A bangaren Rukunin Wakoki Mafi Kyau a Duniya, 'Timless' na Davido da 'I Told Them' na Burna Boy sun yi rashin nasara, inda 'The Moment' na Shakti ya yi nasara.

TRT Afrika