Bayan shafe kwanaki 11 da kashe sama da naira miliyan biyu, kwatankwacin dala 2,493, 'yar Nijeriya mai gyaran gashin kanti, Helen Williams ta kafa tarihin a kambun bajinta na duniya na Guinness World Record (GWR) ta hanyar hada gashin kanti mafi tsawo a duniya da ya kai mita 351.28.
Helen ta kammala aikin hada gashin wajen amfani da daurin gashi 1,000 da gwangwanin feshin man kitso 12 da robar manna gashi na gam 35 da kuma ƙarfen maƙala gashi 6,250.
"Neman kayan aiki na hada gashin Wig mafi tsawo ba abu ne mai sauki ba. Ƙwarewata a matsayin mai gyaran gashin kanti ta taimaka min sosai," a cewar Helen yayin hirarta da GWR.
Helen ta kasance ƙwararriyar mai gyaran gashin kanti a tsawon shekaru takwas, inda take hada gashi 50 zuwa 300 a kowane mako.
"Na horar da daruruwan dalibai kuma na hada dubban gashin kanti," in ji Helen.
Ba karamin jarumtaka ta yi ba
Duk da irin ƙwarewa da Helen take da ita, hada gashin kanti mai tsawo da ya kafa tarihi ba karamar jarumtaka ba ce.
“A wani lokaci, na kan ji na gaji,” in ji ta, amma masoya da abokai da kuma ƴan'uwa sai su ƙara ba ni karfin gwiwa.
Helen yanzu tana ajiye gashin kantin a ofishinta, inda ta gayyaci kowa ya zo ya kalle shi "duk lokacin da suke so."
Bayan ta girma tana karanta littafin Guinness World Records a kowace shekara, Helen ta yi farin ciki da kasancewarta wacce ta samu damar shiga kundin tarihin ita ma.
"Za a dauki tsawon lokaci ina kakabin hakan," ta ce.
Wannan nasara tana ɗaya daga cikin mafi kyawun abubuwan da suka taɓa faruwa da ni. Har yanzu kallon abin nake kamar a mafarki.