Daga Firmain Eric Mbadinga
Pinocchio, babban jarumin marubucin Italiyanci Carlo Lorenzini na labarin hikaya The Adventures of Pinocchio, mai yiwuwa an san shi ne a cikin almara, amma fasahar sassaƙa ta Sorobabel Ntutumu Obono tana ƙwata gidaje da yawa a Equatorial Guinea a zahiri.
Duk da cewa ba sa motsi ko magana, abubuwan da Sorobabel Ntutumu Obono mai shekaru 30 ke sassaƙa sukan kasance tamkar masu rai, kuma launinsu da siffarsu na da matuƙar ɗaukar hankali ga duk wanda ya samu damar gani ko ya taɓa su, garin a Bata, babban birnin tattalin arzikin kasar wacce take Afirka ta Yamma.
“Lokacin da na koma Bata daga ƙauyenmu a shekarar 2006, na riga na ji ina son zama masassaƙi. Ko a lokacin da nake karatu da sauran buge-bugena, abin ya ya zauna a raina, kuma na san cewa wata rana zan cika burina na yin hakan a aikace," Sorobabel ya shaida wa TRT Afrika game da ƙwarin gwiwarsa na tsawon rayuwarsa.
Kafin ya fara aikin sassaƙa, Sorobabel ya sami damar tabbatar da kansa a matsayin makanike da gyaran injina a gundumarsa ta Mofono yemfen Eviyong.
Kwarewarsa a cikin sana'o'in biyu ta sake bayyana Sorobabel, kafin daga bisani ya himmatu wajen bayyana fasaharsa a aikin sassaƙa a cikin shekarar 2018.
"Bayan waɗannan ƙwarewar, na dawo wurin iyayena da ke zaune a Bata kuma na fara koyon aikin fasaha. Don haka, ina da tunani da yawa kan itace kuma wata rana na ce dole ne in aiwatar da wannan a aikace."
"Na fara kadan da kadan da itacen bamboo, kuma daga nan na fara samun salon abin da zan zana daga mu'amala da wasu," ya shaida wa TRT Afrika.
A lokacin da ya fara sassaƙa, Soro, kamar yadda na kusa da shi suka san shi, ya ce jama’a ba sa nuna sha’awa sosai kuma ba sa ba shi ƙwarin gwiwa kan sana’ar tasa, ba kamar a yanzu ba.
Masassaƙin ya yi amfani da abin da ya ɗauka rashin kulawa zuwa wani dalili na ba shi ƙarin gwiwa inda ya samar da abubuwa masu kyau da kuma inganta sana'arsa.
"Hakan ya ƙara min azama kuma ina son in ƙara himma da inganta aikina, don haka na fara sanya kayana a Facebook da Zaurukan WhatsApp, kuma da kadan-kadan na fara samun abokan ciniki."
"Na ci gaba da aikina cikin ƙwarewa da ƙwarin gwiwata da haƙuri. Yayin da lokaci ya wuce, na kara karfi kuma na sami karin sha'awa don ƙirƙirar wasu samfura da suka bambanta da waɗanda na yi a baya," a cewarsa.
Sorobabel ya ce daga kan ayyukansa na farko da ya sha wahalar yi har zuwa na yau ba zai ce ga waniwanda ya fi so a kan sauran ba.
"Har yau, ƙwarewata da sha'awa da kwanciyar hankali suna ƙaruwa a kowace rana, kuma ina yin duk abin da zan iya yi don ganin na yi aiki mai inganci a ko yaushe don komai ya kasance mai riba,” in ji Sorobabel, wanda aikinsa ke ƙara jan hankali da ba da sha’awa.
Kamar yadda yake a kusan dukkanin kasashen Afirka, kasuwar fasaha a Equatorial Guinea tana da abokan hulɗarta.
Kazalika su kansu 'yan Equatorial Guinea, a halin yanzu abokan ciniki daga ƙasashen waje ne suka fi ba da odar sayen kayan fasihai irin su Sorobabel Ntutumu Obono.