Daraktan shirya fina-finan Turkiyya Ceylan ya koma gasar Cannes da sabbin fina-finai

Daraktan shirya fina-finan Turkiyya Ceylan ya koma gasar Cannes da sabbin fina-finai

Sabon shirin fim din Nuri Bilge Ceylan na daga fina-finan da za su shiga gasar neman lashe kambin Palme d’Or.
Cannes na shirin bikin gasar fina-finai ta duniya karo na 74 da za a yi a birnin Cannes na Faransa / Hoto: Reuters

Daraktan shirya fina-finai na Turkiyya Nuri Bilge Ceylan ya sake dawo wa gasar Cannes ta fina-finai da sabon fim din da ya shirya mai suna ‘About Dry Grasses’ (Game da Busassun Ciyayi).

Sabon shirin Ceylan ya mayar da hankali kan labarin wani matashin malamin makaranta wanda ya so a tura shi birnin Istanbul na Turkiyya, bayan kammala koyarwar dole a wani karamin gari da ke gabashin kasar.

Darakta dan kasar Ingila Ken Loach da Wes Anderson na Amurka da Catherine Breillat ‘yar Faransa da Wim Wenders na Jamus da Kore-eda Hirokazu na Jamus da Aki Kaurismaki na Finland, na daga cikin daraktocin da finan-finansu suke takara a karo na 76 na gasar da za a gudanar a tsakanin 16 da 27 ga Mayu mai zuwa.

A shekarar 2014ne Ceylan ya lashe kambin Palme d’Or a Cannes. A 2009 ya zama mamba na kwamitin tantance fina-finai a Cannes.

Shugaban bikin Iris Knobloch ne ya karbi kambin a shekarar da ta gabata daga hannun Pierre Lescure da daraktan bikin Thierry Fremaux da aka gudanar a Paris.

A gefe guda kuma, tashar watsa labarai ta Turkiyya, TRT ta sanar da cewa akwai fina-finai uku da ta bayar da gudunmowar shirya su da za su shiga takarar a bikin na bana a Cannes.

Daga cikin su akwai shirin Darakta Ceylan na About Dry Grasses da Club Zero na ‘yar kasar Osriteliya Jessica Hausner, da na daraktar Italiya Alice Rohrwacher.

Jimillar fina-finai 19 ne za su fafata a gasar ta bana.

Ga jerin finan-finan:

Club Zero by Jessica Hausner

The Zone of Interest by Jonathan Glazer

Fallen Leaves by Aki Kaurismaki

Les Filles D’Olfa (Four Daughters) by Kaouther Ben Hania

Asteroid City by Wes Anderson

Anatomie D’une Chute by Justine Triet

Monster by Kore-eda Hirokazu

Il Sol Dell’Avvenire by Nanni Moretti

L’Ete Dernier by Catherine Breillat

About Dry Grasses by Nuri Bilge Ceylan

La Chimera by Alice Rohrwacher

The Passion of Dodin Bouffant by Tran Anh Hung

Rapito by Marco Bellocchio

May December by Todd Haynes

Jeunesse by Wang Bing

The Old Oak by Ken Loach

Banel e Adama by Ramata-Toulaye Sy

Perfect Days by Wim Wenders

Firebrand by Karim Ainouz.

AA