Daga Brian Okoth
Sarkodie na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Ghana na zamani.
Mawaƙin mai shekaru 38 da haihuwa ya samu karɓuwa daga masoyansa, har ma a wasu kafafen yaa labarai na nishadi kana sun bayyana shi a matsayin mawakin gambara da ke tashe a Afirka.
An haifi mawaƙin ne a ranar 10 ga watan Yuli, 1985, a garin Tema da ke kudu maso gabashin Ghana. Shi ne na huɗu a cikin ƴaƴa biyar da aka haifa a gidansu, an kuma raɗa masa suna da Michael Owusu Addo.
Sarkodie ya yi karatun boko a Tema, sannan ya yi digirinsa na farko a fannin zane-zane daga Kwalejin Jami’ar IPMC da ke Ghana.
Ya soma waƙa a mastayin ƙaramin mawaƙin gambara
Mawaƙin ya fara sana’ar waƙa ne a matsayin ƙaramin mawaƙin gambara na ƙasa, inda ya halarci gasar gambara da wani gidan rediyon Ghana ya shirya.
A yayin gasar gambarar ne aka gabatar da shi ga fitaccen mai shirya waƙoƙi da ake yi wa laƙabi da Hammer of The Last Two.
Hammer ya taimaka wa Sarkodie naɗar wasu waƙoƙinsa guda biyu waɗanda suka samu karɓuwa sosai daga masoyansa na Ghana.
A watan Satumban shekarar 2009, mawaƙin Amurka Busta Rhymes ya gudanar da wani taro a Accra babban birnin kasar Ghana, kuma Sarkodie na daga cikin mawaƙan ƙasar da suka nishaɗantar a wajen tare da wasu mawaƙan da suka kawo ziyara.
Mawaƙin Afirka na farko da ya lashe lambar yabo na BET
A shekarar 2010 ne, waƙoƙin Sarkodie masu taken "Push" da "Baby" suka kasance kan gaba a jerin waƙoƙin da aka fi saurara a Ghana.
Kundin nasa mai suna "Rapperholic", wanda aka saka a 2012, ya taimaka wa Sarkodie wajen nasarar lashe lambar yawo na BET ta farko da ya taɓa samu, da kuma nasarar da ta biyo baya ta lashe lambar yabo ta Best International Act category.
Kazalika mawaƙin ya zama ɗan gambara na farko a Afirka da ya lashe kyautar BET, kana ɗan Ghana na farko da ya kafa wannan tarihi.
A shekarar 2019 Sarkodie ya sake lashe lambar yabo ta BET rukunin Best International Flow category, kana ya zama mawaƙin gambara na Afirka da aka fi yawan zaɓa a kyautukar ta BET.
Zantawa da aɗliban makarantar Kasuwanci ta Harvard
Mawaƙin gambarar ya lashe kyautuka 108 daga mataki 195 na fegen nishaɗi daban-daban da aka zaeɓ shi, ciki har da ɗaukar lambobin yabo 28 na 'Ghana Music Awards'.
"You Go Kill Me", "Adonai" da "No Kissing Baby" na daga cikin fitattun waƙoƙin Sarkodie.
A 2016, Makarantar Kasuwanci ta Harvard ta gayyaci mawaƙin don ya zanta da ɗalibai kan ƙalubalen da mawaƙan Afirka ke fuskanta a sana'arsu.
A faɗin yankunan Afirka, Sarkodie ya yi waƙokin haɗin gwiwa da dama tare da Victoria Kimani ta kasar Kenya, da Patoranking da Runtown da kuma Burna na Nijeriya, da Diamond Platnumz na Tanzaniya; da kuma marigayin Afrika ta Kudu AKA da dai sauransu.
Yana cikin mawaƙan Afirka da suka fi kuɗi
A mafi yawan lokuta Sarkodie na amfani da harshensa na asali Twi wajen rera waƙoƙin gambararsa.
Harshen Twi na daga cikin rukunin harsunan da al'ummar Ashanti a yankin kudancin Ghana suke amfani da shi.
Kafofin watsa labaru na duniya da dama, ciki har da Forbes da The Guardian, sun ayyana Sarkodie a matsayin ɗaya daga cikin mawaƙa fitattu kana masu kudi a Afirka.
Baya ga waƙa, mawaƙin ya mallaki wani kamfanin sutura mai suna Sark by Yas, wanda ya kafa a shekarar 2013.
Rahotanni sun ƙiyasta arzikin mawaƙin da kuɗin Amurka dalar miliyan bakwai.
Sarkodie ya auri matarsa Tracy, a watan Yuli 2018 kana suna da ƴaƴa biyu tare.