Daga Charles Mgbolu
Nau’in wakar jazz, wadda daya ce daga cikin fitattu na’ukan wakoki, na kara samun karbuwa bayan mawakan bangaren sun shirya taron kalankuwar wakokin na duniya wato Ranar Wakar Jazz ta Duniya.
Domin karrama bangaren wakar, UNESCO ta shirya shirya tarukan kade-kade da raye-raye daga ranar 27 zuwa 30 ga Afrilu a birnin Tangier da ke Arewa maso Yammacin Maroko.
Darakta-Janar na UNESCO, Audrey Azoulay ya ce ana murnar Ranar Wakar Jazz ta Duniya a kasashe sama da 190, amma a kasar Maroko aka shirya taron na bana na a madadin kasashen duniya.
Taron ya kara “bayyana tarihin wakokin jazz a birnin, sannan ya kara fito da alakar al’adu da ke tsakanin Maroko da Turai da Afrika,” kamar yadda sanarwar UNESCO ta bayyana.
Taron, wanda ya samu hadin gwiwar Ma’aikatar Al’adu ta Maroko, ya kuma kunshi tarukan kara wa juna sani ga dallibai, inda aka gabatar da makalu a kan muhimmancin wakar Gnawa na Maroko da kuma alakarta da wakar jazz.
Gnawa fitaccen nau’in waka ce a Maroko da ke hada wakokin baka da wakoki da raye-rayen al’adu.
Babban abin da ya fi kayatarwa a taron shi ne yadda dukkan fitattun mawakan bangaren na duniya irin fitaccen mawakin Gnawa, Abdellah El Gourd daga Maroko da Richard Bona daga Kamaru da Moreira Chonguiça daga Mozambique suka rakashe a tare.
Wakar jazz na kara samun karbuwa a fadin nahiyar Afrika, inda ake kara samun kasashen da suke shirya taron kalankuwar wakar.
A shekarar 2022, an shirya babban taron kalankuwar wakar a birnin Legas da ke Nijeriya, inda mawakan bangaren na Afrika da duniya suka taru a Legas da domin bikin Ranar Wakar ta Duniya.
Ghana da Afirka ta Kudu ma sun taba shirya tarukan nishadin, inda dubban mutane suka halarta.
Ranar Wakar Jazz ta Duniya da UNESCO ta assasa a shekarar 2011, ya shiga cikin kundin ranakun da Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ke sane da su.
Masu shirya taron sun bayyana cewa kalankuwar tana nuna muhimmancin wakokin jazz wajen wanzar da zaman lafiya da adana al’adu da mutunta dan Adam.
A cewar UNESCO, Ranar Wakar Jazz ta Duniya ta samu karbuwa a duniya, inda sama da mutum biliyan 2 suke shiga taron duk shekara ta hanyar shirya tarukan nishadi a zahiri da kuma a gidajen rediyo da talabijin da sauran kafofin sadarwa da ayyukan gayya da sauransu.
Kungiyar wakokin jazz ta Herbie Hancock Institute of Jazz ce UNESCO ta daura wa alhakin tsarawa da shirya Ranar Wakar Jazz ta Duniya duk shekara.