Sakihan Musafiri na da burin fadada harkokinta domin tallafa wa matasa marasa aikin yi.

Daga Firmain Eric Mbadinga

A Gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, kayatatun kayayyakin ado da ake sana’antawa a masana’antar Sakinah Musafiri da ke birnin Goma sun zama ababen kauna, da mamaki da alfahari.

Duk da cewa garin Goma ya fi kaurin suna da matsalar masu tada kayar baya, da kuma yawan aman wuta da dutsen Nyiragongo ke yi, kayan dakin Sakinah Musafiri suna kara fito da sunan gari da gyara shi a idon duniya.

Sakinah Musafiri ta sanya wa kamfaninta suna “La Mano,” wanda a harshen Spain yake nufin hannu domin nuna muhimmancin kafintoci- wadanda su nekan gaba a masana’antar- suke yi.

Kayayykin daki da sauran kayayyakin ado da take yi sun biyo bayan kasancewarta ma’abociyar kyawawan ababe, da kirkira da kaunar da take wa yanayin katakan kasarta kamar yadda ta bayyana wa TRT Afrika.

Mutane da dama suna sha’awar kayan dakin da take hadawa

“Na gano cewa a Congo muna da katakai masu kyau, amma ba a cika amfani da su ba kamar yadda ya dace. Sai na yanke shawarar koyon aikin kafinta, da yadda zan yi amfani da takatai in hada abubuwa masu kyau da za su amfani al’umma da kasata da Afrika da ma duniyar baki daya,” in ji Sakinah.

Domin assasa kamfanin na “La Mano,” Sakinah ta yi amfani da kudadenta ne wajen sayan kayan aiki, sannan ta kama hayar wajen aikin, sai kuma ta nemo matasa maza da mata marasa aikin yi, ta koya musu aikin, sannan ta dauke su aiki.

Aikin farko da suka yi shi ne fitillar katako, wanda cikin kankanin lokaci ta samu karbuwa a wajen mutanen Goma.

Fitilun katakan suna cikin kayatattun kayayyakin da suka hada.

Yadda aikin ya samu karbuwa ne ya karfafa gwiwar Sakina, duk da cewa ba ribar ba ce a gabanta.

“Burinmu shi ne mu koyar da matasa, sannan mu nuna wa duniya kayayyakinmu da katakanmu na Congo.

“Muna so mu karfafa gwiwar mutanenmu na Congo su rika amfani da kayayyakin da ake hadawa a cikin kasarmu, maganar riba kuma watakila sai nan gaba,” inji Sakinah.

A yanzu haka akwai kusan ma’aikata 40 a La Mano, wadanda suke aiki a bangarori daban-daban da suka hada da bangaren kudi da kafintoci da masu walda da sauransu.

Suna hada kayayyakin da suka kirkira da kansu, sannan suna hada kayayyakin da kwastomomi suka bukata a hada musu. Suna kokarin samar da daidaito tsakanin yadda sana’ar take a da, da kuma zamanantar da ita.

Wani lokacin kwastomomi ne suke bayyana irin kayan da suke so a hada musu. Kamfaninta nata ya ware kwana daya a duk wata domin wayar da kan mutane a kan illar sare itatuwa.

A kasa da shekara uku da bude kamfanin, Sakinah Musafiri da abokan aikinta sun samu kwastomomi da dama wadanda kashi 90 dinsu ’yan Congo ne, sai sauran kashi 10 din wadanda mutanen sauran kasashen Afrika da Turai da Amurka.

“Wannan shi ne burinmu, kuma muna farin cikin ganin muna samun nasara,” in ji Sakinah.

Matashiyar mai shekara 27 wadda ta yi digiri a fannin development management ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba. Burinta shi ne ta kara bude wasu kamfanonin kamar La Mano domin horar da matasa da daukarsu aiki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da ’yan wasu kasashen.

TRT Afrika