A birnin Lagos wanda shi ne birnin mafi girma a Nijeriya, an gudanar da wani baje-kolin zane-zane da aka yi wa laƙabi da "+234Arts", don bayyana ababen fasaha da wasu suka ƙirƙira.
An yi bikin nune-nunen daga ranar 22 zuwa 31 ga watan Maris a gundumar Ikoyi ta birnin na Lagos.
Taken nune-nunen shi ne "Sabon Tarihi", kuma manufarsa ita ce ƙarfafa fasahar mutanen yankin da haɓaka basira da al'adun al'ummar ƙasa.
Bikin nune-nunen wata dama ce ta ƙarfafa haɗin-gwiwa tsakanin matasa masu zane-zane, da ma waɗanda suka daɗe a harkar, a cewar Osemedua Iweluma, wanda ke aikin sa-kai a Soto Gallery, wadda ta shirya bikin.
Osemedua ya ce nune-nunen ya shafi ayyukan da ke warware zare da abawa game da tunani mara kyau kan tarihin Nijeriya.
Ɗaya daga cikin manufofin canja ƙaurin sunan da Nijeriya ta yi.
Bikin yana fatan ɗaukaka “harkar sayen kayan fasaha don inganta arziƙin masu zane da ke gida da waje.'' in ji Iweluma da yake magana da TRT Afrika.
Bikin nune-nunen na da "burin samar da dandalin da masu zane-zane da masu tara kayayyakin zane don haɓaka darajar fasha a Nijeriya”, a cewar masu shirya bikin.
Ayyukan da aka nuna sun shafi zamantakewa, da al'adu, da siyasa da cigaban zamani.