Ƙasashen Afirka da suka fi farin ciki / Hoto: Reuters

Majalisar Ɗinkin Duniya ta saki wani jeri na ƙasashen da suka fi farin ciki a duniya, a yayin da ake bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya ranar 20 ga watan Maris.

Rahoton Ranar Farin Ciki ta Duniya na 2024 da aka wallafa a ranar Laraba ya nuna cewa Libiya ce ƙasar da ta fi farin ciki a Afirka.

Daga ita sai ƙasar Mauritius da Afirka ta Kudu a nahiyar, inda Lesotho kuma ta zama ta ƙarshe a ƙasashen Afirka gaba ɗaya.

A matakin duniya kuwa, Finland ce ta farko a jerin ƙasashen da suka fi farin ciki, sai Denmark da Iceland da Sweden, yayin da ƙasashe takwas na Afirka suka kasance daga cikin 10 na ƙarshe a jerin.

Rayuwa mafi inganci

An nemi mutane a ƙasashe da yankuna 143 da su ƙimanta rayuwarsu daga matakin sifili zuwa 10, inda 10 ke nuna mafi kyawun rayuwarsu.

An yi amfani da sakamako na shekara uku da suka wuce don samar da jerin.

A fayyace, gamsuwar rayuwa a yankin kudu da hamadar Sahara ya ƙaru a tsakanin matasa, ko da yake jin dadin matasa ya ragu a Arewacin Afirka.

The annual World Happiness Report was launched in 2012 to support the United Nations' sustainable development goals.

An kaddamar da rahoton jin dadin duniya na shekara-shekara a shekara ta 2012 don tallafawa manufofin ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.

Ƙasashe goman farko na Afirka da suka fi farin ciki a jerin na duniya

  • Libya ce ta 66 a duniya
  • Mauritius ce ta 70 a duniya
  • Afirka ta Kudu ce ta 83 a duniya
  • Algeria ce ta 85 a duniya
  • Congo Brazzaville (Republic of Congo) ce ta 89 a duniya
  • Mozambique ce ta 90 a duniya
  • Gabon ce ta 95 a duniya
  • Ivory Coast ce ta 96 a duniya
  • Guinea ce ta 97 a duniya
  • Senegal ce ta 99 a duniya

Matsayin sauran ƙasashen Afirka a jerin duniya:

  • 102 - Nijeriya
  • 104 - Kamaru
  • 107 - Maroko
  • 109 - Nijar
  • 110 - Burkina Faso
  • 114 - Kenya
  • 120 - Ghana
  • 127 - Masar
  • 130 - Habasha

Kasashe goma mafi karancin farin ciki a Afirka a cikin jerin kasashen duniya:

  • 131 - Tanzaniya
  • 132 - Comoros
  • 134 - Zambiya
  • 135 - Eswatini
  • 136 - Malawi
  • 137 - Botswana
  • 138 - Zimbabwe
  • 139 - Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
  • 140 - Saliyo
  • 141 - Lesotho

A cikin binciken, an yi la'akari da ma'aunai na tallafin zamantakewa da samun kudin shiga da lafiya da 'yanci da karimci da rashin cin hanci da rashawa.

TRT Afrika