Daga Fathiya Bayusuf
A Likoni da ke Mombasa, wani gidan kula da yara da ake kira Gidan Marayu na Jannatul Firdaus ya bude shafin farantawa marayu irin su Rashid Kishki.
Shekaru biyar da suka wuce ne aka kai yaron mai shekaru 12 a yanzu wannan waje, bayan rasuwar iyayensa sakamakon rashin lafiya.
"Babban kalubale ne kasancewa a nan. Ina godiya saboda tarbar da aka yi min, amma a zuciyata, har yanzu ina son na san me ake nufi da samun iyaye, ina son na ji son uwa da uba," in ji Rashidi da ya rasa iyayensa yana dan karami.
Dalibin dan aji shida a firamare ya bayyana cewa "Muna bukatar karin taimako, isasshen abinci, tufafi mai kyau, da wajen kwana mai tsafta.
"Wasu lokutan, ina dimautuwa da kadaici, duk da ina son kasancewata a nan."
Khadija Anton mai shekara 18, da ke rayuwa da nakasa na mararin samun so da kaunar iyaye. An kawo ta wannan cibiya tun tana jaririya bayan rasuwar iyayenta sakamakon rashin lafiya.
Ta fada wa TRT Afirka cewa "Ina bukatar kafar katako da keken dinki ta yadda zan taimaki kaina."
Wani kalubalen kuma shi ne na rashin iyaye. Na so a ce ina da su, su nuna min so da kauna, tare da kula da bukatuna. Ina matukar bakin ciki." in ji Khadija.
Gidan Marayu na Jannatul Firdaus na da marayu kusan tamanin. ya zamar musu gidan da ke samar musu da kayan bukatu da ilimin addini.
Mama Dahabu Mwalimu, wadda ke kula da marayun, ta bayyana kalubalen kula da wadannan yara inda ta kuma yi nuni ga muhimmancin nuna musu so da kauna, ba su tsaro da ingantaccen ilimi.
"Kula da wadannan yaran ba abu ne mai sauki ba. Suna da manyan bukatu, amma a wasu lokutan babu isassun kudade." in ji mama Dahabu.
"A lokacin da suke yara kanana, zai yi wuya a iya sayen duk abun da suke bukata, kuma wasu lokutan ma ko abinci na iya zama kalubale. Muna godiya ga wadanda ke taimaka mana."
A gefe guda kuma, Masana halayyar dan adam na bayyana muhimmanci karfafar tunanin yara kanana.
Lucy Mjomba, mai tarbiyyar yaran ta shaida wa TRT Afirka cewa "Ta hanyar nuna musu so, za mu iya taimakon yaran nan tare da sauya halayyarsu.
"A yayin da suka girma da shiga cikin al'umma kuma suka samu yanayin da zai canja ra'ayinsu, za su iya juya kwakwalwarsu tare da gina makoma mai kyau."
Miliyoyin daruruwan yara na zama marayu saboda rikice-rikice da batan da iyayen su ke yi.
UNICEF na cewa yara kanana miliyan 400 ko kuma daya cikin biyar na kowanne yaro ya gujewa yaki zuwa wani waje na daban.
Daraktar UNICEF Catherine Russel ta ce "Da yawa daga cikin su sun rasa matsugunansu, hakan ya sanya su rabuwa da iyayensu, suna asarar shekarun neman ilimi."
A yayin da dukiya ke bukin Ranar Yara ta Duniya, marayu kamar wadanda ke a Gidan Marayu na Jannatul Firdaus na fatan wata rana za su samar da nasu iyalan tare da ci gaba."
Amma rasa iyayensu wani abu ne da dole su ci gaba da jure shi a tsawon rayuwarsu.