Daga Pauline Odhiambo
Sally Musonye wadda ta girma a unguwar marasa galihu ta Mathare a birnin Nairobi na ƙasar Kenya, ta sha tunawa kanta cewa — wata rana al'amura za su inganta.
Kamar dai sauran gidaje da dama a unguwar, gidansu Sally ma ba su da wutar lantarki, inda a ko yaushe sai dai ta yi aikin gida da ake ba ta na makaranta ta hanyar amfani da fitar ƙwai ta kananzir.
Ta shaida wa TRT Afrika cewa "An shafe shekara 20 babu wutar lantarki a gidanmu."
"Rashin samun kananzir sosai na nufin dole mu zaɓa ko dai aikin makaranta za mu ui ko abincin dare. Dole dai mu zaɓi yin abinci," tana ba da labarin yadda suka yi ƙuruciya cikin yanayi na tsanani.
Ba abin da Sally ta fi so a ko yaushe irin ta yi ta kallon jerin falwayoyin da ke kafe a yankin unguwarsu, tana mai fatan samun lantarki a gidansu.
"Na kan yi hasashen kaina a matsayin ma'aikaciyar kamfanin wutar lantarki ta ƙasa wata rana, ta yadda zan ja mana lantarki a gidanmu mu daina rayuwa a cikin duhu," ta tuna irin burikanta.
Sally ta dage sosai wajen ganin ta cimma wannan burin nata inda har ta samu yin digiri a fannin injiniyan lantarki bayan kammala karatunta na sakandare.
Fatanta shi ne ta ga iyayenta sun yi rayuwa mai inganci bayan yin ritaya daga aiki.
"Burina ya cika a shekarar 2015 inda na samu aiki a Kamfanin Lantarki na Kenya (KPLC), a matsayin injinya har kuma na samu damar jan wuta a gidanmu," ta faɗa cikin alfaharin cimma ƙudurinta.
Bayan haka kuma zamowarta cikakkiyar ma'aikaciyar KPLC zai ba ta damar tara kuɗaɗen da za ta sayi gidan da ta girmaa cikinsa a Arewacin Mathare.
Muradu da dagiya
A shekarar 2015, Sally ta ƙirƙiri wani shiri na AshGold Africa Initiative - wanda ke da nufin "sauya rayuwa daga lalacewa zuwa annashuwa" ta hanyar ƙirƙiren kimiyya da fasaha da lissafi da aikin injiniya (STEM) a al'ummomin da ke fuskantar wariya.
"A wancan lokacin, da yawa daga cikin sa'o'ina sun zama iyaye a ƙarancin shekarunsu ko suna gidan yari ko kuma sun mutu. Arewacin Mathare waje ne da ya zama matattara aikta mugwayen ayyuka da shan ƙwaya," in ji Sally.
"Har yanzu ana cikin wannan halin a Mathare, wanda dalilin da ya sa ma na yanke shawarar ƙirƙirar shirin AshGold don kawo gyara a cikin al'ummar.
A cikin 2017, kamfanin Sally ya aika ta zuwa gundumar Kitui da ke yankin gabashin kasar, inda burinta na kai wutar lantarki ga al’ummomin karkara ya ƙarfafa.
"Wannan ne karo na farko da na fita daga babban birnin kasar zuwa wani yanki na karkara na Kenya. An tura ni da tawagata makarantar sakandare mai nisan kilomita 6 daga inda tashar lantarkin take," Sally, wacce ke aiki a matsayin injiniyar haɓaka tsarin wutar lantarki, ta tuna.
"Makarantar ta nemi a kai mata wutar amma ajujuwa uku kawai take da su, wanda ɗaya daga cikinsu ma shi ne ofishin zaman malamai. Don haka zan iya cewa ba za su iya biyan kudin wutar ba."
Rayuwa cikin duhu
Wani rahoto da aka fitar a 2019 na ƙungiyar kula da lantarki ta duniya ta ce kusan mutum miliyan 18 daga cikin miliyan 138 da ke rayuwa a ƙauyukan Gabashin Afirka da ba su da lantarki a Kenya suke.
A ɓangarenta, Sally ta yanke shawarar fuskantar Cibiyar Injiniyoyin Lantarki IEEE, wata ƙungiya ta duniya wacce za ta iya zuba kuɗi don samar da lantarkin hasken rana a makarantar da ta gano ɗin a matsayin abin da ta fi bai wa muhimmanci.
Ta kuma yi wani tunanin na cewa, baya ga samar da lantarki, za kuma ta horar da ɗaliban makarantar a wasu fannoni na aikin injiniya.
"Na samu tallafin dala miliyan biyar daga cibiyar IEEE inda na haɗa faifan lantarki na rana a makarantar, inda ɗalibai 106 suka amfana. An yi hakan a shekarar 2022 ne," ta faɗa.
"Da muka sake komawa makarantar a shekarar 2023, mun gano cewa yawan ɗalibai mata ya ƙaru da kashi 42 cikin 100 cikin shekara guda."
Shirin ba da shawara
Kazalika Sally ta haɗo kan ɗaliban injiniya na jami'a don goyon bayan aniyarta, ta kuma faɗaɗa shirinta na samar da lantarkin hasken rana zuwa wata makarantar sakanadaren a Gundumar Makueni a yankin gabashin Kenya.
"Na samar da tawagar ɗaliban injiniya a jami'o'in gwamnati shida don na dinga ba su horo da shawarwari," kamar yadda ta bayyana.
"Ɗaliban injiniya sun fi dacewa da hakan maimakon ƙwararru waɗanda ba za su yi daɗin mu'amala ba kamar ɗaliban saboda bambancin shekarunsu."
Shirinta na ba da horo ya kankama a makarantu 13 inda ɗalibai da malamai 7,000 ke amfana.
"Ko a matakin jami'a muna da ɗaliban kimiyya da fasaha mata da dama, Amma sai dai ba mu faye gani suna neman manyan ayyuka ba," in ji Sally.
"We know that gender biases exist, but there is a need for more research and mentorship to help women break that glass ceiling."
She hopes training students in solar energy and other STEM projects will help their career progression.
Shirin da ya samu lambar yabo
Sally ta ƙara da cewa "Idan ina bai wa ɗalibai horo, muka haɗan har da iyaye. Ta hakan ne muka gano cewa akwai iyaye da dama da ke da fasaha a sana'o'in hannu."
"Hakan ya ja hankalina wajen fara sana'ar haɗa sabulu ta yadda iyaye za su iya koyon yadda za su yi amfani da basirarsu wajen kasuwanci inda har za su iya ɗaukar nauyin biya wa 'ya'yansu kudin makaranta da littattafai."
A jumlace, shirin Ash Gold ya samar da lantarki mai hasken rana har kilowat 3.8 ga makarantu biyu — wata nasara da ta sa Sally ta samu lambobin yabo da karramawa har daga wajen Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya.
Ta ce "Ina fatan na ci gaba da zama abar kwaikwayon mutane da dama masu neman su ga hasken lantarki. A duk yanayin da kake ciki, ka duba lantarkin a kan kanka sai ka assasa shi."