Wasu sulan saurari rediyo ko da tafiya suke yi: Photo/Reuters

Yayin da duniya ke bikin Ranar Rediyo ta Duniya, har yanzu masu kafar sadarwar na ci gaba da kutsawa yankunan karkara na Afirka da ƙarfi, a matsayin babbar tushen samun amintattun labaran siyasa da nishadantarwa.

Na'urorin rediyo na gargajiya har yanzu ana amfani da su a ko ina a mafi yawan yankunan karkara, da kuma mutanen da ke shiga gidan rediyon FM ta hanyar wayoyi, wanda ke nuna alamar ci gaba da dacewa da kafofin watsa labarai duk da karuwar shaharar hanyoyin dijital da ake buƙata ta wayoyin hannu.

Zaɓi tsakanin kuɗin da ake kashewa a hawa intanet da wayar sauraron rediyo ba tare da kashe ko sisi ba ya sa rediyon zama hanya mafi sauki ta samun labarai ga masu ƙaramin ƙarfi.

Masu sauraren rediyo a Nijeriya da sauran kasashen Afirka suna sauraron gidajen rediyon da suka fi so yayin da kafafen watsa labarai suke karɓar hanyoyin zamani.

"Idan ba ni da wani aiki da nake kokarin aiwatarwa, ba ni da wani muhimmin aiki da ya wuce sauraron rediyo," in ji Zaidu Bala Kofa Sabuwa, wani mai sauraron rediyo a Nijeriya, kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

“Duk gidajen rediyon da suke watsa shirye-shiryensu da harshen Hausa (harshen gida), a gaskiya sai na saurare su. A cikin motata, ba na saka komai idan ba rediyo ba. Ina sauraron tashoshin rediyo kawai duk inda zan je. Idan zan yi tafiya daga nan zuwa Abuja ko Kano, ba zan saurari komai ba sai gidajen rediyo,” in ji shi.

“Ba zan iya cewa zan shafe awa daya ko biyu ko uku ina sauraron rediyo ba. Halin da nake ciki ne zai tabbatar da tsawon lokacin da zan saurare shi, amma ba ni da wani abin da ya kai na sauraron rediyo,” ya kara da cewa.

Sauraron rediyo ya zame wa masu taga da suke leƙa duniya: Photo/Reuters

A gare shi rediyo shi ne dandalin ilimantarwa inda yake samun fadakarwa kan abubuwan da ke faruwa a gida da waje.

Rediyo a kan wayoyin zamani na komai da ruwanka

Wadanda ke iya sayen datar intanet sun zaɓi sauraron rediyo ta intanet saboda sautin ya fi fitowa fili rangadadau.

"Ina da rediyo daban-daban daga kan Son da Panasonic da Kchibo da sauran su," in ji Zaidu.

"Babu a inda ba na sauraron rediyo. Duk inda na je idan babu network sai kawai na fito da rediyona na saurara. Akwai wasu da nake ajiyewa a aljihuna. Akwai wasu a motata." ya ce.

"Idan kuma inda na je akwai intanet to sai na yi amfani da wayata wajen sauraron rediyo saboda sautin kan fito ras babu hatsaniya," ya ƙara da cewa.

Amma shi Isa Rano Hudu Hadejiya, wani mai yawan sauraron rediyo, yakan yi amfani da wayarsa ta komai da ruwanka wajen kama duk tashar da yake so don sauraro.

Isa Rano Hudu Hadejiya ma ya dade yana sauraron rediyo a arewacin Nijeriya. Ya shafe shekaru yana sauraron rediyo.

Rediyo aboki ne da wasu ba za su iya yi ba sai da shi: Photo/Reuters

“Duk lokacin da ba na yin komai, ina da rediyo a gabana. Ina sauraron rediyo har zuwa tsakar dare lokacin da duk gidajen rediyo na gida da na waje ke rufewa kafin in kwanta barci a kullum," Isa Rano Hudu ya shaida wa TRT Afrika.

“Har yanzu ina amfani da rediyo ta hannu domin idan ina gida, ina amfani da ita wajen sauraron tashoshi. Amma idan ba na nan babu yadda za a yi in saurari rediyo, sai in yi amfani da wayar salula don sauraron rediyo,” in ji shi.

Ya kara da cewa "Ta wadannan hanyoyi guda biyu ne nake sauraron rediyo a kowane lokaci."

Manhajar Podcast na ƙara samun karɓuwa a fagen yada labarai daban-daban a Nijeriya da sauran sassan Afirka don jawo hankalin masu sha'awar saurare irin su Zaidu da Isa wadanda ke amfani da wayoyin hannu don sauraron gidajen rediyo.

TRT Afrika